*Ta Zama Haja! 12*
*Sadik Abubakar*
*Lafazi Writers*https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
Ranar da Zaliha ta cika kwana goma cif a gidan Alhaji Saminu, suka gana Suwaiba. Har ɓangaren Zalihar ta tako da sallama, ta amsa masa da sakin fuska. "Amare manya, ko leƙowa ba a yi a ɗan gaisa." Cikin sanyin murya ta yi maganar.
Murmushi Zaliha ta yi ta sunkuyar da kai ba ta ce komai ba, Suwaiba ta ci gaba da cewa, "Tun washegarin tarewa ba a sake ganin ki ba, ba kya fitowa. Kodayake gidan haka yake bahagon gida ne, gara ma mutum ya yi zamansa shi kaɗai ya fi masa alkairi. Idan ya fito sai a nemi ɓata masa rai da gangan."
"Ai kam dai haka abin yake, rayuwa sai haƙuri." Zaliha ta faɗa cikin murmushi a takaice.
Suwaiba ta yi shiru tana ƙare wa Zaliha kallo sannan ta ce, "Ƙanwata zan ɗan ba ki shawarwari duk da cewa na san abin da aka faɗa miki a gida ya wadatar yadda za ki zauna lafiya maigidanki da kuma abokan zamanki. Amma duk da haka game da wannan gidan sai kin kiyaye wasu abubuwa."
Ta ɗan tsagaita, Zaliha ta baza kunnuwa tana jiran ta ji da me ita kuma ta zo?
Ta nisa ta ce, "Ni ce matar Alhaji ta uku, yaranmu biyu da shi, duk tsawon lokacin da na shafe da shi bai fi sati ɗaya ba ne na yi zaman farinciki ni da shi. Tun daga nan kuwa komai na yi ba birge shi nake ba, ba ya taɓa yaba mini. Kuma duk lokacin da wani abu ya faru ya je kunnuensa to ni ce laifi, koda kuwa ina da gaskiya. Na yi kuka har na gaji na saba. Waɗancan guzumayen matan su ne matsalar gidan nan, sun riga sun ɗaure shi tamajau. Bai isa ya zartar da wani abin ba sai da saninsu, su suke tafiyar da ragamar gidan nan. Yarana ba su da sukuni kamar agololi haka suke a gidan nan. Saboda haka ina son kada ki tanka musu, ki roƙi Allah Ya yi miki tsari daga makircinsu."
Zaliha ta tattara dukkan yanayin tausayi a fuskarta ta ce, "Allah Sarki! Sannu da zaman Ibada. Gaskiya na tausaya miki sosai, wannan zaman akwai zalinci, amma Ubangiji zai yi sakayya babu shakka! Su ɗin da suke ganin kamar sun gagara, ƙarya suke, su ƙananan alhaki ne su guji ƙarshensu ba zai yi kyau ba. Ni ƙaddara ce da biyayyar mahaifiyata ta kawo ni hannun Alhaji, amma ko kaɗan shi ko dukiyarsa ba sa gabana. Kuma har yau ban ji alamar zaman gidan nan ya kama ni ba. Ina sa ran zan fita ba da jimawa ba. Na yi wa uwata biyayya ne a matsayina na budurwa ta aurar da ni ga zaɓinta, amma idan na fita daga nan zaɓin kaina ne zan bi."
"SubhanAllah! Ban gane kin kusa fita ba? Saki kike nufi?"
Cikin murmushin takaici ta ce, "Labarina dogo ne, a dunƙule dai mahaifiyata ce ta ruɗu da dukiyar Alhaji har ta raba ni da wanda ya fi kowa sanin darajata. To amma fa a zahiri ne ta raba ni da shi, kullum neman wayarsa nake, shi ne namijin da zan iya rayuwa da shi a duk faɗin duniyar nan."
"To Allah Ya rufa asiri, gaskiya ke ma na tausaya miki. Wani lokacin iyaye mata suna yin ba daidai ba, ba su cika duba abin da kan je ya dawo ba. Sai kuma abin ya rikice su fi kowa shiga matsala."
