*Ta Zama Haja! 06*
*Sadik Abubakar*
*Lafazi Writers*https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
Tana isa gida kai tsaye banɗaki ta nufa ta wanke fuskarta don ta ɗan rage jan da idonta ya yi sannan ta wuce ɗakinta. Sauya kayan makarantar ta yi da na zaman gida. Umma na can cikin ɗaki, zuwa ta yi ta gaishe ta tare da sanar da ita cewa ta dawa, kana ta komo ta zauna. Tunani kuma ya ce ga shi nan, ta yi zugum da ita abin tausayi. Ta nitsatsa cikin duniyar tunane-tunane kala-kala. "Shin me zan faɗa wa yaya Abdul ya gamsu da ni? Wane bayani zan yi masa? Duk abin da zan faɗa masa da wahala ya fahimce ni. Wane irin kallo Innarsa za ta yi wa magabatana? Da wane zan kalli Jamila? Shin wane hali ma zai shiga? Na fi jin tausayin sa fiye da kaina, domin son da yake mini ya fi wanda nake masa. Ya Allah! Kai ne mai hukunta dukkan al'amura."
"Zaliha!" Muryar Umma ke nan wacce ta fito daga ɗaki har ta iso falo Zalihar ba ta sani ba, sakamakon ta yi nisa a cikin tunanin da take, kiran ne ya katse mata tunanin. A ɗan firgice ta zabura.
Cike da mamaki Umma ta ce, "Na lura so kike ki ɗora wa kanki wata larurar ko? Akan wannan abin da rayuwarki nake son gyara miki. Dubi yadda kika fara yin zuru-zuru da ke sakamakon tunani da rashin cin wadataccen abinci. Ki tashi ki je ki ɗauko abincin ki zo ki ci a gabana, na lura idan ba na matsa miki sai ki lahanta kanki da yunwa."
Miƙewar ta yi ta ɗauko abincin ta dawo ta ajiye. Umma ta ci gaba da fadin, "Abin da nake tsara miki Zaliha ba wai don na cutar da ke ba ne, uwa ba ta taɓa cutar da 'yarta. Ni burina ki yi rayuwa cikin wadata da jin daɗi. Shi wannan mutumin da nake miki kwadayin ki aura babban mutum ne mai arziki, komai a cikin wadata za ki same shi, ba ke kaɗai ba hatta mu ma sai mun ci arzikinsa domin mai alheri ne. Ki duba kuɗaɗen da ya ba ki tun a zuwansa na farko amma kika ƙi karɓa, shi ne wanda ya dace da darajarki da ƙamarki ba Abdullahi ba, ke ba tsararsa ba ce, ba shi da kuɗin da zai iya auren ki."
Tsananin ƙunar rai da takaici ne ke kama Zaliha idan ta ji mahaifiyar tata na faɗin irin waɗannan kalamai wanda ba su da maraba da na wanda ba shi da ilimi. "Shin wai arziki da talauci duk ba na Allah ba ne? Yakan azurta wanda Ya so, Ya kuma talauta duk wanda Ya so babu mai tuhumarSa. Shin wai yaushe 'ya'ya mata suka zama haja ne? Allah Ya ganar da dukkan iyaye masu hali iri na Umma!"
Abin da Zaliha ta riƙa faɗa cikin zuciyarta ke nan lokacin da ta yi shiru. Uwar ta ci gaba da cewa, "Ki saki ranki ki kwantar da hankalinki ki ci arziki, na tabbata alherin da za ki samu a wajensa ba ƙarami ba ne, ko matansa ba su samu ba. Domin yana son ki kuma ke ce ƙarama a cikinsu, don haka zai kula da ke fiye da tsammaninki."
Zaliha ta nisa tare da sauke numfashi sannan ta ce, "Shike nan Umma ba komai na fahimce ki."
"Yawwa ko ke fa, maza ki ci abincin kada ya yi sanyi, ni bari na tashi na yi salla."
