Chapter ten

585 11 3
                                    

🤍Dr.BOBBY🤍

By Aysha Rano✨

Wattpad@aysharano22

10

ASALIN LABARI...

Lokacinda Attahir wato mahaifin Bobby yakai ma mahaifinshi Wazirin Gombe mgnr yanason Auren Nadia daya hadu da ita a kano kai tsaye yace bai amince ba sbd kasancewarta ba bahaushiya ba...hankalinshi ya tashi sosai ganin da gaske waziri naso ya rabashi da matar da yafi kauna a dunia..ya jema mahaifiyarshi da mgnr itama ta nuna batada taimakon da zata iyayi masa har tunda mahaifinshi yace ya hakura da ita kawai ya hakura...bai hakuran ba yacigaba da lalla6a waziri yana nusar dashi illar nunama wanda ba yarenku daya ba banbanci...ya kuma nusar dashi cewa har tunda ta kasance musulma kuma yar Nigeria yana ganin ko addini bai haramta mishi aurenta ba...ran waiziri ya 6aci sosai ya kuma ce matukar shi ya haifeshi bazai ta6a amince mishi ya auri inyamura ba...wnn mgn ba karamin daga hankalin Attahir yayi ba...step brothers dinshi da suke ganin waziri ya fifitashi a kansu nan suka samu damar shiga suna cigaba da ingizashi kan kar ya yadda ya amince ya hada jini da inyamurai wnn zuga kuma yayi tasiri a wurinshi sosai...Attahir da yaga bashida wani mafita kuma bazai iya hakura da Nadia ba kai tsaye yaje ya samu kakarshi mahaifiyar waziri knn yayi mata bayanin duk abunda ke faruwa nan kuma ta goyi bayan lallai sai an aura mishi matar da yakeso...hakan ba karamin 6ata ran waziri yayi ba amma ya hakura ba don yanaso ba ya tura aka nemo masa auren yarinyar har Enugu state bisa umarnin da mahaifiyarshi ta bashi kan lallai lallai ya aurama Attahir matar da yakeso idan baiyi haka ba kuma itama zata tsine masa kmr yanda yayi ikirarin zai tsinewa nashi dan.

Cikin lokaci kankani akayi bikinsu aka gama...sbd sanin da yayi cewa yan uwanshi da mahaifinshi ba son auren suke ba sai ya nema mata gida a kano ta zauna itama tacigaba da karatunta...tsakaninshi da Gombe saidai yaje ya gaisa dasu ya dawo kanon ma kuma bai cika zama ba sbd a lokacin yana aiki a Delta state...tun bayan aurensu kuma ko mutum daya baizo daga cikin 'yan uwanshi da sunan yazo ganin matarshi ba...a haka suka dauki tsawon shekara daya bata ta6a ganin wani nashi a inda take ba..a lokacin ta damu sosai da rashin zuwan nasu shi kuma saidai ya bata hakuri yace mata komai zai wuce...ana haka ya samu kira daga waziri kan lallai ya tattaro ya dawo Gombe da zama a cewarshi wai matarshi ke hanashi zuwa ziyararsu yanda ya kamata...baiyi nasa musu ba ko kadan as baison ya sakeyin laifi a wurinshi haka ya tattarata kaman yanda wazirin yace suka koma gidanshi dake cikin Gombe...da farko Nadia taji dadin komawan nasu sbd tana ganin idan tana kusa da yan uwanshi zasufi saurin kar6anta a matsayin suruka sai kuma daga baya ta gane mutanen nan bazasu ta6a kaunarta ba...kyara da tsangwama ba kalan wanda bata gani ba a wurinsu abun har ya kai ko taro sukeyi bata isa ta shiga cikin matan brothers dinshi ba dan zasu yita jifanta da munanan kalamai suna cewa ita inyamura ce..hatta yaransu sunan da suke kiranta dashi knn inyamura...a lokacin data samu cikin Sumayya tayi farin ciki sosai sbd tana ganin kilan idan ta haihu zata iya samun soyayyar waziri dana sauran 'ya'yanshi ko dan sbd abunda zata haifa...mahaifiyar mijinta dama bata ta6a samun matsala da ita ba hakama Munubiya..kawai dai basa iya sakewa su nuna damuwa da ita sosai sbd gudun 6acin ran waziri...duk wnn abun da ake Attahir bai ta6a daga baki yace zaiyi mgn ba sbd yasan ko yayi ba amfani zaiyi ba tunda goyon baya suka samu wajen waziri...'yan uwanshi da dama tuni yasan basa kaunarshi sbd soyayyan dake tsakaninshi da waziri shiyasa suke amfani da wnn damar suna rura wutar tsanarshi cikin zuciyar babanshi...yana sane sarai suke tunzurashi yake aikata duk abubuwan da yakeyi shiyasa bazai taba bude baki yayi complain ba fatanshi daya Allah ya rabashi da mahaifin nashi lafia.

Lokacin da aka haifi Sumayya Attahir yayi farin ciki sosai hakama qanwarshi mahaifiyarshi sun tayashi murna matuka saidai babu daman nunawa sbd waziri...lokacin da ya dauketa ya kai masa ita ko kallonta baiyi ba yace ya fitar mishi da ita a wurin...wnn abu ba karamin 6ata ranshi yayi ba...yana ganin ko arniya ya aura bai kamata ace his own father yayi treating yarinyarshi irin haka ba..abun ya 6ata ranshi matuka...wnn dalilin yasa baiyi shawara dashi kan sunan da zaa sama yarinyar ba kamar yanda sauran 'yan uwanshi sukeyi duk wanda matarshi ta haihu shi ke za6an sunan da za'a sa...baiyi shawara da kowa ba yasa mata Sumayya sunan qanwar Nadia da bata dade da rasuwa ba a lokacin...aikam taji dadi sosai dan bata ta6a zaton zaisa sunan yar uwarta ba.

🤍Dr.BOBBY🤍Where stories live. Discover now