NYAKU
(K'udan Zuma )Na Sadeeey, Yar Gatan Royal Star....
P. 1
................ "Muraydah sau tari abunda mukeso ba lallai shi ke zama alkhairi a garemu ba, kiyi hakuri kibi umarnin iyayen ki, ni nasan in sha Allah bazasu za6a miki abunda zai cuceki ba. Abunda wata matsashiyar budurwa take fadawa yar uwarta kenan, sai dai dayar wacce aka kira da Muraydah naga ko daga kai batayi ba ballen tana ta tanka, illa danna wayar da takeyi kana lokaci zuwa lokaci tana kara wayar a kunen ta, Wanda ke nuna tamkar bata samu Wanda take nema ba, sai dan gajeren tsakin da take ja, kana tana fadin "Hayat ka amsa wayar mana"
Ba tare data damu da rashin maganar natan ba, taci gaba da fadin
"Dan Allah karki sabawa iyayenki akan Dana miji, me yasa zaki dauki halayen da ba naki ba ki daurawa kanki?" Ni Wallahi haka kawai naji kwatakwata Saleem bai min ba ba, haka kawai naji yaron bai kwanta min a rain va, bansan ke kuma me yasa kika nace masa ba, ki San sanar sa kuwa? Yaron da ko lokacin ki bashi dashi amma ke kin tsaya kina wahalar da kanki,? Gaki da masoya birjik amma ki tsaya akan wani Saleem, ai da Saleem kam gwara Al...........
"dakata ya isheni haka nan, Rukka! Cewar Muraydah cikin zallan fushi, kana taci gaba da fadin
" Ai bansan nufinki ba kenan da tun farko kin sanar kinga da nasan abun yi, haka kawai kin ajiyeni kina karanta mun wasikar jaki, Wallahi kin bani mamaki, ban dauka zan sameki da wannan halin va, na daukeki cikin masoyana masu son abunda nake so ashe ba haka bane.Na kawo karshen friendship dina dake daga yau, bana son Wanda bai son Saleem haka ma Wanda bai son zama na dashi, ke kina daya daga ciki daga yau karki kara Kiran koda suna ne, nagode da abunda kika saka min dashi.
" Ki fita!
Ta fada a mugun tsawace tana kallon Rukka wacce banda hawaye babu abunda ke zuba a kan fuskarta."cikin kuka tace" Muray ki saurare ni please, baki fahimceni ba,
"enough! Just go out please!
" fine, zan tafi amma ki sani, Wallahi zakiyi Dana sanin zama da Saleem, zakiyi Dana sanin rabuwa mu akan Saleem, kai hatta saninsa sai kinyi Dana sani,
Na gaya miki Wanda ya kamata kibi, duk da baki San waye ne shi ba yakama ki bashi dama sanin shi, amma kika ki, shi Ke nan.
Tana gama fadan haka ta fita fita a yayin da Muray ke cewa "bazan yi ba, Don bazan yarda da gaibu ba akan zahiri va, mutumun da bansan wane ne shi ba, tana fadan haka tabi maganar da tsaki abunta kana taci gaba da kwanciya tana danna waya........
Bai wuce minti biyu da fitar Rukka ba, Ammy ta Bude kofar ta shigo.
Kallon muray tayi kaman yadda itama Muray take kallon ta, kana tace "Karan me nakeji haka Muraydah, sannan meta hadaki da Rukayya naga ta fita kaman tana hawaye?
Ba.....Ba...bu.. komai fa Ammy, sannan rukka Kuma waya akayi mata, Babu komai ta karasa maganar a Dan duburce alamun rashin gaskiya.
Kallon ta Ammy tayi kana ta Maida kofar ta rufe tana Mai fadin Allah ya kyauta.
Da dare kaman yadda aka saba wuraren 10pm ba taji Karan wayan ta ba kaman yadda aka sabar mata da Hakan ba, domin yanxu tsawon 27 weeks wato shekara biyu da wata uku kenan na tura mata text kullum safe Rana dare sau uku a Rana, sai dai bata taba bincikar waye bane? Infact ko calling numbern bata taba Yi ba, sannan tsawon wannan shekarun ba'a taba fashi ko sau daya ba sai yau,
Yau din ma ba wai ta damu bane a cewar ta, taso share abun sai dai a kasar renta take Jin kewan night messages din wanda take kokarin dannewa......
Sai dai masu iya magana sukace ita zuciya tana son mai kyauta ta mata ko yayana ne.
Wannan tunanin ta kwanta bacci barawo ya dauketa bayan ta Kara Kiran no din saleem kusan sau biyu Amma baiyi picking ba.
YOU ARE READING
Kudan Zuma
RandomWannan littafi labarin wata yarinya ne akan wata yarinya mai suna Muraydah, wacce ta bijirewa umarnin iyayen ta akan auren saurayin da iyayen basu da tarbiyarsa ba, ita kuma ta nace har takai baban ta ya cire yayi furucin cire hannu a kanta, Wanda d...