To bayan sallar Isha misalin ƙarfe takwas da rabi, 8:30pm yaya Abdul ya iso kamar yadda ya alkawarta mata. Wayarta ya kira ya sanar da ita kamar yadda ta buƙata, tana ganin kiran gabanta ya faɗi. Duk kuwa da cewa da ma abin da take jira ne. Karon farko ke nan da gabanta ya yanke ya faɗi sanadiyar ganin kiran wanda a da idan ya kira ta cikin nishaɗi da annuri take ɗaga wayar. Duniya mai juyi, wai da kwaɗo ya ji shi a ruwan zafi.
Ɗaga wayar ta yi tare da karawa a kunnenta ta ce, "Sannu da zuwa, bari na fito."
"Ba damuwa!" Ya faɗa cikin yanayi marar walwala.
Hijabinta ta saka ta nufi wajen Umma ta ce, "Zan ɗan fita waje."
"Waye ya zo?" Umma ta tambaya.
"Yaya Abdul ne!" Ta faɗa cikin tararrabin kila ma ta hana ta fitar ko kuma ta balbale ta da faɗa.
"Shike nan zan bar ki ki fita amma kada ki jima, na yi miki wannan alfarmar ne don ki san yadda za ki yakice shi a hankali. Na san ba za ki iya cire shi a ranki lokaci guda ba, sannan daga yau ma ba sai ya sake shigowa ba, ya tsaya can wajen har ya gaji ya ƙyale ki. Idan kuma kika daɗe a wajensa ni na san abin da zan yi miki."
Zaliha ba ta sake cewa komai ba ta fito kofar gidan. Da sallama ta isa wajen da yake tsaye, ta gaishe shi ya amsa mata. Yanayin nasu sam ba daɗi, tamkar a mafarki suke ganin abin. Su da suka saba yin hira cikin farinciki da amince a sirrance cikin gida, amma yau su ne a waje cike da damuwa? Wannan wane irin sauyin lamari ne?
Tun bayan gaisuwar sai da suka shafe kimanin mintuna biyar zuwa bakwai suna tsaye ba wanda ya sake furta koda kalma ɗaya ne. Shi ne ya katse shirun bayan ya nisa ya ce, "Shi waye mutumin kuma a ina ya gan ki?"
"Watarana ne na je babban kantin bakin titi, shi ma ya tsaya zai yi sayayya, ya yi mini magana amma ban kula shi ba. Ashe ya biyo ni a baya har gida." Cak! Sai ta tsaya da maganar.
Ya ce, "To sai aka yi ya ya kuma?"
"Shi ne Umma ta ce idan ban saurare shi ba, ba ita ba ni!"
Murmushin takaici ya yi sannan ya ce, "Ki fito kawai ki ce mini kina son shi, kada ki jingina wa Umma komai. Wannan ba wani abu ba ne, kuma na gode wa Allah da Ya nuna mini haƙiƙanin halinki tun yanzu. Ki je ki aure shi ina miki fatan alkairi."
Kuka na gaske irin mai saka zazzafan ciwon kai ne ya suɓuce mata, sunkuyawa ta yi ta dafa ƙafafuwansa zuciyarta na tsananin tafasa da jin waɗannan kalamai nasa. Ashe da ma zai iya hakura da ita? Ita da take alƙawarta wa zuciyarta cewa koda ba ta auri wanda ba shi ba, ba za ta taɓa mantawa da ƙaunar da yake mata ba. Ta yi alƙawarin ta bar masa birnin zuciyarta har abada shi ne sarki, amma ashe shi ba haka abin yake a wajensa ba? Shi ɗin da take ganin za ta samu sauƙin raɗaɗin da take ji, wanda a tunaninta shi ne kaɗai ne magani da salama amma sai ya ɓige da ƙara harziƙa ta.
Cikin kukan ta ce, "Yaya Abdul..." Ya katse ta da cewa, "Babu wata magana da za ki sake faɗa mini, ki sakar mini ƙafa na tafi."
