*ITA CE SANADI.....!*
08
Na isa makaranta lfy amma se dai ban samu lecture ɗin dana taho dominta ba, a lokacin dana isa P.T.F a dai-dai lokacin ɗaliban ajinmu suke tururuwar fitowa, Raina ne ya ɓaci a lokacin dana kalli agogon fatar dake ɗaure a tsintsiyar hannuna.
Daga can nesa dani na hangi class captain ɗin mu hannunsa ɗauke da doguwar takarda, hakan yasa na nufi gurin harda ɗan guduna don ko ba'a gayamin ba nasan attendance paper ce. Ina zuwa gurin na marairaice Fuska na ce,"Ahmad banyi attendance ba yanzu nazo, don Allah ka bani nima na rubuta sunana." nai maganar cikin sanyin murya
Harara ya ɓalla min tareda ɗauke kai ya ce,"bazan bayar ba da can meya hanaki zuwa da wuri kamar kowa?"
"Eyyah Ahmad Don Allah fa nace maka, amma dai kasan bana missing lectures da gangan ko?"
"Ae tabbas bakya missing lectures a shekarar da kika shigo makarantar nan, kafin ki fara ƙawance da waccan ƴar kwaltar Halimah, yanzu kam ai lamarinki sedai mutum ya kalla da idanunsa kawai, amma wllh Nusaibatul'afrah kin canza kamanni a idanuna ko magana ma ni ban cikaso kinai min ita ba, don gudin kar Zama da maɗaukin kanwa ya janyo mini farin kai." daga haka Ahmad yay gaba ya barni Tsaye nai sototo kamar gunki ina binsa da kallo cikin tsananin tu'ajjabi, harya ɓace min da gani ban dena aikin kallonsa ba.
Ina nan tsaye Ubaidah Muhammad Arabi ta iso inda nake ta dafani ta baya, wannan dafawar da taimin ita ce ta dawo dani daga rijiyar mamakin da Ahmad ya cilla ni. Cikin madaukakiyar Fara'a na dubi Ubaidah na ce,"Amaryar Ran gida don wllh yau sedai Hausawa su shafa min lfy sabida na sauya musu karin magana."
Dariya Ubaidah tayi ta ce,"oho miki dai ke kika sani ni dai muje Gurden don wllh yunwa nakeji." tai maganar tana jan hannuna
"Amma Ubaida keda kike jin yunwa aiba gurden ya kamata mu nufa ba, village ya kata muje a nan zaki samu abinda ze riƙe miki ciki." nai maganar har lokacin tana riƙe da hannuna.Shiru tayi bata bani amsa ba har muka isa cikin Gurden ɗin, kallon mamaki nakebinta dashi ganin ƙatuwar jakar dake rataye a kafaɗarta sekace wadda ke goyo, buɗe jakar tayi ta fito da babban sallaya ta shimfiɗa mana muka zauna a ƙasan bishiyar darbejiyan dake gefe, sannan ta fito da wata ƙatuwan leda wadda ke ɗauke da hatimin chiken Republic a jiki.
Nidai banda ido babu abinda nakebin Ubaida dashi tun bata lura da irin kallon da nake mata ba harta fahimta, Murmushi tayi kawai dedai lokacin ta fito da take away ɗin roba guda huɗu ta ajiye biyu a gabana sannan ta ijiye sauran biyun a gabanta, fuskarta har lokacin ɗauke da murmushi ta ce,"bisimillah muci abinci sannan kuma wllh bana son kimin wata tambaya balle kimin gaddama ." tai maganar tana ɓatar da murmushin da ke saman kyakkyawar Fuskarta, Don masha Allahu Ubaida badai kyau ba.
Dariya nayi na ce,"hmmm da alama matar Hashim yau masifa takeji dani sedai kuma ni Nusaibatul'afrah ba gwana bace a wannan fannin." nai maganar cikin son jin amsar da Ubaidah Muhammad Arabi zata bani, amma kuma se tai bris dani ta fara cin abincinta.
Cikin ɓoyayyen sanyin jikin daya mamayi ilahirin jikina nake bin abincin da kallo, nan take Ammah ta faɗo min a rai sakamakon danƙareriyar kazar danai arba da ita a saman shinkafar.
Tuna cewar na barta a gida babu komai a cikinta se ruwan koko wanda ko ƙosai babu a cikinsa yasa naji zuciyata ta karye, banyi Aune ba naji wasu zafafan hawaye masu matiƙar ɗumi suna bin fuskata, ubaidah wadda taji nai ɗib ta ɗago ido tana kallona ganin ina hawaye yasa ta ajiye spoon ɗin robar dake hannunta ta dubeni cikin nuna kulawa ta ce,"Afrah lfy ? Meya faru kike kuka?" ta jera min all this question at same time.
Saurin share hawayen nayi tareda ƙaƙalo murmushi na wadata fuskata dashi cikin tsananin son na ɓoye damuwata, don bazan iya gayawa Ubaidah ainihin sirrin gidan mu na rashin samun wadataccen abincin safe ba, amma kuma a fili se na ce,"wllh Ubaidah tsabar farin ciki ne ya sanya ni zubar da hawaye, don banyi tsammanin wannan babbar kyautar daga gareki ba matar Hashim."
YOU ARE READING
ITA CE SANADI....!
Non-FictionAlwashin da EMRAN BELLO ƘARAYE yayi akaina abu ne da hankali baze taɓa ɗauka ba, amma kasancewarsa mutum mai kafiya akan Ra'ayinsa yasa tsoro mai tsanani ya ɗarsu a Zuciyata......! Hawayen da nake dannewa ne suka ziraro daga kwarmin idanuna, a lok...