*Ta Zama Haja! 11*
*Sadik Abubakar*
*Lafazi Writers*https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
Kimanin mako guda ke nan da kai Zaliha gidan Alhaji Saminu, har kawo yanzu ta ƙi sakin jiki, kullum cikin abu ɗaya take, watau kuka. Ya yi rarrashin har ya gaji. Sati ɗayan matansa suka ba shi ya ci amarci shi da amaryarsa, sai dai ga shi satin ya ƙare amarcin ya ƙi ciyuwa. Bayan cikar mako gudan ne ya fara fita ofis.
To tun ranar da ya tara su ya yi musu jan kunne, matan nasa ba su sake yin tozali da Zaliha ba, tana can sashenta komai Alhajin ne ke kai mata. Fitarsa ke da wuya, Hajiya Lami ta nufo ɓangaren Zalihar, kai tsaye ta shiga har cikin ɗaki. Iske ta ta yi tana kuka, sai mamaki ya kama ta, "To kukan me kike yi kuma? Ke da kika zo cin daula" A ranta ta yi wannan maganar kafin ta matsa kusa da ita. Zaliha ta ɗago kai ta dube ta tare da tsayar da kukan take yi, ganin ta kai sa'ar Umma sai ta yi tunanin ko za ta taushe ta, ta ɗan ƙarfafa mata gwiwa. Amma sai ta ji saɓanin haka, "Yo kukan me za ki yi kuma 'yar nan? Ba dukiya kika zaɓa ba? Don haka kuka ba ki fara komai ba tukunna, da ganin ki ba za ki rasa saurayi daidai aurenki ba, amma shi ne kika biye wa kwaɗayi da son abin duniya. Ke sai kin auri mai kuɗi ko? To za ki ci kuɗi kuma za ki ci takaicin da sai kin yi nadamar shigowa wannan gidan, da ke da dukkan kwaɗayayyun iyayen naki. Allah Ya ba ku samari waɗanda suke son ku amma kuna hange, to za ki ji kuma za ki gani, mu je zuwa." Tana gama maganar ta juya ta fice.
"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN!" Cikin wani sabon kukan Zaliha ta faɗi wannan addu'a sannan ta ɗora da faɗin, "Ya Allah ka tsare ni daga sharrin wannan gida, Allah ka san abin da ba mu sani ba, ka zama gatana kai kaɗai ne ka san ciwona, ina roƙon ka ka kawo mini waraka Ya Hayyu Ya Ƙayyum!"
Tana gama addu'ar sai ta ji kukan ya ɗauke mata tamkar an yi ruwa an ɗauke, haka nan sai ta ji zuciyarta ta ɗan kwarara.
Jim kaɗan da fitar Hajiya Lami, sai ga Hajiya Sabuwa nan ita ma ta shiga da faɗin, "Amarsu ta ango, amarya ba kya laifi koda kin taɓa ɗan samu gida. Har yau ba a gama cin amarcin ba ne, bare a fito a gaisa da 'yan gida? To mu ga mu muna zo da kanmu." Ta ɗan tsahirta da surutan nata, Zaliha ba ta ce mata uffan ba, illa kallon ta da ta yi kawai. Ita ɗin ma kusan sa'ar Umma ce, a ranta ta ce, "In Sha Allah duk kaidinku da makircinku kanku zai tsaya, ba na nufin kowa da mugun sharri duk wanda ya nufe ni da shi Allah ka mayar masa kansa. Walahaula Walaƙuwwata illa Billah!"
"Kin yi shiru ana magana kina jin mutane, ko haka aka faɗa miki idan kin zo kada ka yi wa waɗanda kika tarar magana? To ki saurare ni, idan kin ƙi magana, na tabbata ba za ki hana kunnenki jin abin da za a faɗa ba. Hajiya sabuwa ta zo yanzu ta fafa miki yadda zaman gidan nan yake ko? Cin wannan dukiya ba ya yi yuwa cikin sauƙi, idan har kika dage sai kin ci, to ki yi shirin cin ɓanganre biyu. Ki ci kuɗi kuma ki ci baƙar wahala idan ma ta zo miki da kyau ke nan, ko kuma ki ci tsagwaron wahalar."
Shiru Zaliha ta yi tana sauraren ta, a zuciyarta kuma tana cewa, "In Sha Allahu ba zan ga wahala ba, ke dai da kike ambaton ta ke za ki gan ta da yardar Allah!"
Ta juya za ta fita ke nan sai Zaliha ta yi gyaran murya ta ce, "Na ce ba!"
Da sauri Hajiya Sabuwa ta juyo cike da mamaki ta kalle ta, kamar ta yi magana sai kuma ta ji ta gaza.