Sun jima sosai suna tattaunawa.
To kamar yadda Hajiya Lami da Hajiya Sabuwa suka nuna dogaronsu ga boka, kici-kicin yadda za su bullo wa Zalihar suka shiga. Abin ma har mamaki ya riƙa ba su, yadda ta riƙa zaƙalkala tana nuna ita barin gidan take da muradi. Kodayake Hajiya Sabuwa ce take mamakin hakan, amma ita Hajiya Lami gani take kamar galatsi ne da iyashege, don haka ta sha alwashin za ta bi duk hanyar da za ta bi don ganin ta tsige ta daga gidan.
Bayan kwanaki uku da yin musayar yawun nan ne suka shirya su biyun suka tafi wajen ubangidan nasu, suka kwashe zance suka faɗa masa. 'Ya yi 'yan tsibbace-tsibbacensa sannan ya tambaye su, "Me kuke so a yi mata?"
Hajiya Lami ta ce, "Boka da bakinta ta ce tana son barin gidan, ba son sa take ba, shi ne yake son ta. Don haka a saka masa ƙin ta sosai, ya ji ba ya son ganin ta bare ya yi tunanin akwai aure a tsakaninsu."
Boka ya jinjina kai sannan ya kawo wani garin magani baƙiƙƙirin ya ce, "Wannan a zuba a hanyar da aka san za ta bi ta ƙetara, idan an yi haka zance ya ƙare, a ranar idan ya dawo ba za ta sake kwana a gidan ba."
Cike da murna suka karɓa, suka ba da ladan bokanci tare da yin godiya suka miƙe. A hanya suke tattauna yadda za su barbaɗa maganin. Shin a ina za su barbaɗa mata?
Hajiya Lami ta dubi Hajiya Sabuwa ta ce, "Ke za ki yi wannan aikin, ni na gama nawa. Sai ki kula sosai kin ji dai abin ya ce, idan aka samu matsala to abin kanki zai juyo, saboda haka ki lura sosai idan za ki zuba kada ki ƙetara."
Wani nishi mai nauyi ta saki sannan ta ce, "Wallahi har gabana ya faɗi, anya kuwa zan iya?"
"Ban gane za ki iya ba? Wace irin magana ce wannan? Kin ga ni fa duk wannan abin da kika ga ina yi taimaka miki nake, ke sanin kanki ne Alhaji ko babu boka zan sa shi ya yi ko kuma ya bari. Na ga tamu ta zo ɗaya ke ne shi ya sa ma har nake sauraren ki, idan kuma kina son na bar ki da waɗannan yaran to shike nan, kin ga dai wannan 'yar bana-bakwai ɗin da ya kwaso muku."
A sanyaye ta ce, "To shike nan babu komai."
"Yawwa ko ke fa, ai ba a bori da sanyin jiki. Kin ga yau ba a wajenta yake ba, da Magariba za ki lallaɓa ki shiga sashen nata ki barbaɗa mata shi sosai yadda dole sai ta ƙetara muddin za ta fito."
Haka suka ajiye magana, har suka iso gida hankalin Hajiya Sabuwa bai kwanta da wannan aikin kasassaɓar da za ta yi ba, alatilas ta amsa wa Hajiya Lami don ba ta son yin jayayya da ita.
Bayan Magariba kaɗan Zaliha ta gama ɗan girkinta iya cikinta ta ci, tana zaune tana jiran lokacin sallar Isha ya yi ta sauke farali sannan ta kwanta, sai ta tuna ba ta kulle ƙofar shigowa ɓangaren nata ba. Miƙewa ta yi ta nufo wajen da nufin ta rufe ƙofar, me idanunta za su yi tozali da shi in ba Hajiya Sabuwa ba, tana tafiyar sanɗa hannunta riƙe da baƙar leda tana yaryaɗa magani.
"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN!" Zaliha ta faɗa da dukkan ƙarfinta, hakan ya yi matuƙar razana Hajiya Sabuwa, garin neman hanyar gudu ta ƙetara maganin nan ta yi can ciki wajen Zalihar.
