Shafi Na Goma Sha Uku

2 1 0
                                    

*Ta Zama Haja! 13*
*Sadik Abubakar*
*Lafazi Writers*

https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980

Washegari da wurwuri Anty Maryam ta shirya ta diro gidan, kai tsaye ta wuce sashen Zaliha. Iske ta ta yi tana zaune a falo ta yi jigon. Sallamar Antyn ta ji, ta mike da sauri cike da murna ta rungume ta kafin ta karasa isowa tana fadin, "Sannu da zuwa Anty!"
Suka suka karasa ta sake ta nufi kicin ta dauko abincin da yi don karin safe amma ta gaza ci, ta hado da lemo ta kawo ta ajiye.
"SubhanAllah! Me ke damun ki haka duk kin zuge cikin 'yan kwanaki kalilan?" Anty Maryam ta fada bayan ta kare mata kallo, cikin alhinin damuwa take maganar. Zaliha ta kwantar da kanta akan kirjin Anty Maryam, hawaye tuni sun fara ambaliya daga idanuwanta.
"Anty tunda kuka kawo ni gidan ban ga ranar da za ta fito ta koma ga Mahaliccinta ba face na zubar da hawaye ba adadi, kullum rayuwata cikin baraza take kara shiga. Gori suke yi mini wai na zo cin dukiya, to zan ci kuma zan ci wahala. Manyan matansa biyu sun sha alwashin babu wacce za ta zauna lafiya matukar suna nan."
Ta dan dakata kadan sannan ta dora da cewa, "Yanzu jiya da Magariba Allah Ya tona asirinsu, Ya kare ni daga wani mugun abu da suka shirya mini. Na leko zan kulle kofata na ga matarsa ta biyun tana zuba mini magani a wajen da zan taka, da na ganta shi ne ta rikice tana sambatu wai uwargidan ce ta ce ta zuba mini. A cikin hakan sai ya zo, daga karshe dai ta sake ta, amma uwargidan ta kafe sai ya mayar da ita. Wallahi Anty bakinsu daya, ba ki ga wulakancin da suke yi mini ba. Ta ukun ce kawai take da kirki, ita ma haka suke azbatar da ita har 'ya'yanta. Don Allah ki taimaka mini, na rabu da wannan gidan kafin su illata ni." Ta karasa maganar da shasshekar kuka mai taba zuciya.
Anty Maryam ta jinjina kai tare da cizon lebe ta ce, "Ki daina kuka, na lura yaya Saratu ta fifita dukiya sama da farincikinki. Tun lokacin da na ji an ce mutumin mata ne da shi har uku, na ji ban gamsu da abin ba. Kuma ta boye mana abubuwa da yawa game da shi saboda ta san ba ta taki gaskiya ba. To idan ita ta gaji da ke, mu muna son ki kuma ba za mu zauna ba mu zuba mata ido don takamar ita haife ki ba, ta kai ki wajen da za a sabauta miki rayuwa saboda biyan bukatarta. Sam wannan ba gidan zamanki ba ne, In Sha Allah za a san yadda za a yi. Kodai ya ware miki gidanki can wata unguwar daban ko kuma ya san abin yi."
"Anty don ni ba na son sa ma wallahi!"
Shiru suka yi cikin yanayin damuwa kimanin mintuna biyu, Anty Maryam din ta katse shirun ta fadin, "Ni na yi mamakin yadda abin ya taso gadan-gadan lokaci daya kuma aka daina maganar Abdullahi."
"Wallahi duk Umma ce, ba ki ga ma irin cin fuskar da ta yi masa ba."
Cike da mamaki ta ce, Ikon Allah! To wai ni me ya samu yaya ne? Yanzu yaron ko bai ci darajar komai ba, ai ya ci ta dawainiyar karatunki da yake ba dare ba raba tun ba ki san kanki ba, wani abin ma sai ya hana kanwarsa ya yi miki. Amma shi ne za ta rufe ido? Shin arziki ba na Allah ba ne? Ba ka rena mutum domin ba ka san ya ya gobensa za ta kasance ba. Ki yi hakuri indai har da rabon zama tsakaninku sai kun zauna."
"Wallahi Anty abin da Umma ta yi akan auren nan ta saba wa Allah sosai, har wajen boka fa ta je karbo maganin da za ta raba ni da yaya Abdul."
