*Ta Zama Haja! 07*
*Sadik Abubakar*
*Lafazi Writers*https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
To a ɓangaren yaya Abdul kuwa, tafe yake babu laka a jikinsa. Jin lamarin yake kamar a mafarki. A haka ya isa gida, sallama ya yi cikin sassanyar murya. Inna na sauraren radiyo, ta amsa masa. Kai tsaye ya shige ɗakinsa. Kwanciya ya yi ya gaza tantance wane irin yanayi yake ciki, baƙin ciki ne ko kuwa? Zuciyarsa ta gaza tsayar masa da tunani guda ɗaya tartibi, da ya fara wannan tunani sai wani kutso. Juyi kawai yake bisa shimfiɗarsa.
"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN! Wace irin ƙaddara ce wannan? Wane irin tunani Umma take yi a kaina? Shin me take nufi da kalamanta na cewa Zaliha ba sa'ar aurena ba ce? Da ma fuska biyu ce da ita? a
A baki Musa a zuci Fir'auna? To me na yi mata har da za ta yi mini wannan hukunci? Ire-iren tambayoyin da suke ta sintiri a ransa ke nan. Kimanin mintuna goma sha zuwa sha biyar yana kwance a wannan yanayi. Ya miƙe zaune daidai lokacin zuciyarsa ta shiga tariyo masa wasu al'amuran da suka gabata a tsakaninsa da Zaliha da kuma mahaifiyar tata.
***
"To Zaliha kin ga dai halin da muke ciki a yanzu, Abbanki an rike masa albashi har watanni uku, don haka kawai ki yi haƙuri da makarantar nan. Ni da ma tun asali na san tsarabe-tsarabenta yawa ne da su, ni kuma kin ga ba wani abin nake ba bare na biya miki."
Cikin nutsuwa ba tare da nuna rashin jin daɗi ba Zaliha ta ce, "To shike nan Umma ba komai, ai na san da akwai za a biya mini. Amma don Allah ki yi mini alfarma ɗaya, a maimakon na daina karatun gabaɗaya, ina ga zai fi a mayar da ni maƙarantar gwamnati ko?"
"E haka ne, amma ita ɗin ma dole sai an kashe kuɗi. Ko banza sai an ɗinka miki wani uniform ɗin da kuma ɗan abin da za a miƙa."
"Shike nan Umma ba komai Allah Ya shige mana gaba."
Kwanaki biyu ke nan Zaliha ba ta shiga maƙarantar boko ba a sakamakon hukumar makarantar sun dakatar duk ɗaliban da ba su biya kuɗin makaranta ba. A rana ta uku na zamanta a gida, yaya Abdul yake tambayar ta a Islamiyya wacce take zuwa bayan La'asar zuwa Magariba, game da fashin da take a boko.
Ƙarya ta yi masa da cewa, "Wallahi ba ni da lafiya ne."
Murmushi ya yi mai cike da mamaki sannan ya ce, "Ikon Allah! Wace irin rashin lafiya ce ba ta tashi sai da safe, idan rana ta yi kuma sai a warke?"
Kunya ta lulluɓe ta ta rasa yadda za ta yi, wannan rarraunar ƙaryar tata ko ƙaramin yaro ba zai yarda ba. Ita da kanta ta yi mamakin ya aka yi ma bakinta ya suɓuce ta furta ta?
"Ki dai faɗi gaskiya abin da ya sa ba kya zuwa."
Shiru ta yi kanta sunkuye har yanzu kunyar ba ta sake ta ba, sannan kuma ba za ta iya faɗa masa gaskiyar abin da ya hana zuwa ba. "Kin ƙi yin magana, ko sai anjima da marece idan na zo gidan?"
Kai ta girgiza masa kawai cike da zaƙuwar su rabu ko ta samu sauƙin jin kunyar da ta sa ko motsawa ba ta son yi.
"To shike nan ki gai da gida, ki gai da mini da su Umma, sai na zo ɗin." Ya faɗa tare da juyawa ya koma cikin maƙarantar.
Sai da ta tabbatar ya shige sannan ta yi gaba. Dariya ita ma ta riƙa yi wa kanta akan wannan ƙarya wacce ko a cikin labaran littafi ba a cika jin ta ba. Shi ma dariyar ya riƙa yi mata, ya san ta yi ƙaryar ne don ta ɓoye masa wani abin. Halinta na jin kunya ya sa bai matsa akan lallai sai ta faɗa masa ba. Ƙila da daren ta iya fada masa.
Yana zama kwatsam sai tunaninsa ya kai kan kuɗin makaranta, dayake shi yake biya wa ƙanwarsa Jamila. Take sai ya ji a ransa ba mamaki rashin biyan kuɗin ne ya zaunar da ita a gida, kasancewar ya lura da rashin zuwan ba ita kaɗai ba ce.
Bayan sallar Isha ya isa gidan kamar ya saba, yaro ya nema ya aika, tana zaune a falo ta gama shiri, zuwansa kawai take jira. Miƙewa ta yi suka fito tare da yaron. Tana haɗa ido da yaya Abdul ɗin sai ta ji kunya ta sake tamke ta. Haka dai suka juya ciki tana gaba yana baya har zuwa falo. A ƙasa ya zube ya fara gai da Umma, ta miƙe ta ba su waje.