Da sauri Zaliha ta riƙa furta addu'ar, "A'uzu bikalimatullahi tammati min sharrin ma kalaƙa! Ta Allah ba taku ba, wallahi ba ku isa ku cutar da ni ba!"
"Don Allah 'yata ki yi haƙuri ki rufa mini asiri, wallahi sharrin shaiɗan ki yafe mini."
"Wace ce 'yarki? Wallahi ni ba 'yarki ba ce, ke ba uwata ba ce. Kushiyata ce mai shirin cutar da ni."
Suna tsaka da haka sai ga Alhaji ya shigo, gaban Hajiya Sabuwa ya yanke ya faɗi ta kama rawar jikin razana.
"Tunda sauran girmanka da ƙimarka a idona ka sawwaƙe mini zama da kai, wallahi ban dace da zaman gidan nan ba. Indai ba cutar da ni kake so ka yi ba, to ka yi haƙuri kafin matanka su haukata ni ko su hallaka ni." Zaliha ce ta yi wannan maganar cikin rarraunar murya.
"Wai mene ne yake faruwa?"
"Ita za ka tambaya, ga shi nan kana gani magani take zuba a ƙofa."
A fusace ya juyo kan Hajiya Sabuwa kafin ya yi magana ta fara faɗin, "Alhaji don Allah ka yi haƙuri wallahi ba laifina ba ne, laifin Hajiya Lami ne ita ce ta sani."
"Yi mini shiru munafukar banza! Kamar ke za ki ce wata ta saki ki aikata mugum abu. Ina take ita Lamin?" Daga nan ɗin ya ƙwalla mata kira da ƙarfi har sau biyu.
Ashe tunda ta ji shiru Hajiya sabuwa ba ta dawo kawo mata rahoto ba, ta yi tunanin kodai ba ta je ba ne? Don haka sai ta fito daidai lokacin ne ta hangi Alhajin ya shiga wajen Zalihar. Laɓewa ta yi, saboda haka ta ji duk abin da ya faru kuma ta ji kiran da ya yi mata. Komawa baya ta yi kaɗan, shi kuma ya sake ƙwalla mata wani kiran da ya fi na farko ƙara. Sai ta amsa sannan ta ƙarasa da faɗin, "Alhaji lafiya kuwa kake ta kwaɗa uban kira haka? Maganar take ba tare da ta yarda sun haɗa ido da Hajiya Sabuwa ba,
Alhaji huci yake tamkar wani bijimin sa, yana fesar da wata zazzafar iska ya ce, "Wannan makirar ce take shirya wa wannan 'yar baiwar Allahn wani mugun abin, Allah Ya toni asirinta. Amma bari ki ji daga bakinta."
Ya juya ya dube ta ya ce, "Wa kika ce ta sa ki?"
Cikin kukan nadama ta dubi Hajiya Lami ta ce, "Ba ke ba ce tun washegarin kwananta na bakwai kika ce sai mun tashi tsaye a kanta, shi ne muka je wajen boka muka karɓo wannan maganin kuma kika ce ni zan zo na zuba mata."
Dariyar ƙeta da kisisina Hajiya Lami ta yi sannan ta ce, "Ƙarya kasa ɗan duba ya gano ranar mutuwarsa. Ni da girmana na rasa wacce zan yi wa wannan ƙetar sai yarinyar da na ɗauke ta tamkar 'yata!" Ta ɗan tsagaita da maganar ta matsa kusa da Zaliha ta rungume ta sannan ta ci gaba da cewa, "Ai ni wannan yarinya tamkar ni na haife ta a cikina haka nake jin ta, yaushe ne ma na shigo na ga tana kuka, rarrashin ta na yi da nasihohi. Ina nuna mata ai nan ba gidan kishi ta shigo ba, ta kwantar da hankalinta matuƙar ina gidan nan ba zan taɓa bari a musguna mata ba. Saboda haka ni ban san komai ba Alhaji."
Ya nisa ya ce, "Ni na san da haka ai, marar son zaman lafiya da ma ita ce."
