Page 5

1 1 0
                                    

_*JUHAINA*_

_*Ummufatima*_

_*5*_

A bakin gado ya hango Ammi tana bawa Zuwairaa abu a baki, daga gani ruwan maganin da me maganin ya bayar jiya take ɗura mata a hankali yana shiga. Jin shigowar shi yasa Gimbiya tayi saurin ɗagowa tana kallon shi haɗe da sakar mai murmushi tana faɗin"Sannu da shigowa baba na, har ka tashi kenan? "

Gyaɗa mata kai Abdul yayi yana me ƙarasowa wajen, yana isowa ya durƙusa a dai dai ƙafar ta yace" Barka da safiya Ammi, da fatan kun tashi lafiya? Ya me jiki kuma?"

Ɗan murmushi tayi tana shafa kanshi kafun tace" Mun tashi lafiya lau Alhamdulillahi, saidai jiya ta kwana da zazzaɓi sosai, Amman jikin ta Alhamdulillahi gata nan dai, munyi sa'a ai, idan banda ka fara bata wannan maganin da ina tabbatar maka da cewa sai mun rasa ta, amman da yake Allah ya sa tana da rayuwa a gaba shiyasa ka fara bata temakon gaggawa".

Ɗan ɗagowa yayi yana komawa bakin gadon ya zauna, kallon fuskar fulanin yayi yana wani tausayin ta mara misaltuwa, fuskarta ya ƙara ƙarewa kallo ya ga ta ƙara yin wani ɗau kamar wacce bata da jini a jika abunka dama da farar fata.

Yana cikin wannan tunanin Gimbiya ta katse shi ta hanyar faɗin. "Jiya labari ya isar mun, wai wannan bawan ya ɗau ransa ko?"

Ɗan ɗagowa yayi ya kalle ta sai kuma ya gyaɗa mata kai jikin shi duk a sanyaye don beso hakan ta faru ba, yayi niyyar gana masa azabar da ko yana so ko beso sai ya faɗi gaskiya, domun kuwa azabar da zai gana masa sai ya gwammace mutuwar shi, amman ina hakan be faru ba amman duk da haka sai ya tsanan ta bincike.

Cikin rashin ƙwarin gwiwa yace "Haka ne Ammi, amman na miki alƙawarin wannan karan sai na gano wanda ya aikata mana wannan abun, na ɗaukar miki alƙawari".

Ɗan murmushi tayi tace "Ni kuma ina me ƙarfafa maka gwiwa, in sha Allahu za kayi nasara, jeka maza Takawa yana neman ka".

Tashi yayi a hakali suka fita daga cikin ɗakin yana kallon ƙanwar ta shi wanda ko don saboda ita sai ya nemo ko wanene ummul abasin faruwan wannan abun.

Basu daɗe suna tafiya ba shida Sulaiman suka kawo cikin fadar, yana shiga ya zube a ƙasa yana gaida Takawa, Sarkin fada ne yace"Sarki ya amsa gaisuwar ka yace kuma ka nemi guri ka zauna.

Guri ya nema ya zauna daga gefe yana me sunkuyar da kanshi ƙasa.

Saida aka ɗauki kamar minti biyu zuwa uku sannan Takawa yace "Alhamdulillahi ba tare da wani ɓata lokaci ba Galadima, naji duk abunda ya faru daga jiya zuwa yau a jikin masarautar nan, wasu ma akan idanuwa na abun ya faru, kuma nayi mamakin duk ta yadda hakan ta faru".

Shiru takawa yayi don jin me Abduljalal zai faɗa, shi kuwa Abduljalal jin shiru yasa ya ɗan ɗago kanshi yana kallon me martaba.

Haɗa idon da sukayi yasa yayi saurin sunkuyar da kanshi yana ɗan taɓe baki kafun yace "Allah ya huci zuciyar ka ranka ya daɗe".

Ya ƙarashe maganar yana wani ƙara haɗe girar sama da ta ƙasa, Allah ma yasa rawanin ya ɗan rufe mai fuska don haka ba a ganin abunda yake yi da kyau.

Takawa ne ya ɗan tsira mai ido yana ƙara karantar yanayin shi sai kuma yace"To dukkan alamu dai sun nuna cewa yanzu masaurata bata da wani tsaro me ƙarfi tunda dai har bayi za su iya saka mana guba a abinci kuma ba tare da kowa yasan hakan ba, sa'anan kuma ko wani gajan Bawa yana da damar da zai shigo cikin fada".ya ƙarashe maganar da alamun ɓacin rai cikin ta.

Abduljalal ne yace "Tuba nake ranka ya daɗe" A karo na biyu.

Sake ƙure shi da kallo takawa yayi kafun yace"Ni ban san ma meye amfanin baka Galadiman nan ba, sa'annan shi kuma Abdussamad a matsayin shi na magajin gari bama ya iya tsayawa a cikin masarauta bashi da aiki sai na tafiye2 daga wannan garin zuwa waccan garin, toh a gaskiya zan baka umarni me tsauri yanzu kuma bawai zaɓi na baka ba aa umarni ne, inaso nan da mako biyu ka nemo wainda suka aikata wannan abun sannan kuma da hujja masu ƙarfi. Zaka iya tafiya".

JUHAINAWhere stories live. Discover now