Anty Maryam ta zaro idanu hade da yin salati, "INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN! Wai ni duk yaushe yaya ta sauya haka ban sani ba? Babu shakka ba da tunaninta kawai take aiki ba. To shi Abban naki duk bai san wainar da ake toyawa ba ne? Kuma me ya sa tun a wancan lokacin ba ki fada mini ba?"
"Shi Abba ya san wani abin kuma ya yi fada amma ta ki ji, ta ki fahimtar sa, ni kuma ta ja kunnena akan lallai kada na sake na fada wa kowa, idan ba haka ba sai ta saba mini."
"To shike nan, bar ta daga wajenta zan nufa, ba za ta cutar da ke ba. Ba a bori da sanyin jiki. Na san ba ki da wasa wajen kula da ibada, ki ci gaba da addu'a da karatun Kur'ani. Duk lokacin da za ki fita can ki yi addu'a, Allah zai tsare ki daga dukkan cutarwarsu. Su boka ne gatansu, ke kuma kina Allah wanda ran bokan yake hannunSa."
"To shike nan Anty na gode! Ga abinci nan."
"A'a na koshi! Hala ma ba ki karya ba ko?"
Ta yi murmushi tare da sunkuyar da kai ba ta ce komai ba. Anty Maryam ta ce, "To maza ki dauka ki ci, ki daina zama da yunwa. Ina ba ki tabbacin zan yi duk mai yi yuwa na ga kin fita daga wannan kuncin rayuwar."
Nan dai ta tsare sai da ta ci abincin sosai, tana mata yan nasihohin kwantar da hankali. Daga karshe ta ce, "Bari na tafi sai zuwa jibi zan sake dawowa."
"To Anty na gode sosai Allah Ya saka da alkairi, ki gai da gida, ki gai da mini da Ilham."
Tana fitowa ba ta zame ko'ina ba sai wajen Umma kamar yadda ta yi niyya, fuskarta a murtike babu fara'a ta shiga da sallama. Umman na tsakar gida ta amsa mata da, "Maraba da bakin hantsi, daga ina haka? Shiga mu je."
"A'a ba sai na shiga ba, bar ni daga wajen ma."
"Ban gane daga waje ba? Ina za ki? Sauri kike ne?"
"Babu inda za ni nan na zo kuma ba sauri nake ba."
"To fa! Ikon Allah! Ya na ga ranki a bace? Ina fatan dai lafiya?"
Anty Maryam ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce, "Yaya mene ne ribar abin da kika yi yanzu? Kin dauki 'yar fulillikar yarinya karama kin jefa ta cikin miyagun kuraye azzalumai, suna yunkurin haukatar da ita ko ma su fantsama ta uwa duniya ke kina nan hankalinki kwance babu abin da ya dame ki. Idan kin gaji da ita ne, ai mu ba mu gaji da ita ba, mu ma muna da hakki a kanta sai ki bar mana ita, mu nema mata farincikin da take nema."
Murmushi Umma ta yi tare da fadin, "Magana kike mini a baibai, fito fili ki fada mini me ke faruwa?"
"Babu wata magana da zan fada miki da ba ki sani ba, tunda kin shirya komai don biyan bukatarki. Ba ki duba halin da za ta shiga ba, shin TA ZAMA HAJA ne? Haba yaya! To gaskiya abin da na ji ba zan iya barin 'yata a wannan hali ba matukar ina raye. Gabadaya babu wanda yake son abin sai ke, ke din ma don ki karbi kudinsa ne kika tilasta mata ba don ranta yana so ba. Ko a da ba a yi auren dole an ga da kyau ba bare yanzu. Baya ga haka a dauki yarinya a kai cikin mushirikan mata, wanda sun yi jika da ita ba ma 'ya ba, babu wacce ba ta girme ni ba a cikinsu."
Ta dan tsahirta kadan sannan ta dora da cewa, "Jiya da safe ta kira ni take fada mini abin cutarwar da suka shirya mata, Allah Ya kubutar da ita. Don haka tunda Ubangiji Ya nuna mana, to dole mu san abin yi, mu janye ta daga cutarwarsu."
"To yanzu na fahinta, wato gara ta ta kai wajenki ke nan! Ba ki san Zaliha ba ne, duk abin da za ta fada miki yanzu karya ne. Wancan yaron ne yake ci gaba da hure mata kunne, shi ya sa za ta rika bijiro da abubuwa kala-kala. Kin manta da kawai iskancinta ne, za ta yi ta bari."
