*ITA CE SANADI...!*
بسم الله الرحمن الرحيم
*_Littafina Paid book ne ba free bane. normal group is 500 vip 700, masu so ta prvt 700 zaku biya ta wannan account number:8102777485 Muhammad Zainab Dayyab Opay. Domin magana dani kai tsaye ga number ta nan 08102777485.👏_*
*Ranki shi daɗe dake nake... Idan kinsan ke ƴar siyi ki yaɗace kije na yafe miki base kin siya ba, kije can kisha zamanki Hajjajo uwar ƴan son banzan media😂*
01
*_GARIN KANO_*
A cikin Unguwar Galadanci da misalin ƙarfe 8:00AM na safiyar Litinin, Safa da marwa kawai nake cikin tsananin tashin hankali Mara misali, wanda ban taɓa samun kaina a cikin kwatankwacinsa ba tunda Uwata ta haifeni, babu abinda ke yanko min a wannan lokacin banda gumi, sabida tsananin tashin hankali. Lokaci bayan lokaci nake leƙo da kaina ta jikin labulen dake ɗakin, ina leƙen Kaka ta wadda ke ƙoƙarin dama mana kokon da zamuyi karin kumallo dashi. Cikin mutuwar jiki nayi baya tareda durƙusawa bisa ƙafafuna, Cikin sarewar gwiwa na kifa kaina a tsakiyar cinyoyina na saki wani irin kuka me cin rai, wanda ke fitowa Direct daka ƙasan zuciyata.
A dedai wannan lokacin banida zaɓin daya wuce in zubar da hawaye, wataƙila idan na zubar da hawayen zan samu sauƙin wutar dake cina A ƙasan zuciyata.Abubuwa masu yawa ne kecin zuciya da Ruhina, wanda bakina baze iya kwatanta baƙin cikin dake nuƙurƙusata ba. tambaya ɗaya ne ke min yawo A zuciyata wadda har yau na kasa samin cikakkiyar amsarta,"shin meyasa na biye ma Romon bakan da Halimah Bashir Ɗandago ke min, harta samu nasaran Shigowa cikin Rayuwata?."
Dafe kaina nayi da ƙarfi wanda naji yana barazanar sara min, duk a sakamakon kukan dana jima inayi.
A zahiri zan iya cewa Bani da wani zaɓi wanda ya wuce in rarrashi kaina, Don na lura kuka baze taɓa zama solution ga damuwata ba. ja da baya na farayi zuwa jikin bangon dake gefena, a hankali nasa bayana a jikin bangon tareda harɗe hannayena a saman ƙirjina, cikin mutuwar jiki na tankwashe ƙafafuna.
A zahirin gaskiya mafita kawai nake nema akan halin da nake ciki, amma nasan bazan taɓa samawa kaina mafitar ba dole sai da taimakon HALIMAH BASHIR ƊANDAGO......! Gabana ne yay wata irin dokawa , da sauri na fara girgiza kai cikin tsananin fargaba. Ƙirjina na bugawa da ƙarfi tamkar wadda nai gudin tsere da ingarman Doki maji ƙarfi
Rintse idanu na nayi da suri hawayen dake kwance a tsakiyar Kwayar idanu na suka zubo, A hankali cikin sarewa na ɗaga idanuwana da suka Koɗe sabida kuka, na sauke su akan wayata dake kan katifana. Rarrafawa nayi har inda wayar ke ajiye, sannan nakai hannu na ɗauka.
Na jima ina kallon screen ɗin wayar zuciyata na Harbawa da ƙarfi, da ƙyar na iya tattaro sauran ƙarfin gwiwan da nake dashi na lalubo numbar ɗin Halimah, sannan na danna mata kira.
Bugu ɗaya tai caraf ta ɗauka Kamar dama jira take na kira ɗin, cikin zumuɗi tun kafin nayi magana tai saurin cewa,"Haba Nusaibatul'afra don Allah, ya zakimin haka shikenan daga zuwa guri semu nemeki mu rasa?"Ajiyar zuciya na sauke cikin ƙarama kai ƙarfin gwiwa nace, "ke ni ba wannan maganar tasa na kiraki ba, so nake mu haɗu dake yanzun nan Pls, don wllh akwai gagarumar matsala."
Ɗan jim kaɗan Halima tayi kamar wadda ke nazari akan maganar Dana gama faɗa, sannan ta ɗan taɓe baki tace, " To Nusaiba Allah ya rabamu da matsala aike dama bakya rabo da yawan ƙorafi, wata ƙila ma ba wani serious abu bane amma duk kikabi kika ɗagama kanki hankali, ni yanzu bana gida gaskiya na fita ina TAHIR GUEST PALACE nida Sardauna Ali, idan zaki iya zuwa to se In jiraki a nan kafin na wuce gida."
Rintse idanuna nayi Ƙirjina yana tsananta bugu jin sunan wanda Halimah tace suna tare. Shiru nayi bance komai ba har seda Halimah ta kira sunana a kausashe, sannan na dawo daga gajeran tashin hankalin dana afka.
YOU ARE READING
ITA CE SANADI....!
Non-FictionAlwashin da EMRAN BELLO ƘARAYE yayi akaina abu ne da hankali baze taɓa ɗauka ba, amma kasancewarsa mutum mai kafiya akan Ra'ayinsa yasa tsoro mai tsanani ya ɗarsu a Zuciyata......! Hawayen da nake dannewa ne suka ziraro daga kwarmin idanuna, a lok...