*Ta Zama Haja! 08*
*Sadik Abubakar*
*Lafazi Writers*https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
BAYAN SATI BIYU
Ranar wata Asabar ɗin tsakiyar wata, Umma ta shirya ta tafi kasuwar Kurmi don yin wasu saye-saye. Ta je ta sayo abubuwan da take buƙata, a kan hanyarsu ta dawowa wani mai mota ƙirar A-kori-kura ya lafto kaya, burki ya shanye masa. Ya cacimi Adaidaitar da Umma take ciki da wasu masu tafiyar ƙasa ya haɗa da motocin da ke gabansu ya matse, abin babu kyan gani. Mutane biyu suka karye nan take har da direban Adaidaitar, hatsarin ya yi muni sosai, Umma ba ta samu karaya ba sai raunuka da bugawa, a sume aka kwashe su zuwa aisibitin Murtala sashen ba da kulawar gaggawa (Emergency). Wayoyin majinyatan aka bincika da nufin ko za a iya gano danginsu, cikin sa'a kuwa ana duba wayar Umma, lambar Abba ce kiran ƙarshe da ya shiga. Kiran sa aka yi, yana ɗagawa ya ji muryar namiji yana faɗin, "Barka da war haka, mai wannan wayar ce suka yi hatsari suna nan asibitin Murtala sashen gaggawa, amma da sauƙi."
A razane Abba ya riƙa faɗin, "SubhanAllah! To gani nan zuwa In Sha Allah!"
"Abba lafiya dai?" Zaliha ce ta tambaya cike zaƙuwar jin dalilin tashin hankalin Abban nata.
"A'a ba komai, wai su Ummarki ne suka yi hatsari, bari na je na gani. Ki zauna."
Bai gama rufe bakinsa ta zube ƙasa sumammiya, "INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN Zaliha!" Ya faɗa tare kama ta yana girgiza ta. Ɗaukar ta ya yi ya kwantar bisa kujera ya fara yi mata firfita, tana kwance shame-shame kimanin mintuna biyar ba ta motsa ba, tashin hankalinsa sai ya ƙara daɗuwa ainin. Tashin hankali ba a sa maka rana. Ana bikin duniya ake na kiyama. Ana wata sai ga wata. Abba ya ga ta-kansa, ga mata can ta yi hatsari bai san a halin da take ciki ba, nan kuma 'ya ta suma. Allah ke nan! Mai yin yadda Ya so, a lokacin da Ya so, kuma ga wanda Ya so. Yakan jarrabi bawa da masifu kala-kala ba don Ya tagayyara bawan ba, sai don Ya auna ƙarfin imaninsa.
Ganin Zaliha ba ta farka ba kuma can ana jiran sa hankalinsa zai rabu gida biyu, sai ya miƙe da sauri ya nemo Mai Adaidaita. Ya saɓi Zaliha ya saka a ciki ya ce ya kai shi asibitin Murtala. Tunda ita ma suma ta yi zai fi kyau ya kai ta asibitin don ya tara hankalinsa waje guda.
Yana isa aka shiga da Zaliha sashen kulawar gaggawa ita ma. Sai da aka duba ta aka sa mata ruwa sannan ya nemi ɓangaren 'yan hatsari inda aka kwantar da Umma. Ita ma ɗin tuni likitoci sun hau kanta ana ta ba ta kulawar gaggawa, sai dai har kawo wannan lokaci ba ta motsa ba. Ta bugu a ƙirjinta kuma ta zubar da jini sosai, lamarin da ya sa ake buƙatar yi mata ƙarin jini.
"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN!" Ita ce kalmar da ke ta maimaituwa a bakin Abba. Ba shakka wannan jarabarawa ce mai girman gaske daga Allah, tilas ta girgiza duk wanda aka aiko masa ita. Babban ƙalubalen da zai fuskanta a wannan jinya da zai yi ita ce rashin kuɗi, har yanzu ba a sakar masa albashinsa ba ga shi an shiga wata na biyar. A halin da ake ciki kuɗin hannunsa dududu ba su wuce naira dubu biyu ba.
Jadawalin abubuwan da ake buƙata za a yi wa Umma aka gabatar masa ciki har da jini lita ɗaya, abin da ya fi ɗugunzuma masa hankali ke nan.
