10

0 0 0
                                    

*NYAKU*
_(K'udan Zuma)_

*Na*

_Sadeeey ce, Yar Gatan Royal Star_

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*


.......𝐑𝐚𝐲𝐮𝐰𝐚 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐬, 𝐁𝐚𝐩𝐩𝐚𝐡 𝐤𝐚𝐢 𝐝𝐢𝐧 𝐣𝐢𝐠𝐨 𝐧𝐞, 𝐤𝐚𝐢 𝐝𝐢𝐧 𝐛𝐚𝐧𝐠𝐨 𝐧𝐞, 𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐲𝐚𝐲𝐚𝐧𝐬𝐚 𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐚𝐫𝐚𝐲𝐮, 𝐰𝐚𝐧𝐝𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐚𝐢𝐤𝐢 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐦𝐚𝐫𝐬𝐚, 𝐤𝐮𝐝𝐢𝐧𝐬𝐚 𝐥𝐨𝐤𝐚𝐜𝐢𝐧𝐬𝐚 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐢𝐤𝐨𝐧𝐬𝐚 𝐰𝐚𝐣𝐞𝐧 𝐭𝐚𝐢𝐦𝐤𝐨𝐧 𝐚𝐥'𝐮𝐦𝐦𝐚, 𝐰𝐚𝐧𝐝𝐚 𝐲𝐚 𝐫𝐚𝐲𝐚 𝐫𝐚𝐲𝐮𝐰𝐚𝐫 𝐬𝐚 𝐜𝐢𝐤𝐢𝐧 𝐛𝐚𝐮𝐭𝐚𝐫 𝐀𝐥𝐥𝐚𝐡, 𝐦𝐮𝐭𝐮𝐦 𝐦𝐚𝐢 𝐭𝐚𝐰𝐚𝐤𝐤𝐚𝐥𝐢 𝐝𝐚 𝐠𝐨𝐝𝐞𝐰𝐚 𝐀𝐥𝐥𝐚𝐡 𝐰𝐚𝐧𝐝𝐚 𝐛𝐚𝐲𝐚 𝐦𝐢𝐭𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐤𝐨𝐦𝐚𝐢, 𝐫𝐚𝐲𝐮𝐰𝐚 𝐭𝐚𝐲𝐢 𝐤𝐲𝐚𝐮 𝐭𝐬𝐮𝐟𝐚 𝐭𝐚𝐲𝐢 𝐤𝐲𝐚𝐮, 𝐤𝐚𝐫𝐬𝐡𝐞 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐤𝐲𝐚𝐮 𝐚𝐥𝐫𝐳𝐢𝐤𝐢 𝐲𝐚𝐲𝐢, 𝐚𝐥𝐥𝐚𝐡 𝐲𝐚 𝐣𝐢𝐤𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐝𝐚 𝐫𝐚𝐡𝐚𝐦𝐚, 𝐮𝐛𝐚𝐧𝐠𝐢𝐣𝐢 𝐲𝐚𝐬𝐚 𝐦𝐮𝐭𝐮𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐳𝐚𝐦𝐚 𝐡𝐮𝐭𝐮 𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐞𝐤𝐚, 𝐚𝐥𝐥𝐚𝐡 𝐲𝐚𝐬𝐚 𝐢𝐲𝐚 𝐰𝐚𝐡𝐚𝐥𝐚𝐫 𝐝𝐚𝐤𝐚 𝐬𝐡𝐚 𝐤𝐞𝐧𝐚𝐧 𝐚 𝐠𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐝𝐮𝐧𝐢𝐲𝐚, 𝐮𝐛𝐚𝐧𝐠𝐢𝐣𝐢 𝐲𝐚 𝐲𝐚𝐥𝐰𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐤𝐚 𝐤𝐚𝐛𝐚𝐫𝐢𝐧𝐤𝐚, 𝐀𝐥𝐥𝐚𝐡 𝐲𝐚 𝐫𝐚𝐛𝐚𝐤𝐚 𝐝𝐚 𝐟𝐢𝐭𝐢𝐧𝐭𝐮𝐧𝐮𝐧 𝐤𝐚𝐛𝐚𝐫𝐢... 𝐔𝐛𝐚𝐧𝐠𝐢𝐣𝐢 𝐲𝐚 𝐚𝐥𝐛𝐚𝐫𝐤𝐚𝐜𝐢 𝐚𝐛𝐮𝐧𝐝𝐚 𝐤𝐚 𝐛𝐚𝐫𝐢.....

