*ITA CE SANADI....!*
Paid book
05
Da ƙyar na iya tattaro ƙwarin gwiwan da yay min saura, na ɗaga wayar tare da karawa a kunne na, cikin muryarsa mai zurfi da kauri ya ce,"Allah ya tarfawa garinki Nono Nusaibah, badan haka ba wllh babu abinda ze hanani keta alfarmarki a safiyar yau. Na kwana da kwaɗayin son koya miki iskanci, amma sai gashi wani uziri ya taso min wanda zai hanani aiwatar da muradina akanki"
Wata ɓoyayyiyar Ajiyar zuciya na sauke wadda sautin ta ya isa ga kunnen Emran, murmushi ya saki me sauti wanda har ina iya jiyo sautin a kunnena ya ce,"meye na saurin sauke ajiyar Zuciya tun yanzu? sai kace wanda nace miki na janye ƙudirina akanki? Hmmm Nusaiba kenan ai wllh duk kaffa-kaffan Budurwa dole ne a sha manta wata rana, so kisa a ranki cewa Emran baya ƙyale duk wani abu da yay alwashi akansa. don haka ina mai baki shawara kije ki shiryawa ranar da zaki haɗa gado dani, idan ta kama kiyiwa kanki tanadin maganin rage raɗaɗi, don zangewa zanyi in koya miki iskancin da baki da ilimi akansa...." yana kaiwa nan a maganarsa ya katse kiran tareda maida kallonsa ga agogon fatar dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa.
Kai tsaye inda yay paking motarsa ya nufa cikin nitsatsen takunsa mejan hankali har ya isa jikin motar, yana ƙoƙarin buɗe motar Farouq Ibrahim ya ƙaraso yana jifansa da wani shu'umin mirmushi ya ce,"Mutumina kaga yanda ka zuba kyau kuwa, anya ba rabon yin aure bane ke shirin kaika Ƙaraye ba?" yay maganar yana kallon Emran wanda ke sanye da riga da wando na farin yadin Filtex me taushi da ɗaukar idanu.
Wata uwar harara Emran ya watsa masa cikin tsananin jin haushin maganarsa ya ce," Uban Rabo ne ze kaini ba rabo ba, shege wanda baka faɗin Alkhairi." yay maganar a dedai lokacin da yake shiga cikin motar yaiwa kansa mazauni.
Dariya Farouq yayi hallau cikin salon zolaya ya kuma cewa,"haba yallaɓoi daga yi maka fatan alkhairi shikenan sai kai min sakaiya da zagi? Ina laifi da nai maka fatan Raya Sunnar manzon Allah?" yay maganar yana tsuke fuska kamar gaske.
Ko kallonsa Emran beyi ba ya ce," to don iyayenka ce maka akai ina buƙatar ajiye mace a gefena ne?"
"idan baka buƙatar mace A tareda kai why kake son rusawa Nusaibatul'afrah Rayuwarta?" Farouq ya tari numfashinsa ta hanyar faɗin haka.
"is Just to teach her a good lesson wanda she will never forget it in her life....! Shine kawai" Emran yay maganar kamar ba daga bakinsa ta fito ba.
Gyara zama Farouq yayi still yana kallonshi bai janye idanunsa ba ya ce,"Emran meze hana ka yafe mata kuskuren da tai maka, tunda kafi kowa sanin cewa Nusaibah Othman Galadanci ba ƴar iska bace."
" yafe mata ɗin ne banyi niya ba. ko ana dole akan yafiya ne?"
"a'a sam ba'a dole akan yafiya amma dai ina so ka sani cewa ubangiJi ma munai masa laifi ya gafarta mana ballanta kuma mu ƴan adam, sannan a matsayinmu na ƴan adam idan mukace zamu rayu ba tareda muna yin yafiya a tsakanin mu ba to wllh duniyar ma bazata zauna lfiya ba......"
"hmm cewa zakayi shiga shara ba shanu ka fara. shiyasa kake ƙoƙarin shigar da kanka cikin abinda bai shafeka ba,"
"ni dai koma dai me zakace kace amma don Allah Abokina ka Yafe mata maganar ta wuce haka pls."
"wllh Farouq bazan iya yafema Yarinyar nan ba har sena nuna mata cewa ni cikakken ɗan iska ne kamar yanda ta kirani, ta yanda a duk lokacin da taji an ambaci sunana se gabanta ya faɗi...." daga haka yayma motar key sukabar harabar faculty ɗin, ba tareda ya ƙara tanka maganar Farouq ba. don ya lura nema yake ya shigar da kansa cikin abinda bai shafesa ba...
A haka suka kama hanyar ƘARAYE farouq yana girmama baƙar zuciya irinta Emran wadda babu yafiya a cikinta
******
YOU ARE READING
ITA CE SANADI....!
Non-FictionAlwashin da EMRAN BELLO ƘARAYE yayi akaina abu ne da hankali baze taɓa ɗauka ba, amma kasancewarsa mutum mai kafiya akan Ra'ayinsa yasa tsoro mai tsanani ya ɗarsu a Zuciyata......! Hawayen da nake dannewa ne suka ziraro daga kwarmin idanuna, a lok...