Ƙara sautin kukan ta yi ta ce, "Don Allah ka tsaya ka saurare ni, yaya Abdul yanzu ashe ba ka fahimce ni ba duk zaman da ka yi da ni? Ka tuna fa tun ban san kaina ba kake reno na, idan har akwai wanda zai faɗi haƙiƙanin halin mutum to babu shakka malaminsa ne. Yaya Abdul ban yi tunanin ko a mafarki za ka iya furta waɗancan kalamai a kaina ba. Amma babu komai, ba na so ka sake yarda da ni ɗin. Ina so ka sani na rantse da Ubangijin da numfashina ke hannunSa ina son ka, wannan soyayyar taka a raina ba za ta fita ba sannan ba ban zan taɓa roƙon Allah Ya cire mini ita ba, sai dai na roƙe Shi da Ya ƙara mini koda za ta zama ajalina."
Zantukan nata sun daki zuciyarsa matuƙa, bai taɓa yin shakku akan son sa a zuciyarta ba, amma abin da yake masa tuƙuƙi a rai shi ne, ta ya ya lokaci guda ta zo masa da wannan batu ba tare da an kai ruwa rana da ita ba? Ya kamata aƙalla ko za ta ba da kai bori ya hau, to a ɗan tayar da ƙura mana.
Kuka kawai take kashirɓan, shi ma kukan yake amma na zuci, fuskar nan murtik babu annuri.
Umma na ta jira ta ga Zaliha ta dawo amma shiru, miƙewa ta yi ta leƙo domin gane wa idonta. Karaf sai ta yi tozali da da Zaliha durƙushe tana kuka, "Zaliha mene ne haka? Me ya faru?"
Gabɗayansu suka firgita da jin muryar da ba su yi zato ba. Da sauri ya matsa kusa da ƙofar ya durƙusa tare da cewa, "Sannu Umma ina yini?"
Maimakon ta amsa masa gaisuwar sai ta zarce da faɗin, "Abin da nake so da kai, ka saurare ni da kyau. Zaliha an yi mata miji, don haka ka fita sha'aninta na ɓangaren soyayya. Yanzu ka kalle ta a matsayin ɗalibarka kamar sauran 'yammatan. Da ma na ƙyale ka ne kawai ka kula ta na wucin-gadi, amma Zaliha ba sa'ar aurenka ba ce kana a wannan matsayin. Idan har auren kake so da gaske ga 'yammata nan daidai kai, ko kuma ka koma can cikin dangi a ƙauye ka zaɓo. Saboda haka idan ita tana jin nauyin faɗa maka, to ni na isar maka yanzu sannan na yi maka togaciya da zuwa ƙofar gidan nan da sunan zance."
Cikin risinawa da girmamawa ya ce, ''To shike nan Umma ba komai, na gode Allah Ya saka da alkairi sai anjima."Ya faɗa tare da miƙewa ya bar ƙofar gidan.
Zaman dirshan Zaliha ta yi ta ci gaba da kuka da dukkan ƙarfinta, "Za ki taso ki shigo ko kuwa sai na fizgo ki?" Umma ta faɗa fusace.
Tamkar da gini take maganar, ko gizau ba ta yi. Babu shakka a yanzu tana jin matuƙar haushin uwar tata, duk da taka-tsantsan ɗin da take na gujewa saɓa mata amma ya zama tilas a wannan karon ta nuna mata ɓacin ranta. Don me za ta aikata wannan abin kunyar na zubar wa kai girma da martaba, duk irin girmamawa da biyayyar da yake mata amma ta rufe ido akan kuɗi?
"Ba za ki taso ba ko? To ki zauna a nan ko kuma ki bi shi ku tafi na bar masa ke tunda ban isa da ke ba!"
Ƙememe Zaliha ta kafe ta ƙi motsawa daga wajen, ci gaba da kukanta kawai ta yi. Ta jima tana kuka sannan ta yi shiru. Tana nan zaune, zuciyarta ta fara ba ta wasu shawarwari, "Ki tashi ki bi shi ɗin kawai tunda dai shi ne masoyinki na asali, shi kike so. Idan Abbanki ya dawo ta san me za ta faɗa masa, tunda ta ƙi ta fahimci abin da take so ba lallai ba ne ya zama alkairi ba, amma ta kafe a kai."