To, a Islamiyya yaya Abdul bai ga Zaliha ba har lokacin ya ƙure, har ma aka tashi. Bayan Magariba ya yi salla sai ya biyo ta gidan ya ji ko lafiya? Iske ƙofar gidan ya yi a garƙame da kwaɗo, mamaki ya ɗan kama shi kaɗan haɗe da tunanin, 'to ina suka tafi haka har da kulle gida kuma ba ta faɗa mini ba?'
Yana tsaye a wajen sai ga wata 'yar maƙwabtan su Zalihar ta fito, sai ya tambaye ta, "Waɗannan unguwa suka tafi ne?"
Ta ce, "A'a Zaliha ce ba ta da lafiya sun tafi asibiti tun da rana."
Hankalinsa ya tashi nan take har wani gumi ne ya fara tsattsafo masa. Bai tsaya tambayar ta ko wane asibiti suka tafi ba, da sauri ya bazamo bakin titi ya kira lambar Abba bugu ɗaya ta shiga Abba na ɗagawa bai jira ya fara yin magana ba ya ce, "Abba barka dai, kuna wane asibitin ne?"
"Muna nan Murtala ɓangaren gaggawa."
Jin Abba ya ambaci ɓangaren gaggawa hankalinsa ya ƙara tashi, bugun zuciyarsa ya ƙaru, babu shakka shi ma da za a gwada jininsa a wannan lokaci to za a samu ya hau. A kiɗime ya tari Mai Adaidaita ya ce, "Mu je!"
"Ina za mu je?" Mai Adaidaita Sahu ya tambaya.
"Malam mu je da sauri ka kai ni asibitin Murtala."
Mai Adaidaita ya ja yana faɗin, "Allah Ya sawwaƙe!"
Suna isa ya zaro kuɗi kafin Mai Adaidaitar ya gama tsayawa tuni har ya dire ya kutsa kai cikin asibitin yana kiran lambar Abba, tare da tambayar inda suke. Zuwa lokacin Zaliha ta farfaɗo, ruwan da aka sa mata bai ƙarasa ƙarewa ba. Abban yana kusa da ita yana kwantar mata da hankali game da mahaifiyar tata.
Fitowa ya yi ya shiga da yaya Abdul, idonsa a kan Zaliha tana kwance, kusan minti ɗaya suna kallon juna, hawaye ya ciko a idonsa. Cikin dabara ya share shi duk da haka ta gani, matsawa ya yi daf da gadon ya ce, "Sannu ya ya jikin naki?"
"Jiki da sauƙi" Ta amsa.
Ya juyo ga Abba ya ce, "Mene ne yake damun ta?"
Cikin yanayin alhini Abba ya ce, "Wallahi lafiyarta ƙalau muna tare da ita a gida sai aka yi mini wayar uwar sun yi hatsari shi ne ita kuma ta faɗi a sume!"
"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN! Umma ce ta yi hatsari, tana ina yanzu?" A matukar firgice yaya Abdul ya riƙa yin maganar wadda ta janyo dukkan hankulan majinyatan kansu.
Cikin murya marar kuzari Abba ya ce, "Tana can sashen..." Sai ya dakata da maganar gudun kada Zaliha ta sake rikicewa. Miƙewa ya yi ya fito daga ɗakin, yaya Abdul ma ya biyo bayansa.
Suna fitowa sai ga jami'ar da ke kula da Umma ta taho ta sanar masa lallai fa ana buƙatar jinin da za a ƙara wa Umman da gaggawa. "Ya jikin yarinyar?" Ta tambaya.
Ya amsa mata da cewa, "Alhamdu Lillah! Ta warware saura kaɗan ruwan ya ƙare."
"To madalla, Allah Ya rufa asiri. Da ma batun jinin ne, ya kamata a samo wanda za su bayar a yau domin idan an ɗauka sai an tantance kafin a ƙara mata, ga shi lokaci sai ƙara ja yake."
"Wai Umman ce za a ƙarawa jini?" Yaya Abdul ya tambaya.
Abba ya girgiza kai kafin ya yi magana ya yaya Abdul ya dubi jami'ar ya ce, "Za a iya ɗibar nawa?"
"Me zai hana, gwadawa za a yi tukunna."
