*Ta Zama Haja! 04*
*Sadik Abubakar*
*Lafazi Writers*https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
Ɗan gajeren tunanin da ta yi ke nan a tsaye. Zaliha ta yunƙura tare da dafa ƙafafuwanta, cikin muryar da kuka ya raunana ta ce, "Ummana me yasa za ki biye wa ruɗin duniya da shaiɗanun mutane? Na yi miki alƙawarin zan auri wanda kike so, akan me za ki bari shaiɗan ya yi galaba a kanki? Har ya nemi ya raba ki da imaninki! Umma shekara da shekaru kina bin Allah da ɗa'a, kina bin umarninSa da haninSa amma a yini guda ki ɓata nagartattun ayyukanki? Umma ta dalilina ba na son ki rasa imaninki, ina roƙon ƙi don Allah ki fasa zuwa wajen bokan nan! Idan Alhaji Saminu ya zo zan faɗa masa ya turo magabatansa na yarda zan aure shi." Tana maganar tana kwararar da hawaye, amma ita kuwa Umma ko a jikinta, wai an yakushi kakkausa. Idonta ya gama rufewa akan naira, babu abin da take hange illa irin alherin da za ta tatsa a jikin Alhajin idan 'yar tata ta amince ya zama sirikinta.
Zaliha ta ci gaba da magana cikin kukan, "Ki yi haƙuri da duk abin da ya gabata na ɓacin rai da na haddasa miki, ki yafe mini."
Sai yanzu ta buɗa baki ta ce, "Ba ki taɓa ɓata mini rai ba har zuciyata ta soyu kamar wannan lokacin. Ke sanin kanki ne babu yadda za a yi uwa ta cutar da 'yarta. Farinciki nake nema miki da ni kaina. Bai kamata na ƙyale ki ki jefa kanki wajen da za ki sha wuya ba, daga ƙarshe a zo a yi abin da ake cewa, ka sayar da akuya amma ta dawo tana ci maka danga. Yanzu aure ake yi wajen da mutum zai huta ya ji daɗi, danginsa ma su huta. Allah Ya yi miki farin jini da kyau, sam ke ba matar ƙaramin mutum ba ce."
Kunya mai cike da takaici ta turnuƙe zuciyar Zaliha, "shin me Umma take nufi da wannan maganar? Da ma idan mace tana da kyau da farin jini sai ta zama abar alfahari? Ta zama kamar wata hajar kasuwa? Har a ce ta fi ƙarfin wani saboda ƙarancin abin hannunsa, sai mai kuɗi?" Tunanin da ya kewaye zuciyarta kafin Umman ta ɗora da faɗin, "Ki cire Abdullahi daga ranki kin ji, Allah Ya yi miki albarka. Ki je ki yi wanka ki huta, ni bari na ɗora mana abincin rana."
"Amin Umma na gode!" Ta faɗa sannan ta miƙe ta nufi ɗakinta. Ajiyar zuciya uku ta sauke a jere daidai lokacin da ta aza ƙugunta bisa gefen gado. Zuciyarta ta shiga hakaito mata wata daddadar hira da suka taɓa yi ita da sanyin idaniyarta.
"Shi ne ɗazu a makaranta ina ba da hadda kake cewa na sake ko? Kuma daidai nake yi."
Cikin sigar shagwaɓa take maganar, dariya ya yi sannan ya ce, "Ba wani daidai da kika yi, kin fiye ƙorafi dai. Ba ki ga ba ke kaɗai ba na yiwa haka ba."
"Allah kuwa daidai na yi, har sau biyar fa ina maimaitawa, kuma ba gyara mini ka yi ba."
Ya sake tintsirewa da dariya ya ce, "Kin san me? Watau daɗin muryarki idan kina karatun Ƙur'ani ta daban ce. Kunnuwana ba sa taɓa gajiya da sauraren daddaɗan sautinki."
"Hmm! Za ka fara tsokanar taka ko? Ina wani daɗi a muryar da take karkarwa?"
"Allah ba zancen wasa ko tsokana, gaskiya ce. Don haka ma daga yanzu idan za ki yi hadda naɗar sautin zan yi, sai na riƙa saurare kodayaushe na yi buƙata."
"Cabɗijan! Ai kuwa shiru zan yi na ce ban iya ba, ko kuma na ƙi zuwa ranar karɓar haddar."
Cikin dariya ya ce, Bulala goma ce ba yawa, kin dai sani."
"E na yarda ko ma ɗari ce a yi mini."
"Da ƙarfi fa zan yi miki, ba kamar yadda zan yi wa sauran ba." Ya ƙarasa da ƙyalƙyala dariya.
