Chapter four

610 10 1
                                    

🤍Dr.BOBBY🤍

By Aysha Rano✨

Wattpad@aysharano22

04

Tafiyan almost 10 mins ne ya kawosu area classes...direct driver ya karasa inda aka tanada domin parking school bus din yayi parking snn students suka fara fita...Lamido da Billy ne karshen fita daga cikin motan as always...suna fitowa sukaci karo da Sa'eed dake jingine jikin motanshi yayi crossing legs dinshi yana kallonsu...murmushi kyakykyawa Aysha ta saki tareda nufan inda yake tana fadin"Besty nah"...shima murmushin ya sakar mata yace"yes my besty how are you?.."tace"ina lafia bsty yau kazo da wuri"..murmushi ya kara saki zaiyi mgn ya hango Billy dake tsaye dan nesa dasu tana tattabe baki irin a dole batasan da zamansu a wurin ba...daria sosai ta bashi ganin yanda take basarwa Aysha ma ta juya inda yake kallo sai taga Billy tsaye a wurin nan take itama dariyan ya kwace mata...saida sukayi me isarsu Billy ta gama cika taf saura kiris ta fashe Aysha ta karasa tareda kamota da sauri still tana smiling tace"haba mana Billynmu...me yayi zafi haka why are you frowning your face like this?.."harara Billy ta watsa mata tareda janye jikinta tace"malama let go of my hand badai ni kukema daria ba?..gani mahaukaciya koh"..da sauri Aysha ta sake riko hannunta tana jinjina rigima irin na Billy tace"Billy please mana..besty come and help me i can't handle her alone"...ba musu Sa'eed da har yanzun bai dena dariya ba ya karaso inda suke yana rungume da hands dinshi yace"C'mon mana Billy..we are not laughing at you sorry"...kyakyawar harara shima ya samu daga gareta kafin ta dan tabe bakinta murya can kasa tace"it's ohk na hakura and not because of you"...tayi pointing Sa'eed da hannunta..da sauri ya shiga gyada kanshi yace"hakan ma nine da godia hajia Bilkisu mai gadon zinare"...if you see yanda Billy ke tabe baki kaman wanda taga poopoo...mutanen nata kam banda kunshe daria ba abunda sukeyi...wato Billy is verry funny and annoying sometimes and yet she is the most coolest and amazing girl they both have ever come across...suna kokarin barin wajen wani saurayi ya karaso inda suke da sauri yana sanye da uniform exactly irin na Sa'eed idanunshi kacokam akan Aysha yace"Lamido i need to talk to you plss"...kallo daya tayi mishi tareda gyara tsaiwanta tana rungume da hands dinta tace"go ahead ina sauraronka"...kallon Sa'eed saurayin yayi then back to Billy before ya sake dubanta yace"Lamido in private plss...i can't talk in front of everybody"...tun kafin ya rufe baki Billy da tazo wuya tace"hello who are you referring to everybody...see tun wuri ma ka kama hanya ka bar nan cox she is not interested in talking to you and she will not listen to you"...fuskanshi na nuna tsantsan bacin ran da yake ciki ya sake tsayar da idanunshi kyam akan Aysha baya ko kiftawa yanaso yaga me zatace...ganin irin kallon da yake mata ta juya ta kalli Sa'eed sai taga shima kallon nata yake...ta juya ga Billy still itama idonta a kanta sai ta tsayar da idon kan saurayin da har yanxun ko blinking baiyi ba a hankali tace"am..Tajuddeen am sorry plss..i can't talk to you right now"..tun kafin ta rufe bakinta yace"really?..sbd friends dinki basa sona right?.. Lamido dan Allah why are you doing this to me?..tell me is it a crime to love you?..do you think bansan ciwon kaina ba da nake chasing dinki after all wulakancin da ke da friends dinki kukeyi min?..Lamido bakisan irin son da nakeyi miki bane..i love you so much wlh"...ya karasa mgnr cikeda rauni sosai...nan take Aysha taji tausayinshi ya kamata..koba komai