Chapter six

549 7 0
                                    

🤍Dr.BOBBY🤍

By Aysha Rano✨

Wattpad@aysharano22

06

Suna zaune Bobby ya shigo rikeda waya a hannunshi kai tsaye ya karaso ciki tareda mikama Aunty Sumy wayan yace"Its your call"...ba musu tasa hannu ta amsa wayan tareda karawa kunnenta tayi sallama...a daya bangaren Hafsa tace"wa'alaiki salam Maman Miemie..inata kiran wayanki no answer shine nace bari inyi trying na Bobby in gani sai gashi kuma ya shiga..Ilham ce ta dameni wai tanason mgn daku"..Aunty Sumy ta dan saki murmushi tace"oh Hafsa wai kece?..dama kinada Number Bobby knn?.."Hafsa tace"bani dashi wlh Ilham din ce ta bani wai tunda naki baki dauka shi a kirashi..gata kuyi mgn"..daga haka ta mikama ilham dake zaune kusada ita wayan...yarinyan da bazata haura 8 to 9 years ba ta amsa wayan full of happines tace"Auntyyy"..aunty sumy ta saki daria jin yanda taja sunan nata tace"na'am 'yar gidan aunty ya kike?.."tace"am fine aunty just missing you..i want to come back home"..aunty sumy tace"hope dai ba rigima kikema aunty hafsa ba koh?.."tace"bana rigima aunty kullum sai mun fita yawo..yau ma saida aka kaimu shopping dasu fadeel"..aunty sumy tace"inyee 'yan gidan aunty hafsa..ilham banda fitina kinji?..kuma banda kiriniya banda sa aunty hafsa magana"...daria ta saki sosai kaman wata babba tace"aunty i want to speak to everyone please..where is my Uncle Bobby?.."Aunty sumy tayi putting nata on speaker snn tace"your uncle bobby is here"..cikin excitement ilham tace"my uncle bobby"..yace"yes my mummy how are you?.."tace"am fine uncle bobby ya aiki?.."yace"aiki fine ilham gobe zaki dawo ba?.."tace"yes..kasan me na siyo muku daxu da mukaje shopping?.."yace"sai kin fada mummy"..suna jin yanda ta danyi kasa da murya snn tace"na siyo maka cheesy na siyoma uncle sab sweet na siyoma yaya chocolate snn na siyoma Mummy da aunty biscuits"..dan bata rai Bobby yayi yace" seriously ilham?..of all abubuwan dake wajen ki rasa abunda zaki siyomin sai cheesy?.."daria ta saki sosai tace"to ba kace min kana son cheesy ba..shknn zan sake maka wani yanxu ka bama Mummy da uncle sab muyi mgn"..bai sake mgn ba ya mikama Mummy wayan..nan ma hira suka sha sosai sai kace wata babba snn sab ya karba shima aka sha hiran dashi...miemie ce karshe aka kai mata wayan har daki nan ma suka dora daga inda suka tsaya...Bobby na duban Mummy in a serious tone yace"Mummy nidai kada a sake bari wani daga cikin mutanen nan yazo yace zai dauki yaran nan bana so wlh..after duk abubuwan da suka yi mana yanxub zasu ringa wani zagayowa suna daukan yara sbd mu yadda dasu?.."girgiza kai Mummy tace"kaidai ka fiya riko wlh Bobby..baka manta abu komai qanqantarshi...abun daya faru ya riga ya faru saidai a kiyaye gaba"..aunty sumy tace"kuma Mummy duk abubuwan da suka faru babu ruwan hafsa a ciki..lokacin ma tana england komai ya faru so bazan iya hanata ba muddin ta nuna tanason daukansu koba komai qanwar mahaifinsu ce"..wani kallo Bobby yayi mata yace"sbd tana qanwar mahaifinsu bashi zai daman zuwa koda yaushe tace zata daukesu ba..idan abun da gaske ne meyasa shi baban nasu ya kasa nemansu duk tsayin wadan nan shekarun sai ita?.."dafe goshi kawai Mummy tayi dan tasan kome zaa fada bazai yadda ba tunda ya riga ya dauki zafi haka...itama aunty sumy sanin halinshi yasa taja bakinta ta tsuke tunda it's of no use trying to explain things to him bazai taba fahimta ba..ya mike zai koma flat dinshi Mummy ta kira sunanshi...ba musu ya dawo ya zauna yana fuskantarta...itama tana dubanshi tace"wane magana kukayi da Nuru dazu kace bazaka iyaba?.."da sauri ya kalli Nur da yayi wani kasa da kai sai kace mutumin kirki...wato ma karanshi yazo ya kawowa Mummy sbd yasan ita kadai zata iya mishi dole koh...rai a dan bace Mummy tace"bada Bobby nake mgn bane?.."a hankali yace"Mummy lecturing fa yakeso inje inyi..sbd Allah Mummy ta ina zan wani fara shiga class ince zanyi lecture bayan ba tabayi nayi ba..idan tsakani da Allah ne shi meya hana bazai je ya koya musu da kanshi ba"..yana rufe baki Nur yace"amma kasan da field dina ne ba abunda zaisa ma in tambayeka sbd nasan 6atamun lokaci zakayi..kaine gynaecologist dan haka kai ya kamata ka koya musu ba ni ba"...wani irin daci yaji yana taso mishi tun daga throat dinshi zuwa bakinshi..gaba daya sai ya zama speechless a wurin..nan take Mummy tace yaje ya  taimaka musu koda na one or two days ne...as usual ya amsa mata da toh snn ya mike zuwa flat dinshi...Nur ya bishi da kallo yana kunshe daria...sallama yayi dasu Mummy snn ya mike zuwa flat din Bobby ya sameshi kwance kan three seater a parlor idanunshi lumshe yayi pillow da hannayenshi...murmushi ya saki tareda sunkuyawa saitin kunnenshi yace"this is your punishment for making Lamido cry"...Bobby da yaji mgnr kaman daga sama baisan lokacinda ya mike zaune da sauri yana kallonshi ba...mamaki ne karara a fuskanshi jin abunda yace...shi kuwa Nur juyawa yayi ya fita daga parlon yana daria kasa kasa yasan yanxu komai taurin kanshi dole yayi abunda yakeso tunda Mummy tasa baki...Bobby kam sbd tsabar takaici baisan time daya dunkule hannunshi tareda naushin kujeran da yake kai ba yana fadin"Fuck you Nur".

🤍Dr.BOBBY🤍Where stories live. Discover now