Gwajin aka fara yi sai dai bai yi daidai ba, amma za a ɗiba sai a yi musaya a wajen masu sayarwa. Sai sun ba da wani abin ihsani. Yaya Abdul ya ce, indai sai sun ba da kuɗi ne kawai a bar shi. Nawa ne lita ɗayar? Aka faɗa masa, nan take ya tinkari wajen da ake sayar da jinin ya sayo ya kawo aka tantance aka jona wa Umma.
Ruwan da aka sa wa Zaliha kuwa tuni ya ƙare har an cire mata, ta miƙe garau da ita. Ta matsa sai ta ga Umma amma Abba ya hana.
Yaya Abdul ya dubi Abba ya ce, "Bari na ɗan je gida yanzu zan dawo."
Ya fito ya sake tarar Adaidaita ya kawo shi gida, lokacin Inna har ta fara gyangyaɗi. Tashin ta ya yi a hankali ya cikin dabara ya sanar mata cewa, "Umma ce ba lafiya, tana zazzaɓi mai zafi. Suna asibiti ko za ki tashi mu je ga Mai Adaidaita Sahu har ƙofar gida, sai ya kai mu ya dawo da mu?"
Da kamar za ta ce masa ya bari sai gobe mana tunda dare ya yi kusan ƙarfe goma, sai ta ce, "SubhanAllah! Allah Ya sawwaƙe, bari na tashi mu tafi."
Jamila na kwance ta yi luf ashe ba ta yi barci ba, ta ji duk abin da suke tattaunawa. Fit ta miƙe ta ce, "Ni ma zan je."
Inna ta ce, "Babu inda za ki, ki zauna yanzu za mu dawo."
"Allah kuwa sai na je, ni ba zan iya zama ba ni kaɗai ku tafi ku bar ni."
"Rabu da ita ta zo mu tafi, ɗauko hijabinki." Cewar yaya Abdul.
Babu jimawa suka iso asibitin, ɗakin da Zaliha take ya kai su, aka gaisa tare da yin ya jiki. Sannan suka rankaya su duka zuwa inda aka kwantar da Umma. Sai a yanzu ne Zaliha ta yi tozali da mahaifiyar tata. Kuka ta saki sosai mai ɗaga hankali ta nufi gadon da gudu za ta rungume uwar, aka riƙe ta.
"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN! Inna ta faɗa cikin sigar tashin hankali, ta dubi yaya Abdul ta ci gaba da cewa, "Ka ce mini zazzaɓi take, ashe hatsari ta yi?"
Abba ya karɓi akalar zancen da cewa, "Ya faɗa miki haka ne don gudun kada hankalinki ya tashi sosai. Da a ce ya faɗa mini ma ba zan bari ya sanar da muku ba, tunda dare ya yi."
"Allah Ya sawwaƙe, Allah Ya kiyaye gaba, Allah Ya sa kaffara ce. Allah Ya ba ta lafiya."
Nan dai aka yi ta nuna jimami da alhini, yayin da ita kuwa Zaliha sai ɓarin hawaye take, Jamila kuma na aikin rarrashin ta. Da kyar ta ɗan numfasa. Yaya Abdul ya kira Inna waje gefe guda ya ce, "Inna don Allah ina roƙon ki wata alfarma ɗaya, ki zauna ki kwana tare da Umma, ba za a sallame ta ba a yau tunda ko jinin ma bai ƙare ba."
"Haba ɗan nan! Mene ne abin magiyar a nan? Ai ko babu komai tsakaninka da Zaliha ni mai jinyar Umma ce. Tun kafin mu same ku muke zumunci, indai wannan ne kada ka damu."
"Yawwa Inna, to yanzu bari na je na kawo muku kayan shimfiɗa da sauran abubuwan da za ku buƙata ko?"
Suna gama wannan tattaunawa suka koma can ɗakin jinyar, yaya Abdul ya dubi Abba ya ce, "Na san ba za a samu sallama ba a yau, to ga Inna za ta zauna a nan. Yanzu zan je na kawo mata shimfiɗa."
"A'a ba za a yi haka ba, sam tana fama da kanta, ka bar ta ta koma gida ta huta." Abba ya faɗa. Rufe bakinsa ke da wuya Innar ta ce, "Yo ai ba shi ne ya tsara haka ba, ni ce da kaina."