Wata zuciyar kuma ce mata ta yi, "Kada ki bi shi, ki tashi ki shiga gidan, amma ki taurare mata akan wanda kike so. Domin ke za ki zauna da shi ba ita ba. Kuma ƙila ita ɗin ba auren dole aka yi mata ba amma ga shi ke za ta tilasata miki, sam kada ki yarda."
Zuciya ta uku kuwa cewa ta yi, "Kada ki tashi ki ci gaba da zama har Abbanki ya dawo ya same ki a nan, zai tambaye ki me ya faru sai ki warware masa zare da abawa. Domin mafi yawan abubuwan da suke faruwa ba sani yake ba, idan har tana taƙamar ita ta haife ki, to shi kuma mahaifinki ne. Da ita da ke duk a ƙarƙashin ikonsa kuke, da kai da kaya duk mallakar wuya ne. Shi zai san yadda zai bɓullo wa lamarin, ki yi haƙuri kowa da yadda jarabawarsa take zuwa daga wajen Ubangiji."
Wannan shawarar ta ƙarshe ita ta fi kwanta mata a rai, domin babu shakka lamarin Umma ya fi ƙarfinta. Duk yadda ta so na ƙin kai ƙarar ta abin ya ci tura, tilas ne ta sanar da Abban nata. Tana zaune sai ga hasken fitilar mashin nan ya karyo kwanar layin. Wani sanyi ta ji ya dira a tsakiyar zuciyarta. Yana ƙarasowa daf da gidan ta miƙe da dukkan kuzarinta ta buɗe masa ƙofar ya shige. Mamaki ne ya kama shi na ganin ta a wajen da wannan dare. "To ko me ya fito da ita?" A ransa ya yi wannan tambayar.
Ta bi bayansa yana tsayawa ya saukko da tambayar, "Lafiya dai Zaliha me kika fito yi yanzu?"
Rungume shi ta tana sakin ajiyar zuciya wata na korar wata, ta gaza magana.
"Ina Umman taki ne?" Kuka sosai ta fara tana rungume da shi. Dayake ya san ta da shagwaɓa, rarrashin ta ya riƙa yi ya kamo hannunta suka shigo ciki.
Umma na zaune bisa kujera ta dube ta ta ce, "Au ashe ba ki cika mai zuciya ba, ai na yi zaton kin bar gidan ke nan!"
"Wai me ke faruwa ne Saratu?
"Akan dai Abdullahi ne, ya zo ya yi kiran ta ƙofar gida sai ƙarya da gaskiya yake shirya mata, ga wanda yake son ta da aure ta ƙi sauraren sa. Shi ne na je na faɗa masa ya rabu da ita tunda ta samu miji, to don me zan hana shi ɓata mata lokaci shi ne ta ja tunga a ƙofar gida take kuka."
Cikin ɓacin rai Abba ya ce, "Saratu ba kya kyautawa, sam wannan ba huruminki ba ne raba su. Ba ki san lokacin da Allah Ya haɗa su ba, ina gudun sauyawar al'amari fa! Yadda kike nuna wa yaron nan ƙiyayya komai zai iya faruwa, daga ƙarshe kuma ki zo kina jin kunya."
"Allah ma ya tsare ni da wannan baƙar ƙaddarar da zan ji kunyar sa, duk abin da zai sa na ji kunyar sa ba na fatan Allah Ya kawo mini shi."
"To wannan kuma burinki ne, amma ki sani iyakacin abin da za ki iya yi ke nan, tabbatuwar abin ko akasin haka wannan ikon Ubangiji ne. Idan ya yi nufin Zaliha matarsa ce babu yadda za ki yi, kina ji kina gani kuma a gabanki da hannunki za ki wanke ta ki kai ta gidansa. Don haka idan za ki yi sara ki riƙa duba bakin gatarin ko don watan-watarana."
Ya ɗan numfasa kaɗan sannan ya juya ya dubi Zaliha, ransa ya ƙara ɓaci ganin yadda 'yarsa ɗaya tilo ta lalace ta rame. Nisawa ya yi sannan ya ci gaba da faɗin, "Yanzu duba ki ga yadda ta faɗa saboda tunani da tsangwama. Shin wai ba ki san cewa su 'ya'ya amana ce ba kuma kiwo ne Allah Ya ba mu ba? Sannan sai ya tambaye mu yadda muka kiwace su, ya yi hisabi?"
