7

54 6 2
                                    

DA WATA A ƘASA

Na
Rahma Kabir mrsMG.

Page 7.

Washe gari da sassafe motar kwashe kaya tazo, Hadiza itace kan gaba wajen jera kaya sai da ta ware nasu kafin aka saka na Yusra daga gafe, ta kalli baba tana cewa.

Baba tunda ku zaku bi motar kaya to zaku rigamu kaiwa, ga kayan Yusra na ware mata sai kasa su Fahad su shigar mata da shi gidansu, sauran kuma su Habu su sashi a nan gida.

To kawai yace mata kana suka shiga gaban mota, Baba da Abubakar sai Fahad kanin Yusra suka hau gaban motar kwashe kaya duk da ya musu kadan haka suka tafi a maneji. Sun jima da tafiya kafin motar da zai dauki su Hadiza tazo, Yusra tayi sallama da su Maman fati suka yi kukan rabuwa tare da kara yiwa Adam addua, suka ce in an kwana biyu zasu kawo musu ziyara, a haka suka rakosu har mota, Hadiza itace a gaba tare da Najeeb da Hanna saboda tana da dan kiba, sai Mama, Inna, Tabawa da Yusra a baya, me gadi ya fito yayi mata sallama harda hawayensa haka me motar ya kunna ya jasu su Hamis suna daga musu hannu cike da rashin walwala, sai da motar tayi nisa kafin suka koma gida. Su kuma suka kama hanyar kano.

Tafiyarsu ba jimawa sai ga Yunus yazo gidan dan yaji yaushe zasu koma kano saboda Munir ya shirya musu kayan abinci da zasu tafi da shi, sai ya samu labarin sun wuce a bakin me gadi, ya ciza yatsa sai ya tafi kawai, yaso ace su tafi da kayan abinci ta yadda zasu rika ganin kirkinsu sosai har abada ba zasu zargi komai ba amma duk da haka yasan hidimar da suka yi musu ma kawai ya isa ya tsarkake musu niyyarsu. Ya isa gidan Munir ya same shi a falonsa ya koro masa bayani, Munir ya nuna rashin jin dadinsa yana cewa.

Amma banji dadi ba naso na gana da Yusra kafin su tafi, saboda na bata damar aiki a companynmu in zata yi, in kuma ba zata yi ba su kawo wani dan uwanta ko dan uwan Adam ya samu gurbi a nan, amma sai in suna da kwalin diploma ko sama da haka.

Kuma shawara ce me kyau amma kuma yanzu ya za ayi a sanar da ita.

Ka samo mana numbern wayarta nasan ba zai yi wahalar samu ba.

Gaskiya ne oga, yanzu zan koma na amso number dinta tunda mutanen gidansu suna nan.

A haka suka rabu, Yunus ya koma gidan ya amsa number yusra a hanun maman fati kana ya wuce ya turawa Munir number din ta text massage.

******

Katsina.

Da baba ya dawo Habibu ya sanar da shi duk abinda ya faru a tsakaninsa da Adam, Baba ya fahimci akwai shafin jinnu a rashin maganarsa dan haka sai ya daura shi a kan magani, domin yana da sani sosai game da addini dama abinda ya shafi halittun ruwa. Fitsarin da Adam din yayi baba shi ne ya gyara masa jiki, ya sanya leda a kan tabarma ya daura shinfida akai sai ya maida shi nan ya kwantar, sannan yasa Habibu ya fitar da kayan daya bata, ya cewa Adam sai yayi hakuri ga abincin da zai rika ci saboda mara nauyi ake so yaci saboda kar ya rika yawan bayan gida. Adam shi dai godiya ya rika yi masa da hannu har da hawayensa, yana mamakin yadda suka rikeshi kamar ɗansu, sai ɗawainiya da shi suke kuma basu numa gazawarsu ba ko kadan, fata yake Allah ya tashi kafaɗunsa ya saka musu da mafificiyar alkhairi duk da yasan bazai taba biyansu abinda suka yi masa ba.

Haka ya cigaba da jinya. A mako guda duk ya rame sai yayi fari sosai saboda baya cin abinci me nauyi, kuma akwai alamar sauki a kafarsa sai dai har lokacin maganarsa bai bude ba, duk ya kosa ya warke ya dawo ga iyalensa dan gaba daya hankalinsa ya koma wajensu.

******

Kano.

Sun isa lafiya kaya an sauke su duk an shiga dasu ciki, Yusar ita da Umma suka shiga gidansu su kuma su inna suka shiga nasu, sun samu Hauwa ta zo da yake ta san da dawowarsu ita ce ta shirya musu abinci, sai da suka koshi kafin suka samu damar tattaunawa, bayan sunyi addu'a ga Adam, Tabawa ta yi sallama da su ta wuce gidanta, duk suna zaune a tsakar gida Hauwa ta kalli Hadiza tana cewa.

DA WATA A ƘASAWhere stories live. Discover now