Ya ɗan numfasa sannan ya sake mayar da akalar maganar kan Hajiya Sabuwa ya ce, "To ki saurare ni da kyau, kafin ki cutar da 'yar mutane zan yi wa tufkar hanci. Ki je na sake ki saki ɗaya."
Ihu haɗe da kuka ta saki, cikin sautin kukan ta riƙa cewa, "Hajiya Lami Allah Ya isa tsakanina da ke macuciya azzaluma, duk ke ce kika sani aikata wannan abin. Kuma wallahi ka yi bincike a kanta duk abin da take faɗa ƙarya ne, ko Madina ma ita ce ta fitar da ita daga gidan nan. Wannan ɗin ma kuma za ka gani."
Cikin dariyar makirci Hajiya Lami ta ce, "A'a Alhaji bai kamata ka yanke hukunci cikin fishi ba, jan kunne ya kamata ka fara yi mata, idan har ba ta bari ba, so sai a ɗauki wannan matakin."
"Ai wannan ɗin ma jan kunne ne, kanta rawa yake, gara ta je can gida ta yi musu rawar kan ni na gaji.''
"Haƙuri za a yi Alhaji, a bar ta ta ci albarkacin 'ya'ya. Da girmanta bai kamata ta koma gida da sunan zawarcin saki ba. Ina roƙon ka don Allah ka janye wannan sakin, idan mai ji ce wannan sai ya zame mata izna nan gaba."
Alhaji ya ja numfashi sannan ya ce, "To wallahi don kin sa baki ne zan ƙyale ta amma da zamanta ya ƙare a gidan nan, ba na son sakarcin banza."
"A dai yi haƙurin Alhaji, mai haƙuri ke da nasara, na gode sosai Allah Ya ƙara girma. Mu bari mu koma. Sai ki taso mu tafi ai."
Alhaji ya dakawa Hajiya Sabuwa tsawa da cewa, "Ki tashi ki ɓace mini da gani. Miƙewar ta yi ta bar wajen salalo-salalo.
Zaliha ta koma cikin ɗakinta tana kuka, bin ta ciki ya yi domin ya rarrashe ta. "Wallahi sai na tafi gidanmu, ni ba zan zauna a nan ba a haukata ni ko a saka mini wani ciwon da zai fi ƙarfin iyayena. Ka ƙyale ni na tafi kawai!"
Rarrashin dai ya ci gaba da yi tare da alƙawarin cewa zai ɗauki tsattsauran mataki akan lamarin, idan akwai yi yuwar ya sauya mata gida ma to zai ware ta daga cikinsu. Nan dai ya samu ta daina kukan sannan ya koma can sashen da yake, watau ɓangaren Suwaiba. Ita duk wannan hayaniya da ake ba ta sani ba, illa dai ta ji kiran da Alhajin ya kwaɗa wa uwargidan. Ba ta cika shiga sabgar da ba a kasa da ita ba.
Yau dai Hajiya Sabuwa ta ga tsantsar makircin Hajiya Lami, ta haɗa mata gadar zare ta rufta da ita. Ranta a ɓace yake, saulin abin ma duk yaran gidan ba sa nan, suna can bikin murnar zagayowar ranar haihuwa ta 'yar maƙwabtansu. Waje ta nema ta zauna tana tunanin yadda za ta rama wannan kunyatarwar da uwargidan ta yi mata, ta lashi takobin ba za ta bari abin ya wuce haka nan ba, sai ta ɗauki fansa ko ta halin ƙaƙa. Yadda ta sa ta ji kunya ta zubar da hawaye, to lallai ita ma sai ta ga faruwar hakan a kanta. Gabaɗaya daren nan gaza barci ta yi, tsananin baƙin ciki da takaici ne suka hana ta sakat!
To ita ma Zaliha kusan hakan ce ta kasance da ita, ba ta yi wani barcin arziki ba. Gari na wayewa ta kira Umma, lokacin kuwa Abba bai kai ga fita ba. Mamaki ne ya kama Umma na ganin kiran, domin tunda aka kai ta wannan ne kiran farko da ta yo mata, "Allah dai Ya sa lafiya." Ta faɗa a ranta kafin ta ɗaga wayar.
