*NYAKU*
_(K'udan Zuma)_*Na*
_Sadeeey ce, Yar Gatan Royal Star_
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_*Alk'alaminmu 'yancinmu*
*Ko juti fuu wodi kerol*
P. 6
................"Bazan miki baki ba, amma Wallahi kina tare da matsanan ciyar wahala tun da kika maida waya ita ce cikon farin cikin rayuwar ki, kina da aiki babba, kuma kin hadu da wahala a rayuwar ki, wahalar da baki san ranar karewar ta ba, don ko aure kikayi Wallahi zai hadaki da mijin ki da ma dangin sa baki d'aya .....
Ace mutum ya maida kansa tamkar kashin maciji, ba taki ba magani, ba zakiyi wa kanki abun arziki ba, ballen tana kiyi wa wani wannan wace irin rayuwa ce Muraydah? Kina matsayin ya mace mai shekaru 24 da haihuwa, amma aikin kitchen kafin kiyi sai an kai Ruwa rana?
Kacokan rayuwarki kin dauka kin damk'ata wa waya, dama don irin ku nasara yayi ta, amma kuma yaci galaba akanki da masu irin halin ki, yayan yanzu basu da aiki sai maida waya tamkar alqurani dama carbi, "
" Ammmm........ "
" shut up! Stupid..!
Ammy ta fada cikin tsawa, kana ta kara da fadin
"Na rantse da Allah akan wayar nan zanyi mummunan sa6a miki fiye da yadda bakya zato, ai gata ba hauka bane, da garin Allah ya waye baki da aiki sai danna waya kina kwance kaman ruwa sai dai ki canja wajen kwanciya kaman inuwa, to Wallahi this time around bazan dauka ba, waya kuma na dauka naga kutin da zai sani baki........sannan idan kinaso karki amsa kiran mahaifinki ya rage naki."
Dama cike nake dake akan fadan ki da rukayya, Wallahi Muraydah kin bani kunya ba kadan ba, ace yanzu akan saurayi zaki rabu da kawar ki tun a tele - tele, ni ko lafiya kike? Akan saurayi, saurayin ma ba na gari, Wallahi kibi duniya a sannu, in dai ba so kike ta miki atishawar tsaki ba......
"Banga abun nacewa akan wannan yaron ba, yaron da bashi da hankali, bashi da Wadataccen ilimi sannan ba nagartacen nasaba da tushe mai kyau ba, yaron da kowa yake gudu hada zuri'a dasu, amma kika nace har kina fada da kawar ki da kuka tashi tare akanshi, Wallahi kiyi hankali, domin shi namiji K'udan Zuma ne, bazaki San hakan ba sai ya d'and'ana miki zafin ciwon sa kin rasa mai cire miki kaya zaki gane, shi da namiji sand'a akewa sonsa ba'a fitowa a fili, amma ke kika fito fili kika nunawa duniya kina son sa, kina tare da wahala.
Wallahi kibi a hankali, ki San me yake miki ciwo, ki San waye zaki tsaya dashi a matsayin saurayi, sannan kisan Wanda zuciyarki zata fada so a akansa, ba dai irin yaran Alhaji Mannir Barau ba, ki sani ba uba nagari kike kokarin za6awa yayan ki na nan gaba ba, sannan ba miki nagari kike kokarin za6awa kanki ba, ki farka tun wuri kafin lokaci ya kure miki.......
Sanyaya murya tayi, kana taci gaba da fadi.
"Muraydah please ki nutsu, ki San me miki ciwo, ki San inda kike saka kafarki, wannan soyayyar banji a jikin zata haifar miki da da mai ido ba....
Dan Allah ki nutsu ki za6awa kanki Abu mai kyau, sannan ki nemi Za6i Allah.
. Ta karasa maganar tana fita a dakin...........
Ta fita ta bar Muraydah cikin kuncin zuciya don numfashin ta har wani dagawa yake, don bawai maganganun Ammy na karshen sun shiga kanta bane, hasalima ko daya bai shiga ba, don shiga suke da kunnen hagu suna fita ta dama.
Sannan Abu daya yake dawo mata a rai Tsabar bakin ciki da haushin kar6e mata wayan da Ammy tayi, taya babba da ita Ammy zata kare mata waya kaman wata yar secondary school, kwalin degree fa gareta, an then she's 24yr da yanzu, ba wai 14 ba, jami'a ta gama ba wai primary ko secondary school ba, Wallahi wannan abun ba zai yu ba, dole ma take wajen Abhie yasan ya zaiyi da ita, ta karasa maganar tana mukewa tare da fita daga dakin.