Nan fa yaya Abdul ya sake sunfayowa gida ya kwashi dukkan wani abu da ya san za su buƙata ya kai musu. Misalin ƙarfe goma sha ɗaya, su huɗu watau, Abba da yaya Abdul sai Zaliha da kuma Jamila, suka yo shirin dawowa gida. Adaidaita Sahu ɗaya suka hayo, suna tafiya yaya Abdul ya roƙi Abba da ya bar Zaliha su wuce da ita can gidansu, sai su kwana tare da Jamila. Hakan aka yi, Abban suka fara saukewa sannan suka isa gida, har lokacin dai Zaliha hankalinta ba ya jikinta, zuciyarta na can tunanin Ummarta. Ita a yadda ta gan ta ma gani take kamar babu rai a jikinta.
Cikin gidan suka shiga a falo suka zauna, yaya Abdul ya ci gaba da kwantar mata da hankali yana cewa, "Jikin Umma da sauƙi sosai, kawai ciwukan da ta ji jini ya ɗan zuba shi ne ake ƙara mata. In Sha Allah gobe za a sallame ta."
"Ko motsi fa ba ta yi za ka ce jikinta da sauƙi, ni idan ta mutu kawai ku sanar da ni." Kuka ya sake ɓalle mata sai da ta ɗan tsahirta sannan ya ce, "Ki yarda da abin da na faɗa miki. Umma jikinta da sauƙi rashin motsi ba wani abu ba ne, allurar da aka yi mata ne."
Da kyar dai shi da Jamila suka shawo kanta ta tsayar da zubar da hawayen. Jim kaɗan ya ce su shiga ɗaki su kwanta, shi kuma ya kwanta a nan falo. Sai Asuba ya tashi ya je Masallaci, bayan ya dawo ya tashe su suka yi salla. Jamila ta shiga kicin ta fara haɗa kayan karin kumallo. Shayi na gaske da wainar ƙwai ta yi, yaya Abdul ya sayo manyan burodi irin mai yanka-yanka. Ta ɗauko wani babban flas ɗin shayi ta maƙare shi fal sannan ta zuba wainar a wani flas ɗin abinci, bayan ta saka takarda a ciki domin kada gumi ya koma wa wainar. Tana gama haɗa wannan, sai ta zuba wa yaya Abdul ta kai masa ɗakinsa, sannan ta haɗo musu ta kawo falo. Zaliha na can ɗaki ta haɗa kai da gwiwa ta tsunduma kogin tunani. Ji take tamkar ta zama tsuntsuwa ta tashi ta nufi asibitin nan, ta zaƙu matuƙa da son ganin motsin mahaifiyar tata.
"Zo mu ci abinci." Jamila ta faɗa yayin da ta shigo ɗakin, miƙewa ta yi tare da sakin ajiyar zuciya. Jamila ta dafa ta sannan ta ce, "Ki yi haƙuri, dole ne hankalinki ya tashi. Amma ki riƙa addu'a maimaikon tara damuwar a ranki, ita cuta ba mutuwa ba ce, Umma za ta samu lafiya In Sha Allah."
Da haka ta rarraso ta suka dawo falon, sai dai ta gaza cin komai. Sam babu sauran abin da zai yi mata ɗanɗano a harshe muddin ba ta ga tashin Umma ba kamar kowa. Jamila ta buga ta raya akan ta ci ta ƙi, sai da yaya Abdul ya sa baki sannan ta ɗan kurɓi ruwan shayin kaɗan. Suna gamawa suka shirya suka fito suka tari Adaidaita Sahu sai asibiti.
Lokaci ɗaya suka isa da Abba, ajiye shi ke nan yana tsaye a ƙofar yana tunanin ya ya za a yi ya shiga asibitin hannu na dukan cinya? Idan marar lafiya ba ta iya cin abinci ba, 'yar jinyar fa? Ganin su da flas ya sanya ransa ya yi masa daɗi ya san abinci ne suka zo da shi. Gaishe shi suka fara yi sannan suka wuce. Ido biyu suka iske Umma, Inna a kusa da ita. Farinciki ya kama su gabaɗaya. Kuka ya sake ƙwace wa Zaliha, ta isa gaban gadon ta kifa kanta.
"Daina kuka Zaliha na samu sauƙi, tsautsayi ne ba ya wuce ranarsa." Umma ta faɗa cikin sassanyar murya.