A fusace ta ce, "Cutar ta nake yi ko? Watau kana nuna mata cutar da ita zan yi Allah zai saka mata ko? Tun ba yau ba na sani kana ƙoƙarin nuna mata kai ne kake son ta, ni ƙin ta nake ina ƙuntata mata. To gaskiya ka daina yi mini haka."
Bai sake duban ta ba, sai ya juyo kan Zaliha, cikin lallausan harshe ya ce, "Ki kwantar da hankalinki, zan yi bincike akan mutumin idan ba na gari ba ne ba zan amince ba. Ba zan sa mata ido ba ta kai ki wajen da za a cutar da ke. Ki daina kuka kuma ki ci gaba da yi mata biyayya, kada koda wasa ki mayar mata da magana ko ta faƙa ki faɗa. Sannan idan Abdullahi ya yi miki magana ki saurare shi, kada ki taɓa yi masa wulaƙanci."
Cikin dukkan ladabi ta ce, "Abba ya yi fishi fa sosai wallahi! Ba na jin ko a makaranta zai sake shiga sabgata, abin da Umma ta faɗa masa ya ce ya ji kuma zai yi aiki da shi."
"To shike nan ki bari ni zan neme shi zan yi masa bayanin da zai fahimce al'amarin. Kin dai ci abinci ko?"
"E, na ci."
"To ki je ki kwanta, Allah Ya yi miki albarka."
Miƙewa ta yi ta nufi kicin ta ɗauko masa abincinsa sannan ta wuce ɗakinta. Umma na bin ta da harara har sai da ta shige.
Abba kuma ya dube ta cike da jin takaici ya ce, "Watau Saratu na lura so kike ki zama marar godiya ga ni'imar da Ubangiji Ya yi miki, kuma ina mamakin lokacin da kika sauya haka. Kin tsangwami yarinya babu gaira babu dalili, kawai don biyan buƙatar kanki. Idan wata matsala kike gani a tattare da yaron ai ba shi kaɗai ba ne ke son ta, sai ki ba ta dama ta fitar da wani, ba ki ce lallai sai ta auri wanda ke kike son shi don cim ma buƙatarki ba. To ki sani ba zan laminci wannan abin ba, ina kallo ba zan bari ki jefa mini yarinya cikin ƙunci da damuwa ba."
Sama ta taso tamkar bubukuwa ta ce, "Yo akwai ƙuncin da ya wuce inda take burin kai kanta? To ka sani ni ma ai ina da hakki a kanta, don haka ba zan bari ta shiga cikin matsala ba. Kuma da kake cewa don buƙatar kaina nake so ta auri mai kuɗi, ai ba ni kaɗai zan ci arzikin ba, kai ɗin da kake faɗin haka sai ka fi kowa zaƙewa, a lokacin duk ka manta da haka."
"Wa? Allah Ya rufa mini asiri, ai ni ba girman kai ba, babu sirikin da zan buƙaci abin hannunsa. Alhamdulillah, na gode wa Ubangiji da abin da Ya ba ni. Ke dai da zuciyarki talaka ce har kika mayar da 'yar cikinki HAJA, kike neman kuɗi da ita, kika fifita ƙazantar duniya akan walwala da kwanciyar hankalinta sai ki je."
Daga haka bai sake tanka mata ba, nan ta ƙaraci sababinta ta yi shiru. Shi kuwa abincinsa ya ci yana gamawa ya miƙe ya nufi ɗaki ya yi kwanciyarsa.
***────────────────────────────
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ mai lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._**_•••©ᴀʙʙᴀɴ ᴀɪsʜᴀ_*
YOU ARE READING
TA ZAMA HAJA!
General FictionLabarin akan yadda aka mayar da aure tamkar hajar kasuwa a wannan zamani, wanda hakan ke haifar da tarin matsaloli.