*Ta Zama Haja! 10*
*Sadik Abubakar*
*Lafazi Writers*https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
Masu hikimar magana na cewa, "Zancen duniya ba ya ɓuya." Wannan batu haka yake ba shakka. A wayewar garin daren da aka kawo kuɗin auren Zaliha, tuni zancen ya dira a kunnuwan yaya Abdul da ɗumi-ɗuminsa. Labarin ya daki zuciyarsa matuƙa. Dauriyar da yake yi sai ya ji ba zai iya ba, ashe raɗaɗin da yake ji a baya sam ba komai ba ne. Wasa farin girki! Yanzu ne ya tabbatar da cewa ya rasa Zaliha. Ranar Juma'a ne aka kawo kuɗin, washegari Asabar babu makaranta, boko sai Islamiyya kuma yanzu ba ta zuwa. Ga shi yana masifar son su haɗu da ita, ba don komai ba sai don ya amayar mata da wasu martanai.
A da can bai cika ganin laifinta ba, to amma yanzu lokaci ya yi da ya kamata ya buɗe mata aiki, tunda dai ta kufce masa babu sauran tausayawa. Alatilas ya yi haƙuri zuwa ranar Litinin, wadda ta kasance ranar da za su fara rubuta jarabawa. Da wuri ya fita daga gida ya nufi hanyar da ya san tana bi, zuwa makarantar ya tsaya. Babu jimawa kuwa sai ga ta nan tana tafe cikin nutsuwa. Ba ta waige-waige idan tana tafiya, takan fuskanci gabanta ne kawai, don haka har ta gota shi ba ta lura da shi ba yana tsaye kan mashin ya juya baya. Kafe mashin ɗin ya yi, ya taka ya bi bayanta. Daf da ita ya ce, "Babu shakka na yarda da abin da zuciyata ta riƙa haska mini game da ke, yau ga shi kin tabbatar mini. Amma ina so ki sani Allah sai ya saka mini."
Jin maganar ta yi kamar daga sama, cak ta tsaya tare da waigawa. Ya ɗauke kansa bai yarda sun haɗa ido ba, ya ci gaba da faɗin, "Na gode wa Allah da ya nuna mini haƙiƙanin halinki kafin na aure ki. Zaliha ke maci amana ce, soyayyata a ranki ƙarya ce. Mahaifiyarki ta kira ni ɗan yaudara a gabanki, kalmar ta ƙona mini rai, matsayin uwa na ɗauke ta har gobe. Aure kuma ina miki fatan alkairi."
Yana faɗa ya juya zai tafi, ta yi sauri ta riƙo masa hannu ta ce, "Wannan ba ita ce maganar da ta sa ka tako ka zo har nan don mu hadu ba, idan ka koma to ka yi asarar ƙafarka da lokacinka. Idan kuwa ita ce ta kawo ka, to a iya sanina kai ɗin adali ne. Kana ba wa kowa damarsa ya faɗi abin ke ransa, ka faɗi abin da harshenka ke so, amma ni ka ƙi ba wa nawa bakin dama ya fesar da abin da ya gumtse. Shin ka yi hakan ne a matsayin sakayyar cin amanar da na yi maka?"
Ta ɗan tsagaita ba don ya ba ta amsar tambayar da ta yi ba, sakin hannunsa ta yi sannan ta ɗora da cewa, "Kodayake bai kamata na hana ka tafiya ba, je ka. Amma ni ma ina son ka sani tafiyar taka ta tabbatar mini da abin da nake zargi a kanka. Ban taɓa gaskatawa ba, duk lokacin da na ji zuciyata ta fara mini hasashen hakan, nakan nemi tsarin Allah daga shaiɗan don na san sharrinsa ne. To ashe gaskiya zuciyata take nuna mini, na gode da fatan alkairi. Kafin na tafi zan jaddada matsayin zuciyata a kanka, ba wai don ka yarda ba. Yaya Abdul, tunda Allah Ya sa na kawo munzalin fahimtar abin so da abin ƙi, ban taɓa jin son wani ɗa namiji ba face kai, kuma ba zan taɓa jaraba son wani ba a yanzu. Kai nake so! Kai zan ta so a kowanne irin yanayi, son ka ne a zuciyata. Idan Ubangiji Ya ƙaddara ba za ka zama mijina ba, to ina roƙon Sa Ya tsayar mini da wannan ƙaddarar a iya nan gidan duniya, a lahira ina roƙon Sa da ya haɗa ni da kai a gidan Aljanna. Ina da tabbacin zai amsa mini roƙona, domin duk abin da bawa ya kyautata niyya ya roƙi Mahaliccinsa a nan duniya ya ga bai ba shi ba, to tabbas Ya yi masa tanadin sa a dawwamammen gida wanda ya fi nan alkairi."
Gabaɗaya jikinsa ya yi sanyi liƙis, zantukan nata sun ratsa masa zuciya matuƙa. Tausayin ta ne ya kama shi sosai, babu shakka yarinyar tana son sa so na haƙiƙa, kuma kamar yadda ta faɗa babu wani namiji take so sai shi, shi ɗin shaida ne akan haka.
Cikin rarraunar murya ya ce, "Na gaza samun sauƙi da sukuni ne a raina! Tun ranar da Asabar ban rintsa ba, ko na kwanta babu abin da nake sai tunanin yadda zan yi rayuwa ba tare da ke ba, ba zan iya ba! Ba da son raina na faɗa miki waɗannan kalaman ba, kawai na ga kin nuna kamar ba ki damu da rabuwar tamu ba, ko nema na ba kya yi."
"Yaya Abdul ke nan! Yanzu ni ban yi wannan ƙorafin ba sai kai? Gabaɗaya ka janye mini lokaci guda, duk abin da zai haɗa mu magana ka dakatar da shi. Wani lokacin kafin a tashi daga makaranta ka fice kuma duk don kada mu haɗu ne. Idan ka shigo ajinmu ba ka taɓa yarda mu haɗa ido, ni har tsoron ka na fara yi. Zuciyata ni kaɗai na san abin da nake ji."
Hawayen da take ta jarumtar riƙewa suka cika mata idanu fal! Ɗumin saukarsu ta ji a kuncinta, cikin dabara ta juya ta share sannan ta ɗora da faɗin, "Kuma tun daga ranar da Umma ta faɗa maka wannan maganar ka rufe lambata, ka hana kirana shiga wayarka, ko saƙo na tura ba ya tafiya.'' Cikin sautin kuka maganar ta riƙa fita, abin da ya ƙara ɗaga masa hankali ke nan. Ya dube ta sosai ya ga yadda ta faɗa ta lalace, duk wanda ya san ta a baya yanzu ya gan ta zai yi tunanin lallai wani abin yana damun ta, kodai rashin lafiya ko kuma damuwa ta samu muhalli a zuciyarta.
Murya ƙasa-ƙasa ya ce, "Ya isa, ki daina kukan haka. Mu ci gaba da faɗa wa Allah kukanmu, babu abin da ya fi ƙarfinSa. Ki saki ranki, yau za a fara jarabawa. Mu tafi."
Ya janyo mashin ɗin ya karkata mata ta haye ya ja suka tafi. Suna tafe yana ci gaba da yi mata lafuzan tausasa zuciya, sai da ya kawar mata da damuwarta kafin su isa makarantar. To wannan ke nan.
YOU ARE READING
TA ZAMA HAJA!
General FictionLabarin akan yadda aka mayar da aure tamkar hajar kasuwa a wannan zamani, wanda hakan ke haifar da tarin matsaloli.