Zaliha ta ci gaba da cewa, "Abin mamaki, ke da uwar ɗakin taki kun tako takanas ta Kano har nan kun faɗi maganganun da kuke buƙatar amsarsu, amma kun gaza haƙurin 'yan ɗakikun da zan ba ku amsa. Hakan ya nuna kuna shakkar abin da zai fito daga bakina ke nan, to Alhamdu Lillahi! Allah na gode maKa da wannan baiwa da ka yi mini. Ina so ki buɗe kunnuwanki ki saurari abin da zan faɗa miki sannan ki isar wa da ita shugabar taki."
Ta ɗan ja numfashi ta ɗora cewa, "Da ke da ita dukkanku kun haife ni, ba zan yi kishi da ku ba, ba kuma zan taɓa faɗa muku maganar rashin tarbiyya ba. Amma ku sani duk yadda kuka ma'amalance ni haka za a ma'amalanci 'ya'yan da kuka haifa a cikinku, na tabbatar duk kalaman da kuka zo kuna yi mini babu wacce za ta so 'yarta ta tsinci kanta a gidan mata masu irin halinku. Amma daɗin abin lamarin ba a hannunku yake ba, don haka abin da kuka shuka shi za ku girba. Sannan na ji duk kumfar bakin da kuke yi akan wannan ƙazantar ce da ba ku san ta wace hanya ya tara muku ita ba, to ku kuka damu da ita. Ni ba ta gabana, aurena da wannan mutumin umarnin mahaifiyata na bi. Da za ku yi mini alfarma ɗaya da kun sa Alhaji ya sake ni, kuma da kun cika mararsa son kishiya da ko auren ma ba za ku bari ya yi ba."
A fusace Hajiya Sabuwa ta ce, "Lallai yarinyar nan ba ki da mutumci, tunda haka kika ce, za ki ga makircinmu. Sai kin yi nadamar faɗa mini wannan maganganun."
"Ki gafarce baiwar Allah! Ni fa ban faɗa miki wani abu na zafi ba, abubuwan da ya kamata ki sani ne, domin tafiya ba tare da ka san halin abokin tafiyar ba da wahala. Sai a yi ta samun cikas da saɓani, amma yanzu aƙalla kin fara sanin ko ni wace ce? Don haka nan gaba idan kin ji na faɗi wata magana ko na yi wani abin ba za ki yi mamaki ba. Amma idan kalamaina sun yi miki ciwo to ina neman yafiyarki, ban yi don haka ba akasi aka samu."
Rasa abin cewa ta yi, ta juya laƙwas gwiwa a saluɓe. Wajen Hajiya Lami ta nufa tana hucin harbin iska, "Kin ga garin kwashe-kwashen Alhaji ya je ya kwaso mana 'yar jaraba, kin ji yadda ta zage ni tas da baƙaƙen maganganu? Gaskiya sai mun tashi tsaye akan wannan yarinyar, sai mun yi kamar muna yi kafin ma ta samu gindin zama. Idan ba haka ba kuwa za mu yi ƙarkon kifi."
Dariya Hajiya Lami ta yi sannan ta ce, "Ke do Allah ba na son wannan barkwancin naki, yarinyar da wataƙila tun zuwanta gidan nan take faman kuka, shi ne za ki ce ta zage ki. Ko iya haɗa ido da mutane ba ta yi."
"Cabɗijan! Lallai kam, amma dai kin san idan wasa nake za ki ga alamar dariya a tare da ni, idan ba ki yarda ba zo mu je ki ji da kunnenki."
Miƙewa ta yi suka sake komawa, daidai lokacin Zaliha ta fito da Ƙur'aninta za ta ɗan taɓa tilawa. "Lafiya dai? Ko akwai abin da kuka manta ba ku faɗa ba ne? Ta tambaye su bayan ta ɗaga kai ta dube su.
Hajiya Sabuwa ta dubi Hajiya Lami ta ce, "Kin ji abin da na faɗa miki ko?"
Kafin ta yi magana Zaliha ta kalle ta sosai, zuciyarta a dake babu jin fargaba ta ce, "Ba ki yarda da abin da ta faɗa miki ba ne? Saƙona ne zuwa gare ku gabafaya. Kamar yadda kuka amayar mini da abin da yake ranku wanda kuke so na sani, shi ne ni ma na furzar muku da nawa saƙon, kun ga an yi canjaras ke nan (Watau Balancing) a harshen 'Yan Jarida. Saboda haka idan babu damuwa ku ɗan fita zan yi karatu ne."
Wani irin mamaki ne ya ɗaure musu kai har suka rasa abin da za su ce, sai kallon juna suke, zuwa can Hajiya Lami ta nisa tare da cewa, "Ke 'yar nan ki yi ƙasa-ƙasa da muryarki, iyayenki ne a gabanki. Ki bi mu ki zauna lafiya a gidan nan, idan kin ƙi kuma kwaɓarki ta yi ruwa. Yanzu za mu yi sanadiyar yanka miki biza zuwa inda kika fito, kin ga kin ci ribar auren Alhaji, kin zama ƙaramar bazawara."