Murmushi ta yi ba tare da ce komai ba. Suka yi shiru cikin daddaɗan yanayi da nishaɗi. Zuwa can ya nisa da faɗin, "Ina roƙon Allah Ya ba mu 'ya'ya masu kama da ke, masu irin halinki, masu basirarki da kunyarki."
"Hmm! Kai ko, na fuskanci yau zolaya kake ji. Tun da ka zo kake tsokana ta. Duk waɗannan nagartattun siffofin da ka zayyano ai kai kake da su."
"Ko kuma ke ɗin ce mai zolayar ba."
Siririn murmushi ta yi tare da sakar masa wani kallo mai jefa zuciya cikin saƙe-saƙe kala-kala. Cikin lallausar murya ta ce, "Abban Khakil!"
"Waye Abban Khakil kuma, me ya faru da shi?"
Cikin ɗariya mai ɗauke da nishaɗi haɗi da walwala ta ce, "Wani kyakkyawan saurayi ne da aka jima ba a yi kamar sa ba a tarihin duniya, sai wata 'yar almajirar yarinya ta yi sa'ar zama sarauniyar birnin zuciyarsa. Shi ne take fatan idan sun tsinci kansu a duniyar ma'aurata, Ubangiji Ya ba su da namiji, ya raɗa masa suna Khakil, sai ta riƙa kiran sa Abban Khakil."
Kallon ta kawai yake yana sakin murmushi cike da mamakin kalaman da take furtawa, da ta ɗan tsagaita sai ya nisa ya ce, "Kai Ma Sha Allah! Amma sun birge ni matuƙa, musamman ma ita yarinyar da ta kasance mai ƙanƙan da kai. Hala ba a wannan zamanin suke ba ko?"
Ta sake aika masa da wani irin kallon ƙauna ta ce, "Ai kuwa a wannan zamani suke, yanzu haka ma suna tare da juna yana sakar mata ƙayataccen murmushi da kalaman da ke sawa ta ji ta tamkar wata sarauniya."
Dariya ya yi sosai yana ji a ransa lallai wannan yarinyar ta musamman ce, ta haɗa komai. Ga kyau, ga iya magana mai ratsa zuciya. Cikin dariyar ya ce, "Ai kuwa ta fi sarauniyar ma a wajensa, yadda yake jin ta a ransa tamkar carbin ƙwai. Kuma indai wannan shi ne burinta, to ya lamince mata tun yanzu ma ta riƙa kiran sa Abban Khakil ɗin."
Nishaɗi da fara'arta suka ƙara yalwatuwa sosai, yayin da shi kuma yake bin ta da wani asirtaccen kallo. Ta sunkuyar da kai ta ce, "Idan kuma mace ce na bar maka ka zaɓa mata sunan da kake so."
"Idan mace ce sunan Umma za mu raɗa mata, kin ga mun samu Umma babba da Umma ƙarama."
Murmushi ta yi kawai ba tare da ce komai ba. Sun jima sosai suna wannan hira mai cike da kauna. Da zai tafi ta rako shi har waje, ya dube ta ya ce, 'To Maman Khakil ni zan wuce sai yaushe?.''
Sunkuyar da kai ta yi cike da kunya ta ce "Kai ɗin nan ko! Ka gai da gida, kuma ka kula mini da kanka."
Yayin da ta kawo nan a tunanin, sai ta saki ajiyar zuciya, ta miƙe da kyar ƙafafuwanta ke ɗaukar ta. Banɗaki ta shiga ta watsa ruwa sama-sama. Fitowarta ke da wuya aka fara kiran sallar Azahar, alwala ta yi sannan ta koma ɗaki ta yi salla ta janyo jakarta ta Islamiyya da nufin ta bibiyi darusan baya. Amma sam sai abin ya gagara, da zarar ta fara ko layi guda ba ta kaiwa sai tunani ya katse ta. Ta yi ƙoƙari kauda tunanin amma abin ya gagari Kundila. Tattarawa ta yi ta ajiye ta ɗan kwanta bisa sallayyar, wani barci marar daɗi ya yi awon gaba da ita.
"Assalama alaikum wai ana sallama da Zaliha?" Murya wani yaro ce da ba zai wuce shejara goma sha biyu ba, lokacin da ya shigo tsakar gidan.
"In ji wa?" Umma ta tambaye shi.
Yaron ya ce, "Wani mutum a mota yana waje."
"To je ka ce tana zuwa."
