DA WATA A ƘASA
Na
Rahma Kabir mrsMG.Page 3.
Adam kafin ya karasa NDC an kira sallar magrib, dan haka yana isa ya tsaya a babban masallacin dake kan titi yayi parking sai ya shiga ciki da yake da alwalarsa, yana shiga aka tada sallah. Su Lawali da suke biye dashi tun daga fitowarsa gida a cikin mota suma parking din suka yi suna ganin ya shiga masallaci sai lawali yasa daya daga cikin yaransa yace yaje ya fasa tayar motar Adam domin suna so suyi amfani da wannan damar dan cika aikinsu, haka ya fita ya fasa tayar baya ya dawo ya zauna a motar suna jiran fitowarsa. Bayan sun idar ya fito ya shiga mota yana tadawa ya fara tafiya yaji tayarsa tayi faci sai ya ja guntun tsaki ya yi parking a gefen hanya ya fito ya duba, tayar baya ce tayi faci sai ya soma waige waige ko zaiga masu faci sai dai kash bai samu ko daya ba saboda dare yayi duk sun tashi, sai kawai ya shiga mota ya gyara parking ya matsa daga gefen hanya sosai ya fito ya dauko sifiya taya a bayan boot da kayan aiki sai ya soma kokarin sauya taya, sai da ya bata sama da rabin awa kafin ya sauya tayar ya gama ya shiga mota lokacin ana kiran sallar isha'i dan haka sai ya sake fita daga motar ya rufe ya wuce masallacin yayi alwala, kana ya shiga ciki liman ya tayar da sallah. Suna idarwa ya fito cikin sauri ya duba agogo sai yaga karfe takwas saura sai ya isa wajen motarsa ya shiga ya dauki wayarsa ya kira Malam Sani, bayan sun gaisa ya sanar da shi yana NDC dsn haka ya fada masa unguwarsu sai ya karaso, Sani ya sanar da shi ya fita yayi hakuri saboda tun yamma yake jiransa bai zo ba shi kuma daya ji shuru sai ya dauko ko ya fasa ne shiyasa ana yin sallar magrib ya tafi unguwan shanu gidan iyayensa, sai dai ya bari da safe yazo suyi maganar, Adam ya nuna rashin jin dadinsa dan haka sai suka yi sallama ya ajiye wayar yana daura kansa a kan sitiyarin motar, ya dauki tsawon minti goma a haka dan ya rasa me yake wa tunani saboda kansa ya kulle, haka ya sauke numfashi ya tayar da motar ya wuce, yaje wajen da zai yi youton sai ya taras wasu sunyi accident sai kawai ya wuce zuwa rigacikun dan yayi youton din a can, da yake lokacin sanyi ne motoci sun fara raguwa sai tsiraru ne a hanya, sannan kafar mutane ta dauke shiyasa yake tafiya a hankali cikin natsuwa, ya kusa kaiwa inda zai juya dayan hannun sai ya ga alamar wata mota tana bin bayansa taki wuce shi, kuma sai a lokacin ya tuna da motar tun dazu kamar shi take bi sai yaji gabansa ya soma faduwa saboda ya san da wuya CEO Munir ya rabu da shi ba tare da ya yi masa wani barazana ba, hakan yasa yake so su bar kaduna da sauri kafin ya soma dana masa tarko, ya san zai iya aikata komai akan asirinsa ya rufu, sai yanzu yake ganin fa yayi wauta daya nuna masa zai yi fito na fito da shi, dan haka tsoron daya shiga yasa shi kara wutar gudun motarsa sai ya hango suma sun kara gudu hakan ya tabbatar masa da shi suke bi, shi da zaiyi youton sai ya zarce yayi gaba, bai san ya wuce ba sai da ya iso toli gate a sannan ne ya juya dayar hannu ya cigaba da gudu suma suna biye da shi kamar zasu tashi sama, Adam a wannan lokacin niman hanyar da zai tsirar rayuwarsa kawai yake yi, dan haka yana isowa unguwar Barakallahu sai ya fada hanyar domin ya shiga mutane,saboda yana da yakinin da sun ga haka zasu rabu da shi, sai dai kash ba wasu mutane a unguwannin saboda sanyin da ake yi sai tsirarun mutane ne yake wucewa dan haka ya cigaba da gudu suma basu fasa ba, har ya isa wani kwana ya fada barakallahu GRA, titi ne mikakke da kwalta kuma duk gidajen masu hannu da shuni ba ba kowa a hanyar, Adam ya kara tsorata dan ya san da wuya ya tsira tunda ya kawo kansa unguwar da bai sani ba, haka ya cigaba da gudu har ya isa wani kwana ya cigaba da tafiya su kuma suna ganin ya kai kansa tarko, domin an rubuta wani signboard cewar ba a bin hanyar da mota saboda ana gyaran hanya, dan haka Lawali ya fito da kansa ta gefen windon motar ya ciro bindigarsa ya shiga harba masa dan ya harbi tayar motar, Adam ya kara firgita sosai ya tabbatar wannan aikin Munir ne, dan haka ya kara gudu saboda bai shirya mutuwa yanzu ba, akwai tarin abubuwan da suke a zuciyarsa wanda yake son fallasawa Yusra, sannan yana son ya dauki fansar abinda Munir yayi masa, sai dai da alamu lokaci ya kure masa, yana cikin tunanin yadda zai tsira motarsa ta ci karo da wani katon dutse wanda yasa ya wultsilo ya bigi gilashin gaban motar ya fashe ya fito kamar an fizgoshi ya wulwula zuwa wani kwazazzabo mai tsananin zurfi, tun kafin ya kai kasan wajen numfashinsa ya bar jikinsa salati kawai yake yi domin ya san tashi ta kare. Suna karasowa suka yi parking ne sa da motarsa suka iso wajen da kafa sai suka leka cikin kwazazzabon suka ga akwai duhuwa duk da sun haska basu ga karshen ramin ba, ga bishiyoyi da ganye da suka yi rassa a ciki sannan suka hango wani katon teku a gaban kwazazzabon hakan ya tabbatar musu da Adam ya cika musu aikinsu ba tare da sun kaddamar masa da kansu ba, dan haka suka dawo wajen motar suka bincika ciki basu samu komai ba sai wayarsa da takardun motar, lawali ya kira Yunus ya sanar da shi halin da ake ciki, yunus yace cikin jin dadi.
YOU ARE READING
DA WATA A ƘASA
General FictionAkwai son zuciya me sanya mutum a tarkon nadama, zalunci mai kunshe da keta, zawarci mai sanya kunci, mutuwa mai dauke da yankan kauna. Nadama mai sanya kukan zuci gaba daya duk a cikin labarin DA WATA A ƘASA.