Episode 3

13 2 0
                                    

*ITA CE SANADI...!*

*_Littafina Paid book ne ba free bane. normal group is 400 vip 600, masu so ta prvt 600 zaku biya kuma ta wannan account number:8102777485 Muhammad Zainab Dayyab Opay. Domin magana dani kai tsaye ga number ta nan 08102777485.👏_*

03

Ban ƙara sanin inda kaina yake ba, se farkawa nayi na ganni kwance a gadon Asbitin makaranta dake old site. Sakamakon jinina dake barazanar hawa sabida tashin hankalin dana samu kaina a ciki, hawaye ne ya fara bin fuskata.

A hankali na fara buɗe idanuna da sukai min nauyi tamkar an ɗora min ƙaton dutse, har na gama buɗesu tar a saman silin ɗin ɗakin, "sannu Afrah ya jikin naki?" na tsinkayi muryar Halimah a saman kaina, a ɗan tsorace na juyo don na tabbatar da cewa ita ɗince kokuwa kunnuwa na ne ke ruɗata.

Murmushi ta sakar min wanda na jima banga tayi min Irinsa ba, ɗauke kaina nayi gefe ina jin wani irin yaayi yanamamayar gabaɗaya ilahirin jikina. Tamkar wadda aka jonawa lantarki haka nake jin zuciyata na karkarwa sabida tasirin tsoron dake jikina, da ƙyar naƙe iya jan numfashi saboda wahalallen yamayi da nake ciki. Rintse idanu nayi da ƙarfi a lokacin dana ji tsokar zuciyata tana tattarewa a guri guda, a cikin raina nake hasaso girman bala'in dake shirin tinkaro ni. Cikin wata wahalalliyar muryar wadda ke fallasa asirin zuciya da gangar jiki na firta kallamar "Innanillahiwa'inna'ilaihirraji'un.....!" al'amarin daya janyo hankalin Halima gareni kenan ta tsareni da manyan idanunta tana kallona.

Harara na galla mata sannan na sake ɗauke kaina don bana buƙatar tayi min tambayar da na gani kwance a tsakiyar idanunta. Ganin haka yasa tayi murmushi taci gabada danna wayarta

Niko a can ƙasan zuciyata ba abinda nanatawa sai," ya Allah ka bani mafita akan wannan iftila'in dake shirin zama barazana ga mutunci na." Haka naita juyi a saman gadon ƙirjina yai bala'in nauyi kaina yana tsananta ciwo.
Ko buɗe idona bana iya yi sabida sarawar da kaina keyi, a taƙaice dai bamu bar Asibitin ba sai ƙarfe Uku na rana sannan aka zare min ƙarin ruwan da aka saka min. Halimah ce ta taimaka min muka fito zuwa inda ake karɓar magani, ƴar takardan da likitan yai rubutu a kai Halima ta miƙawa mutumin dake cikin inda ake bada maganin. Karɓa yayi ya fara duba takardan sannan ya ɗaga kai ya kalleni ya ce,"ke yanzu ƴar ƙaramarki dake me yai miki zafi a wannan rayuwar da zaki janyo ma kanki masifa? Anya kinsan illar da Hawan jini ke janyowa bawa kuwa?" yayi maganar yana tsareni da idanu cikin alamun nazarta.

Ƙasa nai da kaina na gagara cewa komai, jinjina kai yayi sannan ya ajiye takardan a gefe ya ɗauki leda ya zuba min maganin da aka rubuta a jikin takardan sannan ya miƙawa Halima ya ce,"Allah ƙara sauƙi."
"Amin ya Allah mun gode ƙwarai da gaske." Ta faɗi hakan tana kama hannuna a hankali muka fice daga cikin gurin a hankali.

"Afrah Hawan jini at your age?" cewar Halima
Banza nayi mata don bansan abinda zan iya ce mata akai ba. nidai tafiya kawai nakeyi tamkar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki.

"duk abinda zai sameki a rayuwa sai nake ganin bai kamata ki ƙwallafashi a zuciyarki irin haka ba, a shekarunki kinyi ƙarama ace irin wannan ciwon ya kamaki Afrah." Halima ta sake faɗin haka cikin alamu na nuna damuwarta a gareni.

"shikenan ubangiji bashi da ikon da zai jarrabi bawa da lalura haka kawai sai da dalili?" na jefa mata wannan tambayar cikin ƙosawa da jin maganganunta.....
"no at all Afrah. Ubangiji yana da ikon zartar da duk abinda ya tsara a rayuwar bawansa, ni wacece da zanyi tawili akan hakan?" cewar Halima
Shiru nayi ban ƙara magana ba har muka fito get muka tsaya muna neman Abin Hawa.
Bamu jima a tsaye ba muka samu ɗan'adaidaita Sahu muka shiga, Halimah ce ta sanar dashi inda ze kaimu ni dai da ido kawai nake binta na kasa magana. saboda tashin hankalin da Emran ke shirin jefa rayuwata a ciki.....

