DA WATA A ƘASA
Na
Rahma Kabir mrsMG.Page 8.
Bayan sallar la'asar Hassana kawar Yusra ta zo gidan yi mata gaisuwa. Ta kasance kawarta tun na yarinta, da a unguwarsu Yusra iyayenta suke da zama sai daga baya mahaifinta ya samu gidan kansa a wata unguwar sai suka koma can suka bar nan gidan haya, tare suka yi rayuwar kuruciya har suka kammala makarantar secondary kuma Hassana ita ce tayi mata babbar kawa lokacin bikinta, Yusra ta rigata aure da shekara uku kafin tayi aure a nan kano, yamzu yaranta uku. Ta shiga gidan da sallama Umma da take tsakar gida ta amsa ta, Hassana ta tsuguna a inda umma ke wanki ta gaisheta tare da yi mata gaisuwa kana ta mike ta shiga dakin umma ta samu Yusra kan dadduma tana jan charbi ta idar da salla, cike da walwala Yusra ta karbeta ta zauna suka gaisa kana ta yi mata gaisuwa da bata hakuri akan rashin zuwa kaduna da bata samu tazo ba, saboda yaronta karamin bai da lafiya, Yusra ta fahimceta saboda ta san amintarsu ba baya ba inda babu uzurin rashin lafiya tasan da ta zo, daga haka suka shiga hirar rayuwa har suka zo kan zancen rabon gado, Yusra ta kwashe labarin yadda yan uwan Adam suka yi mata, lokacin Umma ta shigo taji hirar da suke yi sai ta cewa Hassana.
Sai ki bawa kawarki shawara ta yi hakuri ta kauda ido akan abinda suke yi mata karta biye su, dan nayi mata magana naga bata ji sai kokari take yi ta numa musu karfinta.
To Umma sai ta barsu ta zuba musu ido, ai wannan rainin hankali ne, dama wannan shegiyar Hadizan ido a naira ina zata barki kisha ruwa, nasan duk ita ta karantawa su baban wannan rashin imanin da suke nunawa, kamar suna jira ya mutu, ko kansu ne aka fara talauci.
Au zugata za kiyi kenan.
Ba zugi bane Umma amma dai lamarin nasu ne da haushi wlh, sai dai kuma babu abinda ya kai hakuri dadi, dan duk wanda aka cuta shine ake bawa hakuri, ki rabu da lamarinsu kiyi addu'a Allah ya kawo miki hanyar da zaki tallafi yaranki, duk abinda suka yi kansu suka yiwa, kuma arzikin bawa yana goshinsa.
Yauwa yafi dai ki fada mata tayi hakurin, dan hakuri da rashinsa tazararsu kadan ne, wata rana sai labari.
Hakane Umma, Allah dai ya jikan Adam ya bada hakurin rashi.
Cewar Hassana, suka amsa da Amin sai Umma ta fita bayan ta dauki kayan data zo dauka, Hassana ta cigaba da bata hakuri har zuwa gabda magrib, ta bude jaka ta ciro kudi dubu biyar ta ajiye a gaban Yusra tana cewa.
Kawata ba yawa ki siyawa yarana sabulu, insha Allah nan da kwana biyu zan dawo Allah ya jikansa.
Yusra ta amsa da amin kana tayi mata godiya sai ta wuce, da Umma ta shigo ta fada mata kudin da Hassana ta bata tayi mata Allah ya sanya alkhairi ta ce ta adana saboda tsaron lalura.
******
Bayan kwana biyu.
Zaman kano ya fara bin jikinsu, Ysura ta tabbatar da ta dawo gida ba ranar barinta tunda ta rasa bago abin jinginawarta, Allah ne gatanta sai kuma Adam shine walwalarta da jin dadinta, sai dai kash Allah ya rabasu ba tare da sun tsufa tare ba, ga yaransu da take tunani yadda rayuwarsu zata kare a maraici. Da dare Baban Adam ya aiko Yusra ta je saboda za suyi mata magana akan gadonsu, haka ta shirya ta tafi ta same su a falon Inna shi da ita sai Abubakar kanin Adam me bi masa, ta gaishe su suka kara yiwa juna jajen rashin Adam daga bisani suka daura da cewa.
Na kira ki ne kan batun gadonku, to na samu wani malami nayi masa bayanin komai akan ni da Innarku mun yafe kudin da suke hannu na na gadonku sai dai mashin dinsa roba roba na dauka, sai ita kuma inna kayan kitchen data dauka tace sun isheta, to sai malamin yace to ai hakan yayi gado ya raba kansa kudin sai ya zama naki ke da yara, to shine na kiraki na fada miki yadda muka yanke akan kudin, tunda yaran nan kanana ne za muyi kasuwanci da kudin mu juya su, zuwa nan da shekara guda an samu riba sai na hada kudin gaba daya na siya muku karamin gida, sai mu zuba yan haya ana karban kudi ana yiwa yaran amfani da shi, kafin nan gaba mu san yadda zamu raba muku lokacin sun girma.
YOU ARE READING
DA WATA A ƘASA
Ficción GeneralAkwai son zuciya me sanya mutum a tarkon nadama, zalunci mai kunshe da keta, zawarci mai sanya kunci, mutuwa mai dauke da yankan kauna. Nadama mai sanya kukan zuci gaba daya duk a cikin labarin DA WATA A ƘASA.