Cikin sigar mamaki ta ce, "Yaya kin ga halin da take ciki kuwa? Yanzun nan fa daga wajenta nata nake, yarinya ta rame ta lalace ta firgice duk ta sauya kamar ba ita ba, ana aure a samu kwanciyar hankali, yaro ya murje ya gyagije amma ita sai dai akasin haka. To ina amfanin auren ke nan? Kuma na tambaye ta sarai ta ce ita ba ta son sa ko kadan biyayya ta yi akan tilastawar da kika yi mata. To idan so kike sai an kawo miki ita a gadon asibiti ciwon zuciya ya kama ta ko kuma an haukata ta sannan za ki yarda, to mu ba za mu bari a kai ga hakan ba. Na zo ne na sanar da ke zan yi duk abin da ya dace domin na ga saka farinciki a ranta."
"To wai banda abin ki, ke ma kina neman zama marar tunani. Ina kika taba ganin gidan da ba mace daya ba an zauna lafiya? Ai da ma abin da ake tsammani ke nan, shirin da nake yi wajen jibi zan je na karbar mata dan taimako da maganin miyagu na kai mata."
Wani irin kallo mai cike da tuhuma Anty Maryam ta yi mata, da ta fuskanci ba za ta fahimce ta ba sai ta ce, "Shike nan yaya sai anjima ni zan koma!"
"Ki dakata ba abin fishi ba ne, ya kamata ki fahimci yaran zamanin nan idan aka rika biye musu da zabin nasu cutar da kansu za su yi, su cutar da wani ma."
Anty Maryam ba ta sake tanka mata ba, a ranta kawai ta ce, "Ai ke yanzu ga shi nan a matsayinki na uwar zamani kina cutar da 'yarki saboda kudi, kin zabi abin duniya sama da farincikinta. TA ZAMA HAJA! Ta jikinta za ki samu dukiya, to ba ki isa ba wallahi. Yarinya sai ta shaki iskar 'yanci kamar kowacce 'ya, mu zuba ni da ke!"
Nan ta fice ranta a bace sosai, tana tafe tana tunanin yadda za ta tinkari lamarin. Yini biyu ta kwashe tana sake-saken hanyar da za ta bi, daga karshe ta yanke cewa za ta sake komawa ta tattauna da Abba. Shi dayake namiji ne zai fahimce ta sannan kuma abin zai fi kyau a ce maza ne za su magantu a kai.
Bayan kwanaki uku da zuwanta gidan Zalihar, ta sake shiryawa ta koma kamar yadda ta alkawarta mata. Ita ma Anty Maryam din ta fi son rabuwar, to sai dai abin da wahala. Daga yin aure ba a ci Talata bare Laraba a ce an rabu, abin babu dadi wai mahaukaci ya ci kashi.
Dayake zuwan hantsi ta yi iske ta ta yi tana aikace-aikacen gida, ga gida har gida, komai ga shi nan a wadace washasha amma babu kwanciyar hankali. Cike da farinciki Zaliha ta dauki Ilham tana cewa, "Anty ba don makaranta ba ai bar mini ita za ki yi a nan."
Cikin murmushi ta ce, "Ai kam dai da sai ku yi zamanku, da ma kullum cikin tambayar ki take."
Nan da nan Zaliha ta hau kici-kicin yi musu girki, ta dora ta komo falo suka fara hira. Suna cikin hirar sai wayar Zaliha ta shiga ruri, dubawar da za ta yi ta ga sunan Umma na harbawa, ta dubi Anty Maryam ta ce, "Umma ce." Sannan ta daga kiran da sallama, bayan ta amsa mata ta ce, "Kin gan ni nan a kofar gidan naku."
Mamaki ne ya kama ta ta ce, "To sannu da zuwa bari na fito" Ta fada tare da sauke wayar ta sake duban Anty Maryam ta ce, "Kin ji wai Umma ce ta zo tana waje."
"Je ki shigo da ita toy." Anty Maryam ta fada ba tare da wani armashi ba.
Cikin rashin karsashi ta fito babbar kofar gidan, ta shiga da shiga mahaifiyar tata.
"Ikon Allah! Ashe ku ma kuna nan ke nan?" Umma ta fada bayan sun hada ido da Anty Maryam.
"Ai kam dai kin gan mu! Sannu da zuwa, ina kwana?" Suka gaisa.
Zaliha ma ta gaishe ta cikin girmamawa. Jim suka yi babu wanda ya sake magana, ba don ba su da abin fadar ba. Kowa na son wani ya bude babin tattaunawar. Zaliha ta mike ta nufi kicin ta zubo abinci ta kawo ta aje sannan ta sake komawa ta kawo kayan ruwa da lemuka.