Murmushi kawai suke musaya a junansu kimanin minti ɗaya sannan ta ce, "Sannu da zuwa, ina yini?"
Ya amsa mata da cewa, "Lafiya ƙalau, ya ya jikin namu? Au ashe fa sai da safe ne ba mu da lafiyar!"
Kunya ta sake tamaimaye ta, sunkuyar da kai ta yi. Ya ci gaba da cewa, "Gaskiya wannan cuta tamu ta musamman ce, ya kamata mu gayyaci 'Yan Jarida su zo su yi hira da mu, domin wannan labarin zai ba da citta."
Cikin shagwaɓa sosai ta ce, "Allah zan tafi na yi barcina tunda tsokana ta kake yi."
Ya kwashe da dariya sannan ya ce, "Allah Ya ba mu haƙuri, ai ba tsokana ba ce. Sannu da jiki nake yi mana, wanda ba shi da lafiya kuma idan aka ce masa sannu daɗi yake ji."
Ta ɗan turo ƙaramin bakin nan gaba ta ce, "Ba za ka bari ba ko yaya Abdul? Ni lafiyata ƙalau kawai na gaji da zuwa makarantar ne."
Cikin dariyar ya ce, "Ikon Allah! Watau mun gaji da zuwa makarantar boko amma ba mu gaji da zuwa Islamiyya ba."
Ta sake zumɓurar baki ta ce, 'Yaya Abdul! Yaya Abdul! Shike nan bari na tafi kawai tunda yau sai dariya kake yi mini idan na yi magana."
"To ai idan mutum ya ji abin yin dariya ba ya sanin lokacin da take kufce masa, amma a yi mini afuwa ba zan sake ba. Yanzu faɗa mini gaskiya dai, idan ba haka ba kuma zan ci gaba da yin dariyar."
"To shike nan zan faɗa maka. Da ma ba komai ba ne da ma Abba ne. Ka ga wata makarantar kawai nake so a sake mini."
Dariya ce ta sake suɓuce masa, ya yi ta tulluƙa abarsa har sai da ta fara fusata sannan ya ɗan numfasa ya ce, "Gaskiya kyanki shirin drama irin mai ban ban dariyar nan. Daga rashin lafiya sai gajiya, yanzu kuma canja makaranta ma za a yi gabaɗaya."
Ta gama ƙulewa sosai ta miƙe baki a zumɓure za ta tafi. Cikin sigar rarrashi da tarairaya haɗi da sakin wani ƙayataccen murmushi ya ce, "Koma ki zauna ƙanwata ta kaina, abar alfaharina mai sa ni farinciki da nishaɗi."
Zaman ta yi ya riƙa bin ta da wani irin kallo mai cike da kulawa har sai da ta magantu da cewa, "Ya dai?"
Ya ɗan kauda kai tare da haɗiyar yawu sannan ya ce, "Abban ne ya ce za a canja miki makaranta ko kuwa?"
Kanta a ƙasa ta ce, "A'a ba shi ba ne, kawai dai shi yanzu ba..."
Ya yi saurin katse ta da cewa, "Ya isa haka gobe ki shirya ki tafi makaranta."
Ta rasa inda za ta sa kanta saboda jin kunya, ta fuskanci ya gane dalilin ƙin zuwan nata. Sun jima suna hira, yana zolayar ta ita kuma tana masa shagwaɓa tamkar ƙaramar yarinya.
Washegari da safe ta shiga kici-kicin shirin makaranta, Umma na kallon ta ba ta ce mata uffan ba, sai da suka gama karin kumallo ta ce, "Umma zan tafi makaranta, jiya da yaya Abdul ya zo ya ce yau na shirya na je."
"Don me za ki faɗa masa? Shi ma yana fama da ƙanwarsa da mahaifiyarsa duk nauyinsu na kansa." Abba ne ya yi wannan maganar cikin sigar faɗa. Umma ta karɓe zancen da cewa, "To ai ba komai ba ne idan ya biya mata indai ba tambayar sa ta yi ba. Ko tambayar sa kika yi ne?"
Kafin Zaliha ta buɗa baki Abban ya sake karɓe akalar zancen da fadin, "Ba haka ba ne, yaron nan yana yi daidai gwargwado. Bai kamata a siƙe shi ba."
Cikin tsantsar biyayya da bayyana dukkan gaskiya, Zaliha ta ce, "Abba wallahi ba roƙon sa na yi ba, da ya tambaye ni ma me yasa ba na zuwa ce masa na yi ba ni da lafiya. Shi ne ya ce to ai yanzu na warke na tafi kawai."
"To shike nan ba komai, Allah Ya yi miki albarka, Allah Ya sa a biya mu albashi sai na biya miki na shekara ɗaya ma na huta."
"Amin Abba!"
