*ITA CE SANADI...!*
*_Littafina Paid book ne normal group 500 zaku biya vip 600 ta wannan account number:8102777485 Muhammad Zainab Dayyab Opay. Domin magana dani kai tsaye ga number ɗina 08102777485_*
Free page
02"Wai meye haka kukeyi sekace a zamanin jahiliya?, Wannan wani irin watsewa ne haka? idan har zamana a nan besa kunji kunyar idanuna ba, ya kamata ai kuji tsoron Allah, sannan Ku tuna cewar yana kallonku, Wani irin ruɗun duniya ne ya ke kwasar ku haka? Shin bakwa jin Tsoron Ranar da Rayukanku zasu bar gangar jikin ku ne? Yanzu idan mutuwa tazo ta ɗauke ku a wannan ƙazamin yanayin me zaku gayama ubangiji.....?" na Jera musu wa ƴannan tambayoyin ina sauke numfashi daƙyar, tamkar wadda ke ɗauke da ciwon Athma
Wani kallon galala Halimah ke jifana dashi, wanda yafi kamada na rainin hankali sannan ta gyara kwanciyanta a jikin Sardauna Ali, wanda tunda na fara magana yake kallona. Kauda kaina gefe nayi takaici da baƙin cikin dake cina a rai yana ƙara Ƙaruwa.
Taɓe baki Halimah tayi tana ƙare min kallo from head to toe tace,"Hmmm amma ban taɓa ganin ƴar renin hankali irinki ba Nusaibah Ko'a labari, wato kina nufin idan bamu bari don kunyar ubangijin mu ba, kenan semu bari don waƴan nan idanunki?, kinga malama kiyi Rayuwarki muyi tamu tunda dai bake kika halicce mu ba. In banda shegen sa'ido a Rayuwar jama'a ba abinda kika iya, wllh da ace kinsan tarin tagomashin abin arziƙin dake cikin harkar nan, da tuni kin daɗe da shigowa cikinta, Haba Nusaibah don Allah ki tsaya ki ƙarewa kanki kallo, gaki cikakkiyan mace kin haɗa komai da ɗa namiji zeji daɗi dashi, amma kin tsaya kina duhun kai da gidadanci. Kinga malama inzaki zubar da wannan ƙuntataciyan Rayuwar da kikeyi kisama ma kanki lafy to....."
Mamaki da al'ajabin maganar Halima yasa na saki baki kawai ina aikin kallonta, Idan har na fahimci maganarta dedai to tayin Fara Karuwanci take yi min. Rasa abinda zan ce nayi se kawai nai ƙasa da kaina bayan na rintse idanuna nace," ni zan wuce makaranta idan kin gama abinda kikeyi seki kira ni Ko ki sameni a languages zan jiraki a can, don bazan iya zama a ɗaki ɗaya tareda waƴanda basa jin kunyar ubangijinsu ba.......!" na ƙarasa maganar ina ƙoƙarin nufar ƙofan fita daga ɗakin, kaman daga sama na tsinkayi muryan Halimah tana faɗin, "wllh Nusaibah idan kikabar ɗakin nan bazan ƙara taimakonki akan ko wace irin matsala dazaki shiga ba......"
Mamaki ne ya kamani jin maganar da Halima take faɗa, haka nan sai na samu kaina da maimaita abinda ta gama firtawa. Murmushi ne ya suɓuce min wanda yafi kamada na tsantsar takai ci, hannu nasa na gyara zaman niƙabin dake fuskata sannan na ɗaga kai na kalleta ido cikin ido sannan na ce,"a iya zamana dake dama na taɓa neman wani abu a tareda ke ne? Idan na taɓa nema kin sani Halima,idan a ranki kin san ban taɓa neman alfarmar agajin taimako a garurinki ba ina ganin nafi ƙarfin ki buɗe baki kice zaki min barazar iska." na faɗi hakan ina ƙara girman idanuna ta cikin niƙabin wanda hakan ya tasirantu ƙwarai a gangar jikin Halima
Cikin rashin guzari ta janye idanunta daga cikin nawa bayan ta gyara kwanciyarta a ƙirjin Sardauna, ta ce,"naji ban taɓa taimakonki ba kamar yanda kika faɗa, amma nasan haka kawai bazaki biyoni irin wannan wajen ba, tabbas akwai agajin da kike nema daga gareni Afrah."
Kaina ne yai nauyi a lokacin dana tuna girman abinda ya kawoni ganawa da ita, nan take sai naji zuciyata tayi rauni irin raunin dana jima banji kamarsa ba, lumshe idanuna nayi cikin jarumtar son na ɓoye ruwan hawayen dake kwance a tsakiyar idanuna. Sannan na sake yin ƙasa da kaina don bazan iya jurar kallonsu a irin wannam ƙazamin yanayin ba nace,"haƙiƙa kin karanci ɗabi'ata dedai gwargwado, haka kawai kam bazan biyoki wannan ƙazamin gurin ba, sai dai ganinki a cikin wannan halin da nayi yasa na fahimci bazaki iya magance min abinda nazo gareki domin sa ba."
"maganar banza....! Idan kin san bazan miki maganin komai ba to uban me ya kawoki nan ɗin? Nifa bana son munafurci malama, karki zo ki fake da wani abin na daban kici min mutunci. Sannan da kika saki baki kina gaya min duk abinda kika ga dama ai ba gaiyatoki nayi ba taki ce ta kawoki, sannan duk lalacewata wlh ina miki amfani tunda wani lokacin dani kike jingina kina samun biyan buƙatun kanki. Na faɗa na ƙara wllh idan kika fita daga ɗakinan duk abinda zai taso miki a nan gaba bazan taimaka miki ba na rantse da Allah......"
YOU ARE READING
ITA CE SANADI....!
Non-FictionAlwashin da EMRAN BELLO ƘARAYE yayi akaina abu ne da hankali baze taɓa ɗauka ba, amma kasancewarsa mutum mai kafiya akan Ra'ayinsa yasa tsoro mai tsanani ya ɗarsu a Zuciyata......! Hawayen da nake dannewa ne suka ziraro daga kwarmin idanuna, a lok...