Episode 7

17 0 0
                                    

*ITA CE SANADI....!*

Paid book

Free page
07

Jin sallamar Emran daga bakin ƙofar Falon yasa Yakumbo Uwani ƴar Uwa ga Baba hajara ta ɗaga kai tana kalon ƙofar cikin maɗaukakin farin ciki, jinjina kanta tayi cikin alamu na gamsuwar cewa ƴar uwata na gab da samun lafiya, kallo ɗaya zakai mata ka fahimci itama shekarunta sun fara turawa. Amma duk da haka ita ce mai kula Baba Hajaran  dukda cewa akai masu hidimta mata ta wani fanin, sosai taji daɗin Zuwan Emran har hakan ya gaza ɓoyuwa ga kamilalliyar fuskarta, a ƙalla shekarunta zasu Haura sittin da biyu zuwa da uku. amma idan ka ganta garau take da sauran ƙwarinta, tamkar ba Dattijuwa ƴar shekara sittin da ɗoriya ba,  jikinta irin ɗan kyarau ɗin nan ne irin na  Fulanin Gwarzo.
Cin abinci mai kyau da gina jiki ne ya taimaka wajen dedaituwar ƙarfin jikinta, cikin jin daɗin zuwansa ta  ta ce,"Maraba da ja'irin miji wanda baya sauke nauyin matarsa,. nan Hakimi yaita zabga maka kira ta waya amma da ike bakai da ranka ba cewa kai wai kanada abinyi." ta faɗi hakan tana wugar masa harara daga nan inda take a zaune

"tunda gurinki nazo ai seki maida ni" cewar Emran
"ni a wani dalilin zakazo gurina? Waƴanda suka damu da kai ɗin dai kuje can ku ƙarata, suyi ta fama da kai kamar kullum, don wllh iya zama da kai kam se wanda  Ubangiji ya halicce shi da baiwar Haƙuri." tai maganar tana ƙoƙarin kwanto goron dake ɗaure a bakin Zaninta.

Jin sunan da Yakumbo ta ambata ne yasa Baba Hajara dake kwance ta buɗe idanunta a hakali, waƴanda turawar shekaru tasa ƙwayar idon ta sauya launi daga baƙi zuwa launin blue mara cizawa. Bugu da ƙari ga raunin ganin da yaiwa idanunta dirar mikiya, a nitse ta fara ƙoƙarin yunƙurawa zata tashi. Da taimakon ya kumbo ta miƙe ta zauna sannan ta kai hannuntata lalubi gilashinta ta maƙala a idanunta ta ce, "Uwani da gaske kike Emrana ɗan wajan Bello ne yazo?"

"da gaske nake yaya shi ɗinne dai  Ba wani ba, Kin ganshi nan dai Kamanni duk sun  canza zuwa na matashin Banasare. ni dai kam Zuwan Masu jajayan kunnuwan nan  be mana Rana ba. Don gabaɗaya Sun sauya mana Emrana gabaɗayansa kamar bashi ba, yaro ya zama sankacece a tsaye sai kace ɗan kokawa sabida Allah? be tsira da Uban komai ba se farin yadin daya ziro a jikinsa ya taho inda kika san me shirin shiga kabari....."

Shidai Emran Banza yay mata don bata ita yake ba, babban burinsa shine ya isa inda Baba Hajara ke kwance  yaga halin da take ciki.

Taɓe baki Yakumbo tayi tana wani ƙanƙance idanu ta kuma cewa," Shi dai Bello yana fama wllh. Salihin bawa me haƙuri da bin Allah Irinna mutanan farko, amma sai gashi Ubangiju ya azurtashi da miskilin Ɗa. irin wanda bahaushe kance yafi mahaukaci ban haushi, ni dai inajin da Emrana a Kurma ko bebe Kuluwa ta haifo ka. da Allah kaɗai yasan Irin rigimar da zaka dinga ɗakkowa Hakimi a  garin ƙaraye. Ita dai yayata bazan zuba ido ina kallo takaicinka ya kaita kabari ba, gwara in tisata gaba mu nufi gidan Ubanmu Limamani Gwarzo kowama ma ya huta."

Shi dai Farouq dake tsaye a bakin ƙofar Falon kallonta kawai yake  a ransa yana girmama shegen Surutu irin na wannan dattijuwa, badan kar yay mata sharri ba da se yace tunda ta fara magana ko Yawu bata haɗiya ba.

Da sauri Emran ya isa inda ƙatuwar katifar da Baba Hajara ke kai yay saurin kama hannunta ya damƙe cikin nasa, kana kallonsa zaka fahimci a rikice yake, sai dai kamewarsa da nutsuwarsa bazasu barka ka fahimci ainihin firgicin dake zuciyarsa ba. A nitse yake kallon dattijuwar Fuskarta yana mamakin yanda akai ta rame sosai, se kace wadda ta shekara tana ciwo ya ce,"meke ke damunki haka kikai irin wannan  Ramar? me yasa Hakimi be sanar dani da Wuri ba?" yay maganar bakinsa na rawa. Don a Rayuwar Emran  yana  iya jurar komai amma banda abinda ze Taɓa lafiyar waƴannan tsofaffin Biyu, Hakimi da Baba.... idan akwai abinda ke ɗaga masa hankali a tagaiyara nutsuwar rayuwarsa to be wuce waƴannan tsoffi biyu ba, Waƴanda yakewa kallo a matsayin ganiyar Farin cikinsa.

ITA CE SANADI....!Where stories live. Discover now