*ℙ. 10

_________Shuru yayi, kana ya tsurawa tsuntsayen dake shawagi acikin lambun ido, Allah Kaɗai yasan irin zafi da kuma raɗaɗin da yake ji a cikin zuciyarsa, haka kuma
UBANGIJIN daya halicceshi ne kaɗai yasan irin tashin hankalin da yake ciki.

Bai taba jin ya tsorata da lamarin abokan nasan ba sai yanzu, bai san munin abun da suke aikatawan ya kai haka ba.....

Shi abu daya yake damunsa, bai wuce manufar Saleem akan Muraydah ba idan ya aure ta ba, can you imagine ace wai za'a auriki ne saboda a ajiyeki a mataayinki na kekkyawar Mace, domin a Kece a raini da ke? Dama-dama ace zama da ita zaiyi da sauki, amma saboda ɗibar Albarka wai abokansa zai ajiye wa, wannan rashin sanin darajar dan Adam har ina?

Haka dai ya ƙaraci wannan zaman ba tare da ya samawa kansa mafita ba.....

Sai dai Allah kadai yasan irin daci da damuwan dake cikin ransa, wannan halin dake ciki Allah kadai yasani, tunda shi ne masanin gaibu, masanin zahiri da badini, buwayi gagara misali.......




*** *** ***

Zaune take tayi shuru tamkar Ruwa yaci ta, ba komai bane ya haddasa wannan damuwa tata, sai rashin aminiyarta kwaya daya, gashi yanzu har an kusa saka ranar bikin ta.

Rukka kenan, wacce har bayan ta rabu da Muraydah damuwa bata bar ta ba, tabbas ita kanta tasan tayi kuskure data bari fushi yasa ta yenke hukunci wa Muraydah, tunda tasan yanzu tana cikin
Giyar soyayyar Saleem ne....

Kamata yayi ta hakura, ta mata uzuri, kaman yadda Haidar ya fada mata bata kyau ta ba, tabbas bata kyau ta ba......

"But it doesn't mean zaki juri wulakanci akan Muraydah, har a yaushe ta hadu dashi da har zata nuna masa so akanki, ko don taga gidansu yafi naku kudi? Idan ma hakan ne ai ba ni naje nace inason ta da k'awance ba, wata zuciyar ta raya mata haka.....


Take fushin ta ya hau ya ninka na daa....

Don a ganinta ita ce Muraydah tayiwa laifi,
Tunda ta Za6i Saleem akan ta Wanda ai hakan bai kamata ba kwata kwata........



*****

"Hakuri zakiyi Khadija, domin banda addu'a babu abun da Muraydah take bukata a wajenki, ni kaina jikina yana Sanyi a wassu al'amuran natan, amma kici gaba da mata addu'a babu abunda zai faru in sha Allah duk kuma abunda kika ga ya faru to dama chan rubutacce ne a cikin littafin kaddararta, Wanda bata isa ta goge ba ko mu.

Hawayen daya ziraro mata ta saka hannu ta share, kana cikin damuwa da raunin ta ce "ba komai bane yake damuna ba face nasabarsa, bashi da nasaba mai kyau, inajin tsoron zargin mutane ya tabbata akan yaron nan, zai zama kenan mun kaita gidan halaka, gidan da babu iyayen da zasu zo hada jini dasu, gidan da kowa yake gudu, amma mu kuma a nan zamu jefa yarmu, ta karasa maganar wassu sabbin hawaye na kara zubowa.

A jikinsa Abhie ya jata kana ya kara da cewa
" kiyi hakuri, akwai karatun da bazaka koyeshi ba har sai ka shiga cikin makarantar gadan-gadan, a makaranta ake koyan karatu, amma idan aka kasa ganewa sai duniya ta koya maka Wanda kuma dole ne ka gane.....

Kiyi hakuri kawai kaman yadda nace sannan ki bita da addu'a don na Riga na gama yenke hukuci, gobe in sha zan ji daga gareta......

Idanun ta kawai ta mayar ta lumshe domin Allah kadai yasan yadda zuciyar ta ke suya......

Kuyi manage


07041353907

Kudan ZumaWhere stories live. Discover now