Tajuddeen sonta yakeyi and duk mai sonka bai cancanci wulakanci daga gareka ba...amma she have no choice bataso tayi deceiving dinshi tunda ba sonshi takeyi ba...ganin yana kokarin barin wurin tayi saurin cewa"Tajuddeen am so sorry plss...kaga yanxun it's almost time for lecture amma i promise during break time zan nemeka"..da sauri ya juyo yana kallonta with a little smile yace"Really?.."daga mishi kai tayi a hankali nan take sai ga fara'a sosai kan fuskanshi yace"thank you so much Lamido..thank you"...bai jira jin me zata fada ba ya juya ya bar wurin da sauri...Billy ma ta bar wurin kaman zata tashi sama...Aysha ta juya tana kallon Sa'eed tareda langabar da kanta tana squeezing face dinta kaman zata fashe mishi da kuka...daria kawai Bestyn nata yayi tareda girgiza kanshi yana dan hararanta yace"what?.."hannu ta kai ta kama both ears dinta tareda narke murya tace"am sorry"..sake girgiza kan nashi yayi yana daria...ko minti biyu basu kara wurin ba suka nufi classes dinsu...a first floor suka rabu Sa'eed ya wuce class dinsu itama ta wuce 2nd floor inda nasu class din yake...direct seat din Billy ta nufa saida ta gama aikin rarrashi snn ta mike tana kokarin zama a seat dinta ta hangoshi ta window dan haka da sauri ta bar seat din nata tareda komawa can baya ta zauna sbd seat dinta a gaba ne and batason yanda yana lecture kuma gaba daya hankalinshi a kanta...kilan yau idan yaga bai ganta a gaban ba zai hakura...tana can ta fada tunani sai ji tayi colleagues dinta na fadin"Good Morning Sir"..shi kuma gaba daya hankalinshi ba kan gaisuwar da suke mishi yakeba so kawai yake ya lalabo inda take da ya sanyata a eyes dinshi ko zai danji dama dama...extreme end of class din ya hangota dan haka ya shiga takawa zuwa wurin idanunshi gaba daya suna kanta...yana sanye cikin yadin kufta dark arsh dinkin kaftan..kanshi babu hula sai gashinshi da yasha gyara yanata kyalli abunshi...right hand dinshi na sanye cikin pocket dinshi ya karasa gareta...daidai seat din da take zaune ya tsaya tareda zuba mata eyes dinshi...a jikinta taji yana kallonta amma sam ta kasa dagowa..tasan yanxu kaf class din hankalin kowa na kansu har wani shiru class din yayi ko tari ba maiyi duk sun tsaya kallon love...saida suka dauki almost 5 mins a haka ganin babu sarki sai Allah Aysha ta dago kanta a hankali tareda langabewa tana dan turo lips dinta ta sauke idanun a kanshi...wani murmushi taga ya saki kyakykyawa hadda gyara tsaiwa still kuma yana kallonta...a hankali ta dan daga kan nata aikuwa taga gaba daya class din an juyo ana kallonsu sai ta sake narkewa kaman zata fashe da kuka tana mishi signal ya dena kallonta amma sam kmr ma hankalinshi ba jikinshi yakeba...saida ya gaji da kallon nata dan kanshi snn ya juya har yanxun hannunshi cikin pocket dinshi ya dawo gaban class din ya tsaya...nan da nan duk suka dawo da kallonsu gareshi masu kuskus nayi masu kunshe daria ma sunayi...sai yanxun ya zare hanunshi daga aljihu tareda rungumewa ga chest dinshi yana fuskantar yan class din yace"class do you really want this lecture to take place?.."nan take suka hada baki wajen cewa"yes sir"...saida ya sake rungume hannunshi snn yace"then ask your class rep to come back to her normal seat"...yana rufe baki kuwa suka juya gareta kowa na fadin albarkacin bakinshi"Lamido come back to your seat plss...Lamido dan Allah ki dawo...Class rep ki taimakemu ki dawo...Lamido this Lamido that"..kowa dai yana fadan abunda yaga zai iya shi kuma gogan yana tsaye rungume da hannu yana kallonta...ganin yanda duk suketa faman yi mata magiya ta mike daga wurin fuskan nan ba sarari ta dawo front seat dinta ta zauna tareda folding hands dinta...Billy dake zaune bayanta banda smiling ba abunda takeyi...ko Allah yasan tana matukar son union din Lamido da Sir Abdool sbd ba karamin matching juna sukayi ba...shi kuwa saida yaga ta zauna snn ya sake takawa zuwa gabanta ya ajiye mata marker dake hannunshi yana binta da wani sassanyan kallo yace"you are going to be the lecturer today"..dagowa tayi da sauri tana kallonshi sai kuma ta shiga girgiza kai tace"Sir Please!"