Chapter nine

532 7 1
                                    

🤍Dr.BOBBY🤍

By Aysha Rano✨

Wattpad@aysharano22

09

Ranan Thursday da wuri suka shiga school sbd sunaso su zauna da group dinsu before time na presentation...tun 7 suka hadu gaba daya class suna rehearsing karatunsu...karfe 8 daidai kuma suka fara lectures dinsu...inshort basu fito daga class ba sai around 1..suna fitowa suka nufi cafeteria don cin abinci...a ciki suka hadu da Sa'eed yayi musu reserving table suka karasa suka zauna kowa ya bada ordern abinda yakeso...sunyi shiru kawai abincin sukeci don ko breakfast basuyi ba suka fito...kaman daga sama kawai suka ga mutumi yaja empty kujera dake kusa dasu ya zauna...a tare suka dago kansu duk su ukun suna kallonshi...Tajuddeen ne sanyeda uniform dinshi as always yanata kallon Lamido yana sakin murmushi...Billy taja wani tsaki tacigaba da cin abincinta...shima Sa'eed cigaba da cin nashi yayi ba tareda yace komai ba...a hankali Lamido ta ajiye spoon din hannunta tana dubanshi kaman zata sa kuka tace"what?.."kaman jira yake yace"magana nakeso muyi dake kinata min wulakanci Lamido...dan Allah ki bani dama ko Hostel ne nazo sai mu tattauna a can"...yana rufe baki tace"ba damuwa u can come to the hostel anytime u like...yanxun dai kayi hakuri ka tafi cox muna gama cin abincin nn class zamu koma"...ya danyi shiru yana kallonta kaman bai yadda da abinda ta fada ba yace"U sure?.."cikeda assurance tace"💯Sure...just go we'll talk later"...bai sake cewa komai ba ya tashi daga wurin...sai kuma ya tsaya yana kallonta yace"i love you "...gyada mishi kai kawai tayi ya juya ya bar wurin...yana tafiya Billy kaman jira take ta dago tana hararanta tace" ki tabbata a kunnen Ammi duk wnn maganan da kukayi...shine hadda wani cewa yazo hostel ya sameki sbd tsoronshi kikeji koh?.."girgiza kai kawai tayi ta cigaba da cin abincinta as batada energy din rigima da Billy yanxu sai cikinta ya dauka...bestie dai yana zaune pretending kaman baya sauraronsu har suka kammala ya biya kudin gaba daya snn suka fita...su suka wuce female masjid dan yin sallah shi kuma ya koma class cox ya riga yayi sallah tun daxu...suna idar da sallah kiran provost ya shigo wayanta...ta dauka da sauri tana fadin"Good afternoon Sir"...yace"afternoon Lamido are you guys ready?..proprietor ya shigo tun daxu and in the next few minutes zakuzo Auditorium hope you are all set?.."tace"we are Sir "...yace" alright tell them mu hadu auditorium by 2".. a hankali tace"toh.."suna gama mgn ta ajiye wayan a hankali cikin ranta tana nanata Auditorium kuma?...Common presentation da zasuyi shine sai an kaisu har wani auditorium sbd shegen iyayi...tasan duk wnn ba plan din kowa bane sai na wancan inyamurin mutumin...kawai presentation za'ace su tafi har auditorium sbd neman magana.