Har muka iso cikin unguwar Galadanci na kasa cewa Halimah komai, illa ƙoƙarin zaro ƴar fos ɗina daga cikin jakana da nakeyi. Kafin na kai ga fito da fos ɗin Halimah ta zaro ɗari biyar sabuwa fil ta miƙa masa ya bata canjin ɗari. Ni dai se ido kawai, Harara ta wuga min dedai lokacin data gyara zaman jakar dake goye a bayanta ta ce,"Malama irin wannan kallo haka se kace yau kika fara gani na? Kinga in zaki sakko ki sakko kina ɓata masa lokaci."

Yawun dake bakina na haɗiye daƙyar sannan na sakko jikina duk a mace, ga wani azababben ciwon kai daya ƙara tiso ni a gaba kaman kaina ze rabe gida biyu. A haka muka ƙarasa har ƙofar gidan mu

Da ƙyar na iyayin sallama sabida yanda harshe na yayi nauyi.

Amma wadda ke zaune a tsakar gida tana sauraran labaran duniya a tashar freedom ta ɗaga kai tana kallon mu, bayan ta amsa mana sallamar cikin sakin fuska. Kallo ɗaya tai min ta fahimci bana cikin yanayi me ɗaɗi, duba da yanayin idanuna waƴan da suka faɗa sosai kamar wadda na shekara ina ciwo.

Murɗe redion tayi ta kashe tareda kallon Halima ta ce,"lafiya dai nagan ku afija'atan kamar korarru, meya samu Nusaibatul'afran?" Ammah ta faɗi hakan tana tsare Halimah da kallon jiran jin Amsa daga bakinta.

"wllh Amma faɗuwa tai a makaranta muna gabda fara darasi, shine muka kaita Asbitin makaranta amma yanzu dai jikin da sauƙi sosai." Halimah ta ƙare maganar dedai lokacin da muka zauna a gefan tabarman da Amma kekai.

Cikin damuwa Ammah ta kai hannunata saman goshina aiko tajishi zafi Rau sakamakon ciwon da kaina kemin har lokacin, cikin sanyin jiki ta ce "Nusaibatu me yake damunki haka da yai sanadin faɗuwarki A makaranta? Dama bakida lafiya kuma shine kika tsiri zuwa makaranta?"

Ammah ta jera min waƴan nan tambayoyin fuskarta cikeda tarin damuwa mara misali.

Cikin sanyin jiki na ce "Ae Amma kaina ne dama yake ɗan min ciwo, ban zaci abin zeyi tsanani har haka ba." nai maganar ina kallon yanayin Ammah, wadda har lokacin take cikin damuwa.

Jin jina kai tayi sannan ta dubi Halimah cikin kulawa ta ce,"me sunan Uwata kwana biyu baki leƙo mu ba, ya makaranta dasu yayar taki?" murmushi Halimah tayi ta ce, "lafiya lau wllh, kwanaki ma tace dani ingaishe ki idan nazo."

"Allah sarki Sa'adatu matar Bokan turai, ai shekaran jiya ma da mukaje Asbitinsu shine ya duba ni, Allah sarki Shamsuddini ba dai kirki da girmama manya ba." cewar Ammah.

Shiru ne ya biyo baya don Haka na dubi Amma a fakaice na ce,"barin shiga Ciki in kwanta don wllh har yanzu kaina ciwo yake min."

Ban jira cewar Ammah ba na suri jakata nai ɗakina, ina shiga ɗakin wayata ta fara ƙara. Zama nai a bakin katifa sannan na zaro wayar ina bin screen ɗin wayar da kallo, mamaki me tsanani ne ya kamani ganin baƙuwar lamba, da kamar bazan ɗauka ba can kuma sena danna tareda kara wayar a kunnena ba tareda nayi magana ba.

Ɗaga can ɓangaren naji ance "Nusaibatul'afrah kenan, shikenan kuma daga na kora miki bayani seki yanke jiki ki faɗi? Se kace wadda nazo miki da saƙon mutuwar tsohuwar kakarki?"

Rintse idanuna nayi ƙirjina yana bugawa, se dai har lokacin na kasa firta masa komai don baƙin cikin da kalamansa suka jefa ni a ciki. Zan iya cewa tunda nake ban taɓa cin karo da hatsabibin mutum irin Emran ba.

Dariya ya sheƙe min da ita, sannan ya ce " Afrah irin wannan sauke numfashi haka tun ban haye kan Ruwan cikin ki ba? Kinga ki adana jan numfashinki zuwa gobe da misalin ƙarfe 11:00 na safe, to a lokacin ne kunnuwan Emran suke buƙatar jin fitar numfashinki, a lokacin da nake caccakar ki iya ƙarfina....."

Gabana ne ya kuma yankewa ya faɗi, jin irin maganganun banzan da yake firta min, tun kafin na kai ga yin magana ya katse wayar ya barni da baki a buɗe hangangan.... A dedai lokacin kuma Halimah ta shigo ɗakin tana bina da wani iri kallo, wanda yafi kamada na tuhuma.............

COMMENT
AND
SHARE pls

ITA CE SANADI....!Where stories live. Discover now