Gabaɗayansu suka furta, "Alhamdu Lillah! Allah Ya ƙara lafiya, sannu!"
Yunƙurawa ta yi tana son tashi zaune, Inna ta kama ta ta jingine ta da bango, daidai lokacin jami'ar da ke kula da ita ta shigo duba ta. "Sannu ya ya jikin naki?" Ta tambaya.
Umma ta ce, "Da sauƙi sai dai ƙirjina na ɗan yi mini ciwo."
"To ba damuwa bari likita ya ƙaraso sai ya duba, yanzu za ki iya cin abinci. Allah Ya ƙara lafiya Ya kiyaye gaba." Ta fada tana ficewa.
Jamila ta buɗe kayan abincin nan ta zuba shayin a ƙananan kofuna, ta saka wainar da burodi akan faranti ta aje ɗaya a gaban Inna sannan ta ɗauki ɗaya ta matsa kusa da gadon ta fara ba wa Umma, a hankali ta ci ba laifi. Yaya Abdul kuma ya ɗauko magungunanta ya ba ta ta sha. Haka dai suka tsaya tsayin daka a kanta suna nuna tsantsar kulawa. Godiya da sa albarka kawai Abba yake wa yaya Abdul, ko ɗan da ya haifa a cikinsa ƙarshen hidimar da zai yi masa ke nan.
Misalin ƙarfegoma na safe likita ya zo, Umma ya fara dubawa inda ya umarci da a je a yi mata hoton ƙirjin da take ƙorafin tana ɗan jin ciwo. Aka yo hoto sakamakon ya fito likitan ya ce babu wata matsala, bugawa ce ta yi, magani ya rubuta aka ɗora ta a kai. ƙarfe goma sha daya, yaya Abdul ya turo Jamila gida ita da Zaliha su dafo abincin rana, cikin ƙanƙanen lokaci suka haɗa haɗaɗɗiyar taliya dafa-duka wacce ta ji dukkan kayan ɗanɗano da kifi banda. Suna gamawa suka juya asibiti, daidai lokacin likita ya rubuta wa Umma sallama, kasancewar jikin nata ya ƙwarara, abin da ya yi saura kawai raunukan da ta ji, su kuma sai a hankali za su ƙarasa warkewa. Don haka sai suka juyo gabaɗaya, a gida aka ci abincin.
Duk da sun dawo gida sai marece Inna ta koma gidanta. Dukkan hidima da kuɗaɗen da aka kashe a asibiti daga lalitar yaya Abdul suka fita. Ya yi namijin ƙoƙari sosai da kai komo wajen neman lafiyar Umma. Kuma a haka kullum sai Jamila ta kai abinci gidan har tsawon kwanaki goma, a ranar goman ne Abba ya riƙa jin shigowar saƙon kar-ta-kwana a wayarsa daga banki, albashinsa ne aka sakar masa gabaɗaya. Takansa ta Kano ya wanki ƙafa da kansa ya shigo kasuwar Kantin Kwari ya zaɓo wa Inna wasu dakakkun atamfofi manya guda biyu, bai zame ko ina ba sai gidan ya haɗa mata naira dubu goma kuɗin dinki. Cewa ta yi, "Ni duk abin da na yi, na yi don Allah ne kuma na yi wa zumunci, a tsakaninmu babu sakayya."
Shi kuma Abba ya ce, "To ai ko wannan iftila'i bai faru ba ni mai yi miki abin da ya fi wannan ne."
Godiya ta shiga yi masa tare da jero kalaman fatan alkairi da nasarar rayuwa mai ɗorewa.
Yaya Abdul na kawowa nan cikin zuzzurfan tunani nasa, ya saki ajiyar zuciya sannan ya miƙe tsaye yana ɗan yin tattaki a ɗakin. Wani sabon tunanin ya sake shiga, "Shin ta wace hanya zan sanar da Inna wannan rashin girma da daraja na iyayen Zaliha?"────────────────────────────
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ mai lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._**_•••©ᴀʙʙᴀɴ ᴀɪsʜᴀ_*
YOU ARE READING
TA ZAMA HAJA!
General FictionLabarin akan yadda aka mayar da aure tamkar hajar kasuwa a wannan zamani, wanda hakan ke haifar da tarin matsaloli.