Ta faɗa sannan ta juya tana kallon Umma, "Yanzu fa sai ki ce sai na ba ki kuɗin tara ko?" Dariya ta yi tare da sunkuyar da kai. Umma ta ci gaba da faɗin, "Ai ni na san kwanan zancen, wannan kallon da biyu ake mini shi. Yau sai dai Abbanki ya fanshe ni, hutawa zan yi."
Naira ɗari Abban ya zaro ya ce, "To ga shi ko, a yi karatu sosai kuma a kula, Allah Ya tsare."
Da ta zo makaranta ba su haɗu da yaya Abdul ba sai da aka tashi, ta tsaya jiran sa kamar kullum. Mintuna kamar biyar bayan an ragu ya fito, "Mu tafi ko? Ya faɗa kafin ya iso kusa da ita.
Jerewa suka yi suna tafiya, ya sa hannu cikin aljihunsa ya zaro rasitin biyan kuɗin maaranta mai dauke da sunanta ya miƙa mata tare da cewa, "Ki saka wannan a cikin jaka."
Ta karɓa cikin jin kunya ta ce, "Yaya Abdul na gode sosai Allah Ya saka da..."
Ya dakatar da ita da cewa, "Ya isa haka, ba na son ki ce kin gode. Mene ne abin godiya don mutum ya yi wa ƙanwarsa abu, da ma ai haƙƙinsa ne na ya yi mata."
"Hmm! Ai wallahi godiya ta zama tilas! Kuma kada fa ka manta kai ne kake karanta mana haɗisin da ke cewa, 'Wanda duk ba ya gode wa mutane, to ba zai gode wa Ubangiji ba."
Murmushi ya yi kawai, ba shi da ta cewa, domin ta kai kat! Idan aka ce Annabi ya ce, to bi ake a sunkuyar da kai haɗe da mika wuya don neman dace da sa'a a ranar tsayuwa.
Jin ya yi shiru bai ce komai ba sai ta ce, "Ko da gyara a maganata?" Murmushi ne ɗauke a fuskarsa ya ce, "Wane mutum in ji mutuwa! Ni na isa na yi gyara a wannan maganar? Abu ɗaya dai nake so ki yi mini alƙawari!"
Martanin murmushin ta mayar masa sannan ta ce, "Ina jin ka yayana!"
"Yawwa ina son duk lokacin da makamanciyar wannan buƙata ta taso ki riƙa sanar da ni, kin ga yanzu a dalilin ba ki sanar da ni ba ne har kika yi asarar karatun kwana biyu. Koda ba za ki faɗa mini baki da baki ba, to ki riƙa rubutawa kina ajiyewa wajen da zan gani, don na san ki da jin kunya da zurfin ciki. Wannan ne alƙawarin da nake so ki yi mini."
Shiru ta yi, kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci kunya ce ta yi sansani a fuskarta. "Kin yi shiru ba ki amsa mini ba." Ya sake faɗa.
Shirun dai shi ne abin da za ta iya yi a wannan yanayi. A haka har suka zo daidai wajen da suke rabuwa. Da ta iso gida take nuna wa Umma takardar biyan kuɗin, farinciki ta nuna sosai da fatan alkairi. Shi kuwa Abba sam bai ji daɗin hakan ba za ganinsa kamar Zalihar ce ta tambaye shi ya biya mata. Sannan kuma hakan kamar zubar da ƙima ne. Daga ƙarshe dai ya ce da Zalihar ta faɗa wa yaya Abdul ɗin yana son ganin sa.
Washegari kuwa da dare yaya Abdul ya zo daidai lokacin da ya san zai samu Abban, bayan ya gaishe shi cikin ladabi da girmamawa. Abban ya ɗora da faɗin, "Jiya Zaliha take nuna mini abin arziki, kai da kake fama da kanka, ga hidimar su Inna, ai da ka bari wataƙila karshen watan nan a sakar mana kuɗaɗen gabaɗaya. Da ma wani ɗan bincike ake gudanarwa, abin da ya kawo cikas ke nan."
Kansa sunkuye cikin matuƙar risinawa ya ce, "Abba ai ba komai, tun farko ma ban sani ba da ko fashin kwana ɗaya ba za ta yi ba. Kuma ina roƙon ka don Allah ka bar mini wannan ɓangaren na karatunta."
"A'a kai haba! Sam ba zai yi yu ba. Idan amarya ba ta hau doki ba, ai ko ba za a ɗora mata kaya ba. Wannan ma da na san za ka yi wallahi ba zan bari ba. Wannan ɗin da ka yi na gode sosai Allah Ya saka da alkairi."
Cikin jin kunya ya ce, "Abba ai ba wahala ba ce, duk abin da na yi wa Zaliha kaina na yi wa, ƙanwata ce."
Haka dai suka rabu Abba na cewa ba zai ɗora masa wahala ba, shi kuma yana cewa ya ji ya gani zai iya.────────────────────────────
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ mai lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._**_•••©ᴀʙʙᴀɴ ᴀɪsʜᴀ_*
YOU ARE READING
TA ZAMA HAJA!
General FictionLabarin akan yadda aka mayar da aure tamkar hajar kasuwa a wannan zamani, wanda hakan ke haifar da tarin matsaloli.