P.2
............. Shigowanta cikin gidan kenan, amma daga yanayin tafiyarta zaka gane ba'a dai-dai take ba, domin kallon d'aya za'a mata a gane tana cikin wani irin yanayi mara dad' ko kad'an, don hatta idonta bata Bude shi sosai bayan rawan da naman jikin ta yakeyi yana tsuma.
Kallon ta Umma tayi lokacin da take k'ok'arin zama a gefenta akan k'aramar taburman da take zaune. "yaya dai Rukayyatu? Cewar Umma,
Numfashi ta sauk'e kana ta ce " Ba komai Umma, fadar Rukka a dai - dai lokacin da sabbin hawaye suka sake zubowa kan kuncin ta,
" ya zakice min babu bayan gashi kina kuka? Umma ta fada cikin nuna mamakin ta ga halin da Ita Rukka ke ciki.Jikin Umma ta fad'a kana ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, kuka mai zafi, kukan dake nuna zallan kuncin da zuciyarta ke ciki, kukan dake nuna tsagwaran bak'in cikin da Muraydah ta kunsa mata, kukan dake nuna halin damuwar da zuciyarta ke ciki, kukan dake nuna zallan tsagwaran takaici, damuwa, kunci, da nadaman da gangar jiki da zuciyarta je ciki, kukan, domin ba Iya haushi da. Bakin ciki da takaicin muray takeji ba, hatta na nata da kanta tana ji, yadda ta bari zuciyarta tayi mummunar sabo da Muraydah, yadda ta bari gidansu suka dauketa yar uwa ba wai kawarta da anguwa ta hada su zama ba......
Umma dai banda shafa bayan ta babu abunda take yi. Sai data gama kukan kafin ta zayyana wa Umma abunda ya faru. Ba tare da Jan maganar sosai ba Umma ta bata hak'uri tare da bata shawarwari......
Kana ta rufe da fadin, "ya kamata kiyi wa Muraydah uzuri ni nasan ba halin ta bane, kawai dai a ganina ta hadu da shu'umin namiji ne Wanda idan ta aureshi auren zai Iya zama mata makullin da zai bude mata makarantar duniya, ko nace shafin 'Kaddaranta, domin yanzu kam ba zata fahimci komai ba, ki mata addu' a a matsayinki na kawarta da kika San halin ta, daga haka. Suka rufe shafin.......
*****
Washe gari kusan bayan azahar ra samu number din Saleem nan ma sai data kirashi kusan sau uku kafin ta samu ta dauka.
Ba tare data damu da Rashin picking din wayan ba, ballen tana dan complain irin na yan mata, kawai ta hau zuba tana gaya masa yadda tayi kewarsa da kuma yadda ta gagara bacci saboda rashin Jin muryansa da batayi ba.
Illa "hmm," da "um ba bu abunda yake cewa daga karshe yace mata bye yayi bako.
Bata wani damu ba tace ok bye.
Wannan itace soyayyar Muraydah da Sameer wanda Rukayya taso ta fahimtar da ita Amma ta gagara ji.
*Wace ce Muraydatu???*
Sunan ta Aysha Abubakar Mu'azu.
'Ya ce daya tilo tsoka Daya a cikin miya wajen iyayen ta, Abhie da Kuma Ammy.Iyayen ta suna matukar kaunarta kasancewar ita kadai suka haifa, saboda wabin da Ammy ta dingayi, Wanda daga karshe Allah ya ajiye musu Muraydatu, suna Sonta sosai, musamman Abihie saboda sunan mahaifiyarsa da taci.
Sai dai duk irin son da suke mata bai Hana su mata tarbiya da Kuma wadatata da ilimi both Arabic Dana boko
Sun wada tata da ko wanne ilimi sa bo da inganta gobe ta.....
Muraydah tana da hankali kwarai da gaske, sai dai illan ta daya shine kafiya, tana da kafiya akan Abunda ta saka a gaba wannan halin nata shine abunda yake bawa ammy haushi a game da wannan hali nata, domin kuwa duk abunda ta daurawa kanta tana so ko zatayi babu mai tankwarata....
Wannan hali nata shiya bawa shaid'an daman anfani da ita ata ko wace tsiga......
