1

285 20 7
                                    

DA WATA A ƘASA

Na
Rahma Kabir mrsMG.

Page 1.

*Gargad'i*
_Ban yarda ayi afmani da wani b'angare na wannan labarin ba ko kuma satar fasaha, ko a daurafin shi a wata kafa ba tare da izini na ba, dan Allah a kiyaye_

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

KADUNA.
Bypass, Express.

Pure oil Nigerian Limited Campany ne na man gyada wanda yake a tsakanin mahuta da hayin dan mani kan titin express bypass. Babban Campany ne na mataccen mangyada da manja da babu kamarsa a fadin jihar kaduna, domin ya tara manyan masana masu ilimi da gogewa a fannin mai, dan haka shiyasa babu inda baya zagawa a nahiyar kasar dama kasashen dake kewayen nigeria, akwai ma'aikata sama da mutane dari ko wanne da bangaren da yake aiki, akwai waɗanda suke fannin ofisoshi akwai kuma waɗanda suke bangaren matatan man, akwai masu kula da ingina, direbobi da suke kaiwa dilolin 'yan kasuwa, masu tallatawa ga kasuwanni da kafar sada zumunta dama gidajen tv da radio, zuwa securities masu gadi da dai sauran ayyuka da suka shafi kamfanin. Akwai matsakaicin masallaci a ciki duba da musulmai sunfi yawa, sannan akwai dan clinic an tanade shi domin masara lafiya don ba da taimakon gaggawa kafin a kaiga babban asibiti.

Adam Umar shi ne CFO (chief financial officer) wanda a sati hudu da suka gabata ya samu wannan mukami lokacin da aka yi taron shagalin cikar campanyn shekara goma sha biyu da kafuwa, ya samu wannan matsayin ne bisa jajircewa akan aiki da rikon amana, shekararsa biyar da zuwansa ma'aikatar ya fara da marketer ne, a hankali yazo matakin masu kula da fitar da kaya, rikon amanansa yasa aka kaishi matakin acounter daga bisani ya zo wannan matsayi na CFO, sai dai duk da samuwar wannan cigaba daya tsinci kansa a ciki gaba daya baya farin ciki domin kuwa zuciyarsa yana cike da kuncin damuwa wanda bai san ranar fitarsa ba, gaba daya ahalinsa babu wanda bai yi farin ciki da wannan nasara daya samu ba, haka ma matarsa Yusra tayi murnar da baya misaltuwa domin a ganinta mijinta ya kai matakin da zasu samu karuwar arziki fa jin dadin duniya, yaransu zasu samu ingantacciyar rayuwa wanda zai zame musu gata da duk irin yadda masu hannu da shuni suke yiwa yaransu, sai dai a bangaren Adam ba haka bane sai haushinsu da yake ji yadda suke nuna masa murna kamar wanda aka ce an mallakawa companyn, da farko yayi murna sosai da mukamin da aka kara masa amma daga baya ya zame masa abin bakin ciki. Yana zaune a office dinsa ya rafka tagumi sai ya sauke ajiyar zuciya ya ja guntun tsaki ya gyara zamansa tare da jingina bayansa a kujera ya rufe idonsa yana tuno wasu abubuwa da suka shude, a hanlali hawaye ya soma zubowa daga idanunsa yana sauka a kuncinsa, ya bude idanu ya shafi kuncinsa yaji dumi da danshin hawaye, wanda kwanaki da dama yake burin ya fiddasu ko zai samu sassaucin radadi da zugin da zuciyarsa ke yi masa, hakan ya bashi damar cigaba da zubar hawaye ya dago ya dafa table da hannunsa ya soma kuka sosai kamar wanda zai shide, ya dade yana jiran ranar da zai yi kuka irin haka amma bai samu ba sai yau, dan haka yayi me isarsa tare da cizon yatsa yana kaico, jikinsa har wani kakkarwa yake yi, jijiyoyin kansa duk suka tashi tare da gashin jikinsa, duk sanyin dake ratsa cikin office dinsa amma zafi yake ji wanda hakan ya samu ne daga zafin da zuciyarsa ke ciki. Buga kofarsa da aka shiga yi shine ya sashi gimtse sasshekar kukansa ya yi saurin mikewa ya share hawayensa ya dauko bakin tabarau ya makala a idonsa, domin ya rufe jan da idanunsa suka yi saboda kukan da yayi, sai ya yi gyaran murya yace.

Yes a shigo.

Sai ya koma ya zauna yana dago wani file kamar yana dubawa, wanda ya buga kofar ya shigo ya tsaya yana cewa.

Yallabai sannu da aiki, dama oga Jibril ma'aji shi ne yace na kawo maka wannan file din ka sanya hannu akai, na inginar da aka yi oder ne an kawo su kuma yace ka je ka duba ka gani in sun cika adadin kayan da akayi oder.

Ok ba bamuwa inna sanya hannu zan kira a zo a amsa file din, bari na je na fara duba kayan.

Ilyas yace to kana ya fita, Adam ya sauke gauron numfashi kafin ya mike ya fita zuwa bangaren inda ake tace mai domin duba sabbin injinan da aka kawo, ya rufe office dinsa da key ya wuce cikin sauri domin yana so ya dawo ya wuce masallacin juma'a dan ya duba agogo karfe goma sha daya da minti arba'in. Yana isa gate din shiga wajen ya hadu da Mu'azu shugaban bangaren suka gaisa kana Mu'az yace.

DA WATA A ƘASAWhere stories live. Discover now