Karfe biyun kuwa cikin Auditorium din yayi musu...basu jima da zama ba malamai suka shigo su wajen 4 hadda Sir Abdool dinta inji Billy😆..sai shi proprietor din sai provost...daga dan sama kadan malaman suka zauna inda aka tanadar musu kaman high table haka...bayan gaisuwa da dogon bayani daga malaman akace the 1st group should come forward... a yanda suka tsara abun dama ba gaba daya members na kowane group zasu fito ba..each group dunyi selecting mutum uku da zasuyi representing dinsu cox idan akace gaba daya kowa sai yayi bazasu samu gamawa da wuri ba...kaman yanda yake alphabetically group din farko nasu Lamido ne dan haka ba wasting of time suka fita ita da sauran colleagues dinta...first speaker ce ta fara musu bayani tun daga introduction zuwa definition of terms haka..bayan ta gama second speaker itama tayi nata Lamido kuma itace karshe...saida duk suka kammala ta amsa markern dake hannun colleague dinta tareda karasawa jikin white board dake daga gefensu ta zana diagrams dake cikin topic din nasu tayi labelling snn ta fara explanation...sosai Audit din yayi tsit tun daga dalibai har malaman kowa ya nutsu yana sauraronta...da yawa daga cikin malaman dama sun santa tunda akwai wani end of year presentation da sukeyi duk end of session and ko na last year da akayi itace tayi winning...bayan wnn akwai wani tradition da suke dashi a school din at the end of every session ana fitar da overall student for both Nursing and Midwifery departments snn kuma a fitar da Wanda yafi kowa point a gaba daya college din as the overall student of the year...zaayi printing qaton poster mai daukeda pictures na overallers din kowa da sunanshi dana department dinshi sai kuma point dinshi...haka zaa kafe wnn postern kusada general notice board snn a sake kafe wani ta wajen admin block...so da yawa cikin malaman ko basu santa a zahirinta ba sun santa either a wancan poster tunda last year ita tayi overalling a department dinsu ko kuma a end of year presentation da akayi na last year...shi kanshi Bobby yau sai yaji wani abu daban gameda yarinyar...bama ita kadai ba gaba daya class din sun burgeshi sosai coz sunada kokari..cikin ranshi yake ayyana wai haka duk students din nashi suke da kokari ko kuwa iya class dinsu ne haka?..yana cikin tunaninshi yaji Audit din ya kaure da wani irin loud tafi yana dubawa sai yaga ashe sun gama shine ake musu tafi...babu 6ata lokaci group two suma suka fito sukayi nasu followed by group three wanda sune last group...bayan sun gama gaba daya student affairs dinsu ya tashi yana praising dinsu tareda karfafa musu gwuiwa kan karatunsu...bayan ya gama provost ma yayi nashi sai kuma mai gayya mai aiki Alhaji Dr Bobby jikan Waziri lol😃..shima praising dinsu yayi sosai snn ya fadam each group marks din da sukayi scoring wanda dashi zaayi amfani a matsayin c.a dinsu..bayan ya gama malamai suka fara fita followed by students din...kafin su karasa class kiran Sir Abdool ya shigo wayanta...ta dauka tana gaisheshi yace"Lamido can i please see you now?.."ta danyi shiru tana tunanin ne zatace mishi ya sake cewa"ba dadewa zakiyi ba Please!"...ba yanda ta iya haka nan tace mishi gata nan...ta dubi Billy da suke tafiya tare tace"kinji Sir Abdool wai inje...ni kuma na gaji wlh so nake in koma hostel in kwanta"..kar6an text book dake hannunta Bilky tayi tace"yace fa ba dadewa zakiyi ba..kiyi hakuri kije ni zan jiraki a class"..Aysha tayi murmushi tana jinjina wnn so da Billy ke mishi ta juya ta tafi...tazo daidai kofan office dinshi tana shirin budewa Bobby da Nur suka fito daga office din Nurun...ta dauje kanta da sauri sakamakon idanunshi da suka sauka a kanta...ta budr office din da sauri ta shiga su kuma suka wuce don dama tafiya gida zasuyi...tana shiga ya mike daga zaunen da yake tareda dawowa kan soafer ya zauna ya nuna mata kusa dashi itama batayi mishi musu ba  zauna...ya tsura .ata ido yana sakin wani shegen murmushi yanajin ina zai saka yarinyar nan ne tsabar son da yake mata...itadai kanta na kasa as batason wnn kallon kasa kasan da yake mata...shi kuwa rasa kalmomin da zai furta mata yayi sai kawai ya kamo both hannayenta yakai su bakinshi yayi kissing kafin ya ajiye yana fadin"i love you"...daure fuska tayi sosai tana dan turo baki ta kalleshi...yasake sakin wani murmushi yana shafa gashin kanshi yace"Ya Allah"...ganin ta sake tsuke baki ya kama ears dinshi yace"am sorry sonki ne yayi min yawa wlh Lamido..so accept my apology inshaAllah bazan kara ba"..batace mishi komai ba sai mikewa da tayi yace"please forgive me"..ta gyada kanta kawai ta fita daga office din.
Da dare Hostel suna cin abinci itada Billy kiran Daddy ya shigo wayata...tayi saurin hadiye na bakinta ta sake daidaita nutsuwarta snn ta daga tana cewa"Hello daddy barka da dare"..Daddy yace"sallamanki kenan ba?.."da sauri tace"sorry daddy..salamu alaykum barka da dare"..yace"barka dai ya studies?..hope you are doing well?.."tace"inayi daddy ya aiki"..yace"Alhamdulillah na dawo gida..ba wani matsala koh?.."tace"ba komai daddy"yace"MashaAllah bawa Bilkisu waya"..ba musu ta mikama Billy wayan..itama ta kar6a da sallama tana gaisheshi..yace"inda kika fita hankali knn?..ya karatu fatan ba wani matsala?.."tace"babu komai daddy"..yace"to Alhamdulillah aci gaba da dagewa sosai..Allah muku albarka"..Billy ta amsa da"Ameen mungode daddy Allah ya kara girma"..shima yace"Ameen"..daga haka ya kashe kiran...Aysha ta kar6i wayan tana sauke ajiyar xuciya tace"sai yanxu hankai na ya kwanta..da naga kiran nayi zaton ko wani laifin nayi"...Bilkisu ta girgiza kai tana cigaba da cin abincinta tace"bakida gaskia ne ai shiyasa".

🤍Dr.BOBBY🤍Where stories live. Discover now