"Ina kwana Umma?" Zaliha ta faɗa cikin rarraunar murya.
"Wa alaikums salam." Umma ta amsa.
Bayan sun gama gaisawar, sai ta gaza yin ƙorafin da ke ranta, "Ina Abba, ko ya fita ne?"
"A'a, bai fita ba tukunna, bari a ba shi."
Miƙa masa wayar ta yi, ya kara a kunne tare da cewa, "Assalama Alaikum!"
Wani irin sanyi Zaliha ta ji ya ratsa mata zuciya, ta amsa, "Wa alaikums salam! Abba ina kwana?"
"Lafiya ƙalau Zaliha, ya kwanan gidan?"
"Alhamdulillah Abba! Ya ya aiki?"
"Aiki mun gode Allah!"
Shiru ta yi Abba ci gaba da tambayar, "Lafiya dai babu wata matsala ko?"
Kamar ta faɗa masa abin da ke ranta, amma sai ta ji shi ma ba za a ta iya faɗa masa ba, "Ba komai Abba."
"To madalla! Allah Ya yi miki albarka."
"Amin Abba!"
Ya miƙa wa Umma wayar, ta karɓa da cewa babu wata damuwa ko?"
"E." Ta amsa a gajarce cike da jin haushinta.
"To shike nan nan ki gai da maigidan. Sai an kwana biyu zan zo ai."
Zaliha ba ta yi wani farinciki da albishir ɗin zuwan ba, domin ta san zuwan ba na komai ba ne face don ta ƙara wa jakarta nauyi. "Koda ma a ce na faɗa mata matsalar ba fahimta za ta yi ba, ƙarshe ta zama kamar waɗannan mararsa imanin, ta ce bari ita ma ta je wajen bokan ta karɓo mini maganin tsarin jiki." A ranta ta yi wannan maganar. Ta ci gaba da saƙe-saƙenta, zuwa can sai ta yanke shawarar kiran wata ƙanwar Umman ana kiran ta Anty Maryam. Ita ce 'yar auta a ɗakinsu.
Cikin sa'a bugu ɗaya ta shiga, ta ɗaga da sallama, "Assalama Alaikum! Amare manyan gari."
Cikin murmushin jin kunya ta ce, "Anty ina kwana?"
"Lafiya ƙalau, ya kike ya gidan?"
"Lafiya ƙalau!"
"To Ma Sha Allah! Ya ya abokan zaman naki? Da fatan dai babu matsala ko?"
Ƙwalla ta ciko maƙil a idonta, dandanan muryarta ta sauya zuwa yanayin kuka, ta ƙwarara ta da kyar ta ce, "Anty don Allah ki tambayi Abban Ilham, gobe ki zo."
"Akwai damuwa ke nan, me ke faruwa? Ke da shi ne ko kuwa?"
Kukan da take tattalin kada ya bayyana ya kufce mata, cikin kukan ta ce, "Anty kawai ki zo don Allah ke kaɗai ce za ki fahimce ni..." Kukan ya ci ƙarfinta alatilas ta yi shiru.
Hankalin Anty Maryam ya tashi matuƙa, cikin ƙarfafa muryar gwiwa ta ce, "Daina kukan kin ji, In Sha Allah zan zo. Yanzu ma abin da ya sa aikin kwana ya yi har yanzu bai dawo ba, amma ina tafe goben ki kwantar da hankalinki kuma ki ci gaba da addu'a."
Rarrashin ta ta yi sosai kafin ta kashe wayar. Hakan ya ɗan sanyaya mata zuciya, ba shakka tana da yakinin Anty Maryam ɗin za ta taimaka mata fiye da Umma.────────────────────────────
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ mai lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._**_•••©ᴀʙʙᴀɴ ᴀɪsʜᴀ_*
YOU ARE READING
TA ZAMA HAJA!
General FictionLabarin akan yadda aka mayar da aure tamkar hajar kasuwa a wannan zamani, wanda hakan ke haifar da tarin matsaloli.