Yaro ya fito ya faɗa masa abin da aka ce. Mutumin ya zaro naira dari biyu sabuwa kar ya miƙa masa, daidai lokacin Umma ta leƙo ta ga ko waye? Alhaji Saminu ta gani yana jayayya da yaron ya karɓi alherin da ya yi masa ya ƙi, yana cewa, "Wallahi an hana ni karɓar kuɗin wanda ban sani ba, na gode ka bar kuɗinka."Yana faɗa ya wuce abinsa.
Da sauri Umma ta koma ciki, Zaliha na ɗakinta ta ji lokacin da yaron ya shigo da abin da ya faɗa. Kuma ta tabbata Alhaji Saminu ne ya zo. Kai tsaye Umma ta nufi wajenta ta ce, Maza ki shirya, Alhaji ne ya zo. Saura kuma idan ya ba ki kuɗi ki ƙi karɓa kamar yadda kika yi a waccan ranar, za ki ga yadda zan yi da ke a gidan nan."
Uffan Zaliha ba ta ce mata ba, sai dai takaici da ke cin ranta. Ita ta rasa yadda aka yi mahaifiyar tata take masifar son kuɗi haka, ba a cikin wahala suke ba. Abbanta ya tsaya musu tsayin daka, babu wata buƙata da ta taɓa gagarar su a iya saninta, to saboda me Umma za ta riƙa yin haka? Tambayoyin da ke kai kawo a zuciyarta ke nan, wanda kuma ba ta da amsarsu sai dai addu'a.
Nan ta miƙe a wulaƙance ta fito wajen Alhaji Saminu, sallama ta yi masa tare da gaishe shi, "Ina yini?"
Ya amsa da sauri, jin alamar kamar yau akwai sauyi a yadda suka saba, tunda ga shi har gaishe shi ma ta yi. Sai dai daga kalmomin can guda biyu 'ina yini', ba ta sake furta komai ba. Shi kaɗai ya yi kiɗansa ya yi rawarsa. Kamar dai wancan zuwan, ashe yau ma Umma ta biyo ta zaure tana laɓe tana kallon su, ganin yana ta magana ta ƙi tanka masa ya fusata Umma. Komawa ciki ta yi ta sako hijabi ya fito, kai tsaye wajensu ta tinkara ta fara zazzaga wa Zaliha ruwan masifa, "Zaliha ba na son rashin mutumci da rashin albarka, wannan ai iskancin banza ne! Ya ya za ki tsaya ƙerere a gaban mutum yana miki magana kin yi banza da shi idan ba ki yi a hankali ba akan wancan yaron sai na tsine miki"
Kafin ƙiftawar ido jama'a sun kewaye wajen, sun yi musu kuri, ciki har da yaya Abdul.
Alhaji Saminu ya durƙusa har ƙasa yana cewa, "Baba a yi haƙuri ba komai, ai lamarin yaran zamani sai a hankali za ta gane."
"Wannan ai sakarci ne, ga mutanen kirki sai ta biye wa mayaudari wanda ba auren ta zai yi ba. To daga yau kin daina zancen a waje, na ga ta iyashegen. Alhaji idan ka zo ka rika shiga ciki kawai, ai kai ma ka zama ɗan gida. Kuma indai Zaliha ce na ba ka ita halak malak!"
Cike da murna ya ce, "To Baba na gode sosai, Allah Ya saka da alkairi Allah Ya ƙara girma. Ni zan koma." Ya saka hannu cikin aljihu ya zaro wasu kuɗaɗe masu yawa ya miƙa mata tare da cewa, Ga wannan, a gai da mini Abba idan ya dawo."
"To ikon Allah! Har da ɗawainiya kuma, to an gode Allah Ya ƙara arziki."
Ya buɗe mota ya shiga ransa fes, ita ma Umma ciki ta koma ranta wasai, tana jin burinta ya fara cika.
Ita kuwa Zaliha tunda ta tsugunna ta haɗa kai da gwiwa take wani irin kuka marar sauti amma sai azabar raɗaɗi a zuci, irin kukan nan ne mai illata zuciya. Mutanen da ke wajen sai mamakin abin suke, wasu na cewa, "Me yasa Umma za ta aikata wannan ɗanyen aiki na zubar wa kai ƙima da mutumci?" Wasu kuma suka riƙa ba wa Zaliha haƙuri da nasihohin ta bi mahaifiyarta kada ta saɓa mata.
Kowa ya watse aka bar Zaliha durƙushe, yaya Abdul ya matsa kusa da ita ya tsugunna tare da cewa, "Ina son ki yi duk abin da Umma ta umarce ki matuƙar bai saɓa wa shari'a ba, idan har kika saɓa mata to kada ki ce kin taɓa so na. Saboda haka idan har da gaske kike so na, to ki bi zaɓin da ta yi miki, ki aure shi ni na bar masa. Yanzu ina son ki tashi mu shiga gidan ki ba ta haƙuri bisa ɓata mata rai da kika yi."