Mahaifinta yana da Kudi dai dai gwargwado haka kuma ya kai shekara tsufa Don har yayi ritaya, amma yana da kafanoni a kalla guda biyar masu sarrafa mabanbanta abubuwa, sai dai komai yakeyi yana ji don Muraydah, yana mata wani irin tsaftaccen so Wanda babu algus aciki, haka kuma komai yakeyi yanayi ne don ita, domin tunda yayi ritaya ya kasa dukiyarasa gida uku, daya nata daya akai gidan marayu da mabukata a yayin da daya kuma yake na gado, dama tun kafin ya yi hakan yawancin abubuwansa sunan ta ne akai. ba tun yau ba ammy ke gwada masa illa dake tattare da wannan son, sai dai gani yake tamkar bata son Muraydah din ne, ko yanayi mata hali irin na fulani, wannan yasa wassu lokutan take fita hakan su gaba daya.....
Tun batayi 19 ba ya mallaka mata motar ta nata na kanta tare da bata daman driving da kanta, sabida lokacin ta kai shiga jami'a tana ganin ta girma, ba tare da bata lokaci ba kuwa ya yarda ya siya mata dream car din ta wato Camry XLE, Duk ba irin kokarin da Ammy batayi ba wajen ganin ta ganar dashi amma inaa yayi nisa.
Muraydah yarinya ce mai ji da kanta da ji da gata da son da Mahaifinta yake mata, uwa uba irin cikekken kyawun da Allah ya zuba mata na asalin jafunawan fulani, kyan daya taka muhimmiyar rawa wajen kassara rayuwarta, son daya bude mata kofar kaddara, kyan daya zame mata tamkar masifa sai bata gane hakan ba, maybe sai zuwa gaba, idan taci Uwar wahala...
*****
*Haduwar su*Wata rana da yammacin ranar lahadi ta je SAN-HUSSEIN shopping kaman yadda takanyi a wassu lokutan, a nan mosomumin kaddaran ya fara, domin kuwa a nan Allah ya hadata da *Six stars* inda a nan biyu suka kamu da son ta, a lokaci daya, sai dai mabanbantan so, daya yana mata zallan tsagwaran so Wanda babu digon ha'inci ko karya a ciki haka kuma bai kamu da son ta Don kyawun da Allah ya mata ba, kuma bai kamu da son ta Don kyawun dirin ta ba, illa kawai so ne daga min in dillinger, so ne asali Wanda babu digon algus.
A yayin da daya Kuma yake mata opposite na dayan, domin shi Abu daya ya jashi akan hakan, zallan kyawun daya gani a tattare da ita, yasa kawai yaji yana sonta Kuma Yana son ya aure ta.
Idan Yace so bawai Yana nufin asalin so bane, a'a domin shi Babu so na burgewa a tsakanin shi da mace, don baiga me zaiyi da ita ba, kawaii dai yasan idan ya ajiye irin wannan ya kece raini duk cikin 6 stars 🌟. Besides dama wa su Ayyub zai ajiyewa domin duk cikin su shi ne kadai baya mu'amala da mata, idan aka cire Haydar da baya yi duka biyu, Amma sauran sunayin duka biyu, sai shi kadai Wanda baya mu'amala da mata sai maza Yan uwansa.
Saleem shi ya fara mata magana, Kuma ya karbi number din ta, sun Kai kusani 2years a yanxu da haduwa zuwa wannan lokacin Kuma ya gama tabbatar data kamu da son shi, daya Gama tabbatar da hakan sai kawai ya watsar da ita, ya barta da zallan wahalan dakon sonsa......
Domin a farko shi ken Neman ta yake Jin Yaya take kira sai 5 a rana, wato ita zuciya tana da laushi musamman zuciyar mace, tun tana share wa har ta bari ta bude masa zuciyar sa.
Haydar kuwa ganin abokin shi ya fara sai yy niyyar hakura, sai dai furucin sa ne yasashi Jin tausayin ta, a gefe daya kuwa son ta ya fara ginuwa a cikin zuciyar sa, sai kawai bi shawarar zuciyar sa ya fara bibiyarta ta hanyar sanya ido ga Kuma kawar ta da yayi anfani da ita wato Rukka.
Rukka tayi kokarin ainun wajen son nunawa Muray ba son ta Saleem yake ba amma taki ji, daga karshe har hakan ya kaisu ga fada rabuwa ta wanxu......
YOU ARE READING
Kudan Zuma
Ngẫu nhiênWannan littafi labarin wata yarinya ne akan wata yarinya mai suna Muraydah, wacce ta bijirewa umarnin iyayen ta akan auren saurayin da iyayen basu da tarbiyarsa ba, ita kuma ta nace har takai baban ta ya cire yayi furucin cire hannu a kanta, Wanda d...