*ITA CE SANADI.....!*
Zainab Muhmmd Chubaɗo
06
Halimah dake zaune suna cin Abinci, Ita da yayarta Sa'adatu wadda Nauyin riƙonta Ke wuyanta tun bayan Rasuwar iyayensu, wayanta dake gefen ƙafarta ya fara ringing ganin Sunan wanda ke kiranta yasa ta ɗaga kai ta kalli Aunty Sa'adatu, wadda Gabaɗaya hankalinta ke kan abincin da ke gabanta, sannan ta miƙe tareda answer call ɗin tabar Falon
Shiru tayi batace komai ba tana sauraron yanda ya ke sauke numfashi akai-akai, murmushi tayi mai sauti don tabbas ta san akwai magana a bakinsa, don haka cikin sigar jan hankali gamida baiwa lamarinsa mahimmanci ta ce, "jin shirun Sardauna Ali koda a wayane babbar alamace dake nuna cewar yana cikin damuwa, meze hana ka sanar dani ko dan ka taƙaita girman zullumin dake barazanar farmakar zuciyata......"
Murmushi ya saki mai sauti cikin sigar hilata gamida son kawar da tunaninta akansa ya ce,"Halie kenan.. koda ace na baiyana miki abinda ke Raina kai tsaye na tabbata bazaki fahimta ba, sabida ni kaina kallon matsalar nake tamkar gobara daga kogi, kinga kuwa maganinta se ikon Allah." yayi maganar cikin sanyin murya
Shiru tai batace komai ba sai juya maganarsa da takeyi a cikin ranta, amma har cikin ranta takejin tabbas akwai kitimurmura da Sardauna ke shirin ƙullawa. jin shirun nata yayi yawa ne yasa ya katse shirun ta hanyar cewa,"Hello kina jina kuwa?"
" Nidai, please let me know what your real concern is, even if I can't solve it for you, amma wllh zuciyata bazata taɓa samun nutsuwa ba matiƙar bansan abinda ke cikin Zuciyaka ba." Halimah tai maganar cikin taushin harshe gamida nuna damuwarta a fili.
dariya Sardauna Ali yayi cikin rashin baiwa maganarta mahimmanci yace," did I told you something is bothering me Halimah? Ni da bakina nace miki inada wata damuwa? kece kawai kike zargin inada wata damuwa bisa hasashenki, shine kawai na biye miki a hakan...."
" koda ace baka buɗe baki ka gayamin ba ni nasan akwai abinda ke damunka, don sautin muryanka kaɗai ya isa ya tabbatar min da hakan, amma da zaka sanar dani matsalarka wllh da tuni na jima da samo maka maganin damuwarka."
Wani dogon fasali yaja wanda yasa Halimah tai saurin janye wayar daga kunnenta don ƙarar sautin, sannan ya datse laɓɓansa da Fararen haƙoransa yana kallon Ac ɗin dake buso iska mai sanyi cikin ofishin. A ƙalla seda ya shafe mintuna uku ƙwarara ba tareda ya iya furta komai ba, har seda Halimah ta cire rai akan zece wani abu, can kuma ta tsinkayi muryanshi yana cewa,"kawai naji ina kewarki ne shiyasa ma na kiraki, amma kuma se kikai min bazata ta hanyar laƙantar Halaiyyata cikin ƙanƙanin lokaci." Sardauna yayi maganar yana lumshe dara-daran idanunsa yayinda kujerar da yake kai take juyawa dashi a hankali. Daga hagu zuwa dama
Haka kawai se ya samu kansa da ɓoye mata gaskiyar Abinda ke Ransa a kan Nusaibatul'afrah, don jikinsa yana bashi ko giyar wake Halimah tasha bazata taɓa haɗashi da ita ya Aureta ba, don ya jima da laƙantar abinda ke Ranta a game dashi wanda baya fata ya kasance har Abadah, gwara dai suci gaba da masha'arsu kaman yanda suka saba amma baya ji a ransa cewa ze iya Auran Ballagazar mace Irin Halimah Bashir koda ace matan duniya gabaɗaya sun ƙare....
"hmmmm Sardaun kenan a tunaninka ni sakarai ce da zaka iya kawar da tunanina cikin sauƙi haka ko? Ina Ai salon ya jima da canzawa yallaɓoi. Nifa ƴar barikice kamar yanda kake na tabbata akwai abinda kake ɓoye min wanda baka so in sanshi." tai maganar tana sakin wani makirin murmushi
Sannan tacigaba da cewa,"da alama ka manta wacece ni shiyasa kake ƙokrin yin wasa da tunanina har ka samu nasarar raina min hankali. Ga dukkam alamu ka manta cewa Halima tamkar iskar guguwa haka nake, idan har na taso to komai ƙanƙantar Rami binneshi nakeyi." Halima ta katse masa tunani ta hanyar faɗar haka.
YOU ARE READING
ITA CE SANADI....!
Non-FictionAlwashin da EMRAN BELLO ƘARAYE yayi akaina abu ne da hankali baze taɓa ɗauka ba, amma kasancewarsa mutum mai kafiya akan Ra'ayinsa yasa tsoro mai tsanani ya ɗarsu a Zuciyata......! Hawayen da nake dannewa ne suka ziraro daga kwarmin idanuna, a lok...