..shima girgiza nashi kan yayi yace"Lamido please!"..nan take class din ya dauki tafi da sowa...da yawa daga yan class din sunsan dama Sir Abdool nason Lamido coz ba iya boyewa yake ba...masu farin ciki nayi hakama masu black belle irinsu Binta Gumel🤪nayi...Bilkisu kam yau ji take kaman ta taka rawa sbd nishadi..gaskia Sir Abdool ba karamin dan soyayya bane...ganin babu sarki sai Allah Aysha ta dauki markern tareda bude bag dinta ta ciro medicated glasses dinta ta saka snn ta mike a hankali zuwa gaban board sai ta tsaya tana kallonshi wai ko zaiji tausayinta yace ta koma amma sai taga yama koma gefe yayi zaune abunshi...da kyar bakina ya iya furta"MashaAllah"...sbd tsananin kyau da glasses din idonta yayi mata...tunda nake ban taba ganin wanda yayima kyau kaman ita ba..gaskia ita kam Allah ya bata..she have everthing..she's from rich family sai kuma ga kyau ga brain ga class snn kuma ga kyakykyawan zuciya...'yan class din ta kalla suma dai daga masu yi mata daria sai masu yi mata gwalo hakan ya nuna batada wani option dan haka ta juya tana fuskantar Board din taji yace"our today's topic is Endocrine System"...bata juya ta kalleshi ba ta rubuta sunan topic din snn ta sake juyawa tana facing class din...a nutse ta fara musu bayanin Endocrine system tun daga introduction... gaba daya class din sunyi tsit suna sauraronta kuma suna fuskanta sosai dan dama ba yanxu suka fara jin lectures dinta ba...mostly ko tutorials zasuyi itake musu explanation...shi kam Sir Abdool kallonta kawai yake ful of love and affection..he loves this girl to the core..he loves her more than he could say...yanxun da yake sauraron lectures dinta sai yaji koshi bai zama lallai ya iya musu bayani haka ba..she really is intelligent..she is a genius shiyasa kullum sonta yake karuwa cikin ranshi har yakejin kmr heart dinshi zai fashe...he feel like yaje yayi hugging nata right now amma he won't dare...ita kuma Aysha explanation dinta takeyi sosai...komai saida ta fito musu dashi snn ta kammala kafin ta juya gareshi tace"Sir mun gama"..baice komai ba sai hands dinshi daya daga ya shiga clapping mata idanunshi a kanta nan kowa ya shiga tafa mata dan da gaske tayi kokari sosai...saida suka gama clapping din yace taje ta zauna...ba musu ta tafi ta zauna shi kuma ya taso yana tambayan if akwai mai tambaya sukace babu nan yayi musu sallama bayan yace suyi submitting assignment daya basu wa class rep ita kuma ta kai mishi office...yana barin class din suka fara tsokanarta wasu na fadin salon love dinsu da sir Abdool na burgesu wasu kuma na cewa kawai tayi accepting love dinshi dan sun dace da juna...itadai bata cema kowa komai ba ta tattara assignments din nasu ta tafi office dinshi...tana kai mishi bata tsaya ya jata da long story ba tace mishi zataje office din provost kan issue din Reproductive Health Lecturer dinsu data tafi maternity leave..haka nan ya hakura ya barta ta tafi ba dan ya gaji da ganinta ba..yasan ko zasu kwana nan yana kallonta bazai taba gajiyawa ba.

🤍Dr.BOBBY🤍Where stories live. Discover now