Direct 6angaren Abhie ta nifa, daga isa sallama tayi kana ta kutsa kanta cikin babban dalon mahaifin natan, cikin tafiyar hankali wande ke nuna zallan rashin jin dadin da zuciyarta ke ciki.......
Hannu ta mika mata bayan ta iso, kasan cewar sa mutum mai sakewa iyalan sa fuska yasa cikin sakin fuska ya ce "me ya sami Uwar tawa, waye ta6a min ita naji?
Zama tayi a gefen sa tana kara kum6ura baki, cikin yanayin sakalci ta ce" Abhie ba Ammy ba ce ta karba min waya, dan Allah Abhie ka gani fa, babba dani har a yanzu a shekaru na ace ina fuskantar wannan matsalar, Abhie kaman niii...... I'm 24 fa Abhie. Ta karasa maganar cikin wani irin yanayin dake nuna ciwon da abun yake mata a rai.......
Gamarwa ta maganan yayi dai-dai da fitowar Ammy daga dakin Abhie'n, kallon ta tayi, cikin jin haushi ta ce "a ganinki ba kike babba, amma ni a gani na dake da yaro mai rarrafe baku da maraba, kuma Wallahi kisan ta yadda zaki na fitar da magana, ai dama nasan shekarun kin ne suke janki kike ganin kaman ke wani Abu ne, to Wallahi ki sani you are nothing to me, domin dake da bakwaini baku da maraba, tana gama fada kuwa ta fita abun ta.
Kallonta ta kan mayar Abhie Wanda ya wadata fuskarsa da murmushi, ganin zata sake magana yasa ya dakatar da ita kana ya ce "Mamana kiyi hakuri, su iyayen dole ne abi abunda suke so ko da bai yuwa yaro dadi ba, sa bo da son Gama wa da duniya lafiya, zan karba miki wayan ki, amma kema ki mata abun da take so kinji? Kinga kema nan gaba ke uwa ce, ko kina son yaranki suna miki rashin ji? Ta fadi maganar yana kallon ta.
Kai ta girgiza masa alaman a'a, a yayin da fuskarta ke nuna zallan farin ciki na jin Abhie ya ce itama zata wai haihu, yawwa Uwata, je ki bawa Ammy hakuri kinga ranta ya baci ko,
DA to ta amsa masa tana fita. Direct kuma 6angaren Ammyn ta nufa, sai dai samun ta tayi a toilet hakan yasa tayi dakin ta a ranta tana raya ba lallai ta koma ba, don kuwa yasha ruwa m......
(Idan dadi bai kai ki ba, akasin sa zai kaiki yarinya.)
******
*MIYETTI SPECIALIST HOSPITAL*
Zaune yake a cikin office dinsa na consoltant doctor dake mallakin sa, kujeran cikin office din yake juyawaa sannu hankali, domin ya bawa kofar ma baya.
Hakan ne na bani daman karewa office din kallo.
Babban office ne Wanda ya amsa sunansa office, ba laga-laga ba.
Babban office din dauke yake da abubuwan da suka hada da dan madaidaicin fridge, sai TV, a gefen kuma kujeru ne masu kyau simple designers guda hudu, sai table a tsakiya, Wanda ke dauke da dan karamin picture na shi a tsakiyar table din Wanda ya fito da zallan kyau da kuma iliminsa. Gefe daya kuma ke6antaccen waje ne inda zai Iya kwantar da marar lafiya mai dauke da gado da sauran abubuwan bukata, sai table dinsa Wanda yake dauke da dan Abu mai dauke da cikekken sunan sa wato *DR. ALIYU ABUBAKAR MUKADDAS* Wanda a takai ce yake *DR. A. A* sai kujeru guda biyu masu fuskantar nasa
Kofoki guda biyu ne a cikin office din. Daya na rest room ne, Wanda yake dauke toilet a ciki, sai kuma kofar fita.....
Office ne mai kyau Wanda aka masa ado da dark blue sai ratsin baki a akan samu jefi-jefi a cikin office.....
Yayi nisa sosai cikin tunani yaji Ana knocking kofar, lumsassun idanunsa kyawawa ya bude, shuru yayi na nan dakiku, kaman bazai ce komai ba sai kuma ya ce..........
07041353907
YOU ARE READING
Kudan Zuma
RandomWannan littafi labarin wata yarinya ne akan wata yarinya mai suna Muraydah, wacce ta bijirewa umarnin iyayen ta akan auren saurayin da iyayen basu da tarbiyarsa ba, ita kuma ta nace har takai baban ta ya cire yayi furucin cire hannu a kanta, Wanda d...