12

91 10 0
                                    

DA WATA A ƘASA

Na
Rahma Kabir mrsMG.

Page 12.

Last freepage.

Amadu yana shiga gida ya zauna a tsakar gida kan wani babban dutse da baba ke yin alwala akai, ya shiga kwalawa Inna kira sai dai bata amsa ba tana bandaki, Hadiza ce ta fito daga daki tana mustsike ido alamar shi ne ya tasheta daga barci.

Amadu ya aka yi ne kake kiran inna haka sai ka ce kazo amsar bashi.

Kalla wannan kiga ki gani, sai ki tabbatar da dalilin da yasa nake kiranta haka.

Hadiza ta matso ta amsa ta kafe poster din da ido, tana ganin yusra da hotonta ya fito sosai dan a ciki nata yafi girma saboda ita ce babbar jarumar, sai ta shiga cewa da karfi.

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un mun shiga tara, Inna! Inna! Ki fito daga bayin nan ki zo kiga wani masifa.

Ba arziki inna ta fito da sauri har tana cin tuntube ta tsaya kusa da hadiza tana cewa.

Irin wannan kira ai sai ya jefa mutum a mai ko rami saboda firgici. Me ke faruwa ne?

Inna waye inba yusra ba da take niman mu da masifa, wai kinga film ta shiga ashe.

Ta fada tana mika mata poster din, inna ta amsa tana gani ta soma rafka salati tana tafa hannu tace.

Wannan yarinya ta zame mana masifa haka kawai ta ja a zagemu, ta rasa abinda da zata saka mana da shi sai film, gaskiya ba zai yuwu ba dole ne mu je mu ja mata danga saboda mutuncinmu dana yaranta, wlh ina dana sani da amincewa da auren nan, da Adam bai aureta ba da duk haka bai faru ba, amma dole ne mu taka mata burki ba zata bata mana suna ba.

Ya dai kamata kuyi wani abu dan wlh har abokaina sun fara yada mini magana, shiyasa na garzawo da wuri na fada muku ku dauki mataki, in banda iskanci yaushe ta gama takaba da zata fara film kamar dama tana jira ya mutu.

Cewar Amadu ransa a bace, hadiza ta kade baki tana cewa.

Kawai tana niman hanyar yin karuwanci ne shiyasa ta shiga film, banda iskanci me 'yan matan film din suke yi, yara gasu a zube uwa ba kwaba kaka ba tsanani duk sun gagari iyayensu. Wlh inna a wannan karan sai inda karfina ya kare dan ba zata jawo mana zagi ba.

Dauko min hijab dina yanzu ba sai anjima ba mu je mu diran mata daga ita har uwarta mu wanke su soso da salulu, in babanku ya dawo yaji labari.

Hadiza ta shiga daki da sauri ta dauko hijab din inna ita kuma ta dauki gyalenta ta fito,  suka saka suka fito Amadu yana biye dasu a baya suka shiga gidansu yusra sun samu Umma ce a Kitchen Yusra kuwa tana daki tana charting a wayarta, sallamarsu ya katseta ta fito dai dai lokacin itama Umma ta fito daga kitchen suka tsaya cirko cirko, Hadiza ta wurga musu poster din tana cewa.

Yusra ashe kin fada harkan karuwanci daga mutuwar mijinki saboda kina jira dama ya mutu, to wlh ba zai yuwu ki jawo mana zagi ba, da ace bamu hada zuri'a dake ba da sai muce Allah ya bada sa'a amma wlh saboda su Najeeb ba zamu yarka ki bata mana suna ba dan haka ki sake shawara dole ne ki fita daga wannan harka da kika fara.

Banga uban da ya isa ya hanani ba wlh, kuma ku fice mana daga gida tun kafin nayi muku wulakanci.

Cewar yusra cikin fushi, Umma ta tare da ta cewa.

Ai da kinyi shuru da bakinki ni kadai na ishe su, wlh mamaki kuke bani saboda sam ba kuda kunya, amma banda haka har zaku iya zuwa gidan nan kuna fada mana son ranku. To film ni ce na tura ta ta shiga dan haka ba ita za ku yiwa magana ba ni ya dace ku turtse, kuma ku sani yanzu tasa kafa ba fashi, in da abinda kuka isa kuyi sai mu gani.

Aiko wlh baku isa ba dole ne ta bar film dan ba zata ɓata mana suna ba,  ko kuma ku bamu yara su dawo hannunmu dan kar ta bata musu tarbiyya. 

Cewar inna, Umma kuwa ta katseta da cewa.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 23, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

DA WATA A ƘASAWhere stories live. Discover now