Chapter eight

558 8 1
                                    

🤍Dr.BOBBY🤍

By Aysha Rano✨

Wattpad@aysharano22

08

Suna shiga gaba daya class suka hada baki suna gaishesu..Nur ne kadai ya amsa musu da "morning class ya weekend?.." suka amsa da lafia yace"well as a result of maternity leave da malaman Reproductive Health dinku ta tafi nasan you people do miss alot a karatunku ga kuma exams dake approaching...Class Rep dinku tazo ta sameni da maganan and our Generous Proprietor here says he will assist you guys har kuyi covering syllabus dinku"..ya karasa mgn da wani killer smile a fuskanshi tareda dan juyawa ya kalli Bobby dake tsaye rungume da hannaye yana sauraronshi...lokaci daya Class din ya dauki tafi jin Proprietor da kanshi yace zaiyi assisting nasu nan kuwa basu san saida aka kai ruwa rana before ya amince ba...Lamido da Bilkisu kuwa kallo daya sukayi masa gaba daya sukayi kasa da idanunsu..Billy dai addu'a take kada Allah ya kawo dalilinda zaisa wnn shegun idanuwan nashi su sauka a kanta..ita kuma Aysha hararan gefen ido take binshi dashi cikin ranta tace"inyamurin banza inyamurin wofi"..daidai nan kuma Nuru ya dubi Bobby yace"to Dr.Bobby bismillah"..daga haka ya koma can karshen class din ya samu wani empty seat yayi zamanshi a wurin...shi kuma Bobby ya dan kalli class din har yanxun yana rungume da hannu thinking from where to start...saida yayi shirun amost 3 mins kafin yace"where do you guys stop?.."daya daga cikin 'yan class din ta fada mishi last topic da sukayi...yana dan gyada kai ya tambayi course outline nan ma suka bashi...saida ya gama studying course outline din snn ya ajiyeshi kan table dake gabanshi yace"well according to the course outline kunada remaining 5 topics to cover before the exams..now zamuyi kokari muyi covering 2 topics the ramaining ones kuma zakuyi dividing kanku into 3 groups..each group su dauki one topic suje suyi studying dinshi sosai zuwa ranan Thursday zakuyi presentation..do u get me?.."gaba daya suka amsa da sun gane...shi kuma ya juya ga board dinsu yaga akwai rubutu a jiki sai ya sake juyawa garesu yace"who's ur class rep?.."gaba daya suka nuna Lamido...shi kuma ya wani daure fuska ganin itace dan lokaci daya incident din jiya ya fado masa a rai...itama daure nata fuskan tayi snn ta mike kanta a kasa..dukda ba kallonshi take ba tanajin wnn shegun idanun nashi a kanta..."come and wipe the board"..ya fada still looking at her...batayi musu ba ta fito tayi wiping board din ta juya zata koma ya sake fadin"da fingers dina kikeso inyi maku rubutun?.."bata juyo ba ta karasa seat dinta ta bude locker dinta ta dakko wani pink marker ta kai mishi snn ta sake dawowa ta zauna...duk wnn abun dake faruwa Dr.Nuru na bayan class din yana kallonsu...murmushi kawai yake yana girgiza kai cikin ranshi yace"zamuga yanda za'ayi wnn lecture"...sunan topic din Bobby ya rubuta jikin white board snn ya juyo yana facing dinsu yace yanaso daya daga cikinsu ta danyi briefing dinsu about the topic before he starts...wajen mutum biyar ne suka daga hannu shi kuma ya shiga binsu da kallo daya bayan daya yanaso yayi choosing mutum daya a cikinsu karaf idonshi suka fada kan Lamido...ya dage gira yana kallonta da kyau hadda sakin wani dan iskan smile cikin ranshi yana ayyana ita zaiyi selecting dukda ba daga hannu tayi ba kawai dai yanaso yana brain dinta da kullum Nur ke cewa she's genius she's this she's that..yau yanaso ya kure brain din nata...daga nan inda yake tsaye yayi pointing dinta da finger dinshi yace"You.."da sauri ta dago idanunta saidai suna sauka cikin nashi ta sake mai dasu kasa...still yana duban inda take yace"fito kiyi briefing namu akan topic din ba kece class rep ba?.."ya karasa mgn still da wani killer smile a face dinshi...ita kuwa qala batace ba ta mike daga seat dinta ta fito...ta juya taga sunan topic daya rubuta snn ta sake juyawa tana facing class din making sure bata kalli inda yakeba don kada ma ya zuba mata wadan nan idanun nashi yasa ta kasa ta6uka komai...bayani ta shiga yi musu dalla dalla kaman ba briefing dinsu yace tayi ba...tunda ta fara dama ya jingina da wall ya wani lumshe ido yana sauraronta sam baiyi tunanin zata iya ba...a yanda take explaining ma sai yakega kaman koshi da yake certified gynaecologist bai zama lallai ya iya yanda tayi ba..sam baiji dadin hakan ba kuma dan so yayi ya kunyatata a gaban Nur da kullum yake kiranta genius...yanxu kam ko da bai yadda she's genius ba tabbas yasan she's brilliant tunda har ta iya explaining abunda ba'a koya mata ba haka..daga yanayin yanda take magana kuma ya fahimci kaman she's used to it dan babu wani alaman tsoro ko rashin sabo a tattare da ita...duk sai yaji ranshi ya fara 6aci all of a sudden...hada ido sukayi da Nur aikuwa ya dage gira irin ya kaga?..shi kuma ya dauke kanshi ba tareda ya kalleta ba yace ya isa haka ta koma ta zauna...6oyayyen ajiyan zuciya ta saki cikin ranta tace"Finally"..sa zahiri kuma batace qala ba ta wuce ta koma seat dinta..shi kuma ya dora daga inda ta tsaya...bayani yake musu sosai shima irin bayanin da bai ma ta6a zaton zaiyi musu ba..suma kuma class din suna participating sosai...nan take yaji ashe yin lectures dinma is not as bored as he thinks...a da kawai gani yake irin boring lectures zasuyi sai kuma yaga ba haka ba baisan ko sbd class din suna participating bane...yana karasa topic din data fara ya shiga yi musu dayan shima kuma suna understanding sosai...a takaice saida suka dauki almost 3 hours kafin su gama...bayan ya gama amsa tambayoyinsu ya sake jaddada musu mgnr presentation da zasuyi ran Thursday snn yayi musu sallama ya fita mai girma provost yabi bayanshi...har ya fara sauka stairs Nur ya bishi da sauri suka shiga sauka tare yace"ko baka fada ba nasan u enjoyed it"...harara kawai ya watsa mashi baidai ce komai ba...shi kuma ya saki wani smile tareda dan lowering voice dinshi yace"and ya kaga brain din Lamido?..hope you are now satisfied?.."tsaki kawai Bobby ya saki yaki kuma kulashi...saida suka fito yace mishi"zamuyi dropping dika ne?.."Nur yace"don't bother nazo da mota kawai dai dan Allah kace ina gaida su pretty idan kaje gida"...bai sakeyi mashi mgn ba ya shiga mota bayan driver ya bude mishi..shima drivern ya zaga ya shiga snn ya tayar da motar suka tafi...shi kuma Nur saida ya shiga office ya dauko wasu files snn ya shiga nashi motan shima ya wuce.

🤍Dr.BOBBY🤍Where stories live. Discover now