Wata 'yar gajerar dariya mai cusa takaici Zaliha ta yi sannan ta ce, "Iyayena fa kika ce? Anya kuwa kin san ma'anar wannan kalmar ta 'iyaye'? Da dai kishiyoyina kika ce da na fi yarda da ke, domin a zahiri ma matsayinku ke nan. Amma na yi alƙawarin ba zan taɓa yin kishi da ku ba kasancewar kun ajiye kama ta da wanda suka fi ni, kuma shekarunku kusan na mahaifiyata ne. Abu ɗaya nake son ku yi mini, ku yi sanadin fita ta daga gidan nan!"
"Kin yi da 'yan halak yariya, indai mu ne za ki ga tsiya tsirararta kuwa. Suna faɗa suka juya suka fice, ita kuma ta mayar da ƙofar ta rufe ta zauna ta fara karatunta. Karatu ta yi sosai wanda hakan ya sa ta ji kaso mafi yawa daga cikin damuwarta ya ragu. Ta samu nutsuwa a zuciyarta sosai, abu ɗaya ne dai ya tsaye mata a rai shi ne yaya Abdul, amma duk wani baƙin ciki da ɓacin rai yanzu ba ta jin sa.
Hajiya Lami da Hajiya Sabuwa suka yi turus babu nauyi, ɗan lokaci mai tsayi suka ɗauka ba wacce ta yi magana, zuwa can Hajiya Sabuwa ta ce, "To kin gani dai kuma kin ji da kunnenki. Yanzu mene ne abin yi? Ya kamata mu san matakin da za mu ɗauka tun kafin ya ɗauke ta su tafi Umara. Ba don ayyuka da suka yi masa yawa ba da yanzu ya fara shirin tafiyar."
Murmushin ƙeta Hajiya Lami ta yi sannan ta ce, "Don Allah ki kwantar da hankalinki, akan wannan 'yar ƙaramar yarinya duk kin bi kin tashi hankalinki. Wace ce ita? Wace uwarta a garin nan? Me suke da shi? Ina ta sani? Wa ta sani? Kada ki manta fa, boka na kan tsauni yana raye, kuma ya yi mana alƙawarin matuƙar yana numfashi babu wata buƙata da za mu kai masa kokenmu face ya samar mana mafita. Ki bar ni da ita kawai."
"To ai ni lamarin yarinyar ne har tsoro yake ba ni, zance a cikinta kamar an koya mata. Kuma da alama wannan ko wajen bokan aka je da wahala a yi nasara a kanta, domin na ga alamar mai riƙo da addini ce. Kin ga kuwa irin waɗannan ana shan wahala kafin magani ya huda su, wasu ma sai dai a yi ƙaiƙai koma kan masheƙiya."
"Ke kam kina da matsala wallahi, ana ba ki kina roƙo. Ita ɗin banza! Wai kin manta wace ce ni? Na buga da 'yar malamai ma na kai ta ƙasa bare ita, ko kin manta karanbattanmu da Madina 'yar Maiduguri? Yasin ta riƙa jefo mini, amma dayake bokan kan tsauni ya tsuma ni sai da na ga buzunta. Don haka yadda ta ce tana son barin gidan, to sai ta bar shi koda kuwa da izglanci ta faɗa."
Ita kuwa Suwaiba ba ta san wainar da ake toyawa ba, dayake sun haɗe mata kai su biyu suke sha'aninsu. Sannan kuma ita ɗin ba mai son hayaniya ba ce, tana can sashenta tana sabgar gabanta.
A ɓangaren yaya Abdul kawo yanzu a iya cewa ya ɗan samu kansa, ya miƙe. Sai dai har yanzu zuciyarsa fal take da ƙaunar Zaliha, yawan tunanin ta ne maƙare a ciki. Abin da ya sa Inna ta ci gaba da ƙoƙarin kauda masa da tunanin ta hanyar dawo masa da batun Aisha, har ta riƙa kiran yarinyar tana zuwa tana yi tare da Jamila, ko a haka Allah zai karkato da hankalinsa kanta. Domin abin da zai rage masa tunanin ko ma ya cire shi daga ransa shi shi ne ya samu wacce zuciyarsa za ta riƙa bege.
Aisha dai kyakkyawar yarinya ce mai nutsuwa ga kunya, fara ce sosai ba ta da jiki, Zaliha ta fita jiki da tsayi. A ɓaya ɓangaren layin su yaya Abdul ɗin take. Duk da wannan kyawawan siffofi nata, sam yaya Abdul ya ƙi sauraren ta, haka takan zo su yini da Jamila. Wani lokacin yakan yi mata magana amma ba ta soyayya ba. Soyayya gamon jini, wannan batu haka yake.
***────────────────────────────
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ mai lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._**_•••©ᴀʙʙᴀɴ ᴀɪsʜᴀ_*
YOU ARE READING
TA ZAMA HAJA!
General FictionLabarin akan yadda aka mayar da aure tamkar hajar kasuwa a wannan zamani, wanda hakan ke haifar da tarin matsaloli.