Sam ba ta yi tunanin yana wajen ba uwar ta yi haukan da ta yi, da irin miyagun kalaman da ta furta a kansa, sai yanzu da ta ji saukar sautin muryarsa a masarrafar sautinta. Ji ta yi da ma ƙasa ta tsage ta shige, ya fi mata sauƙi akan ta sake haɗa ido da shi. Cin mutumci da cin fuskar da Umma ta yi masa ya yi yawa. Shin wai me ya yi mata ne haka? Wannan ne tunanin da ya game Ilahirin zuciyarta, ta gaza koda motsawa.
Ya ci gaba da cewa, "Ki tashi mu shiga ba komai, kuma ba na son ki sa wannan abin a ranki, komai ya wuce."
Shiru ba ta ce uffan ba kuma ba ta da niyyar tashi daga wajen, "Kowa ya tafi fa, daga ni sai ke. Ki tashi mu shiga."
Da kyar ta miƙe kanta sunkuye suka shiga, Umma na zaune a falo ta baje kuɗin nan tana ƙirgawa tana sakin fara'a.
"Me kuma ka biyo ta ka yi maye?" Umma ta faɗa tare da aika masa wata mummunar harara.
Murmushi ya yi sannan ya ce, "Yi haƙuri Umma, da ma na zo ne na ba ki haƙuri kuma na sanar da ke cewa Zaliha ba ta da laifi. Kamar yadda kika ce ni ne mai laifi, amma ki sani ni ba yaudarar ta nake ba, Zaliha kanwata ce ba zan taɓa so ta shiga damuwa ba, hakazalika ba zan taɓa zama sanadin da za ta saɓa miki ba. Saboda haka ni na haƙura, Allah Ya ba su zaman lafiya, ke Zaliha ki ba wa Umma haƙuri kin ji. Ni na tafi." Yana faɗa ya juya ya fice.
"Munafiki, ka ji da shi. Zaliha ce dai ƙwaleken ka. Yo ban da tsaurin ido ma irin naka, ina kai ina wannan tsaleliyar yarinya? Kawai don ka karantar da ita sai ka ce sai ka aure ta. Nawa ka ajiye a asusunka? Ta ya ya za ka iya riƙe ta? Zantukan da Umma ta riƙa yi ke yayin da take ƙirgar kuɗaɗen nan.
Raɓawa Zaliha ta yi za ta wuce ɗakinta tana kuka, Umma ta ce, "Ko kukan jini za ki yi sai dai ki yi, wannan yaron na raba ki da shi ke nan har abada. Kuma Allah Ya kai mu gobe Alhaji Saminu ya dawo zan ce masa ya turo a yi maganar auren, cikin sati biyu kacal tunda mai hali ne, na san zai yi miki kayan ɗaki duka."
***
Tun a waje aka tari Abba aka fara tsegumta masa abin da ya faru, to amma dayake ba a idonsa abin ya faru ba bai yi tunanin lamarin ya ƙasaita haka ba. Yana shiga gida bayan ya gama cin abinci ya ɗan huta sai ya ce da Umma, "Wani abin ne ya faru ɗazu? Na ji Malam Isa mai wanki ya fara yi mini maganar Zaliha."
"Hmm! Kai ma ai ka san kwanan zancen! Akan dai wancan yaron ne da kuma shi Alhaji Saminu, amma na yi wa tufkar hanci."
Abba ya ɗan gyara zama ya ce, "Wai mene ne ke faruwa Saratu? Shin wai ita yarinyar nan tana son shi Alhajin ko kuwa ke ce kike son shi.?
A wulaƙance ta dube shi ta ce, "Wace irin magana ce wannan? Shi yasa na ce kana goya mata baya. To bari ka ji daga yau maganar auren Zaliha ta fara, ka kwana da sani. Ya ce a shirye yake da wuri yake so a yi a gama."
"To shi ke nan na ji, batun karatunta fa? Komai garaje ai a bari ta kammala sakandire ko?"
"A'a ba sai ta gama ba, zai bar ta ta ƙarasa a dakinta."
"To shike nan Allah Ya tabbatar da alkairi."
***────────────────────────────
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ mai lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._**_•••©ᴀʙʙᴀɴ ᴀɪsʜᴀ_*
YOU ARE READING
TA ZAMA HAJA!
General FictionLabarin akan yadda aka mayar da aure tamkar hajar kasuwa a wannan zamani, wanda hakan ke haifar da tarin matsaloli.