Umma ta dan muskuta ta fito da wani kullin magani ta dubi Anty Maryam ta ce, "Kin ga hayakin da na ce miki zan karbo mata ta rika turarawa, babu abin da zai same ta sai alkairi."
Murmushin takaici ta yi tare da cewa, "Gaskiya yaya abin naki sai an hada da rokon Allah, yanzu a yanayin da kika iske yarinyar nan ba ki ji tausayin ta ya kama ki? Har kike mata sha'awar cigaba da zaman kaddarar nan, wai yaya ko sai kin ga gawarta sannan za ki yarda tana cikin damuwa? Ba don yarinyar mai biyayya ba ce ai da tuni ta yi duk abin da za ta yi ta kubutar da kanta, tsantsar biyayya ce kawai take zaune da ita. Zaliha tana cikin damuwa, ki fahimce ta, ki yi hakuri ki ba ta dama. Wannan mutumin ba sa'an aurenta ba ne, sannan wadannan guzumayen ko ni sun fi karfin na iya kishi da su, azzalumai ne marasa tsoron Allah."
"To ai ni duk yadda kike zuzuta abin ban ga ya kai haka ba. Idan kina batun rama ne, tun tana gida ta rame. Ta ki cin abincin arziki sai tunani ta ajiye a ranta, to kin ga kuwa ai babu laifin aure a nan. Ta cire tunani daga ranta ki ga idan jikinta bai dawo ba."
"Yaya ke nan! Ba musu zan ko jayayya zan yi da ke ba, amma kafin zuwan wannan mutumin cikin rayuwarta ai ba haka take ba. Shi ne ya rikita mata lissafi, domin jininsu bai hadu ba, koda ma kishiyoyin na gari ne, to shi kansa maigidan ba ta son sa, ba ya ranta don haka zaman zai yi wahala a samu yadda ake so. Kina ji dai kullum a kafafen yada labarai yadda auren dole ke jefa yara cikin tasku, wasu har hallaka kansu suke yi, wasu kuma su hallaka mazajen. To mu Alhamdulillah! Tamu ba irin su ba ce, ta yi hakuri kin lankwasa yadda kike so. Allah Ya nuna mana hadarin da zamanta a gidan zai fuskanta, to don me za mu kyale ta? Ba za mu fahimci damuwarta ba?Ban yi niyyar sake tattauna wannan maganar da ke ba, don dai mun hadu a nan ne. In Sha Allahu yau nake shirin komawa na samu Abbanta na yi masa bayanin halin da take ciki, domin na tabbata bai san wainar da ake toyawa ba. Matukar kuwa ya ji ta babu shakka ba zai bar 'yarsa cikin kunci ba, farincikinta shi ne abu na farko a wajensa, sabanin ke da kika mayar da ita HAJARKI."
"To na ji duk abin da ke ranki, yanzu me kike so a yi ke nan? Kina nufin raba auren za a yi?
"Ba abin da nake nufi ba ke nan, amma kuma idan hakan ma ta kama me zai hana, domin ni gaskiya ba zan iya barin yarinyata ta ci gaba da kunsar bakin ciki ba, tun da kuruciyarta ciwon zuciya ya kama ta. Abin da nake so shi ne, a tsaya a tambaye ta hakikanin gaskiya idan tana son sa shike nan sai a kafa masa sharudan da matansa ba za su gan ta ba bare ma su yi yunkurin cutar da ita. Idan kuma ba ta son sa to babu tilas fa, sai ya hakura. Ita kuma a ba ta dama ta zabi wanda za ta zauna da shi, wannan shi ne abin da ya zai haifar da abin da ake bukata, sabanin haka kuwa babu abin da zai haifar sai dimbin nadama, Allah Ya kiyashe mu."
Sun jima suna ta musayar yawu ba tare da daya ya fahimci manufar daya ba, daga karshe Umma ta ce, "Za a duba amma dai ba maganar rabuwa." Ita ta fara tafiya ta bar Anty Maryam a nan.
Sai da Anty Maryam ta sake mantar da Zaliha duk wata damuwa sannan ita ma ta tafi. To wannan ke nan!

────────────────────────────
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ mai lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*_•••©ᴀʙʙᴀɴ ᴀɪsʜᴀ_*

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 25, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

TA ZAMA HAJA!Where stories live. Discover now