*NYAKU*
_(K'udan Zuma)_*Na*
_Sadeeey ce, Yar Gatan Royal Star_
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_*Alk'alaminmu 'yancinmu*
*ℙ. 11
Bayan kwana biyu,
______A washe garin ranar da sassafe ya fita daga gidan don dubo kayan da aka shigo musu dasu daga waje, ba kasafai yake zuwa wajen kayayyakin da sukayi order ba, sai dai kasan cewar wannan kayan yasha banbam da sauran yasa da kansa yake zuwa gudun kar a samu matsala.
(Allah ya dai ya kiyaye matsala, amma ai dole wata rana kan matsala ta faru... )
Rayuwa tayi masa zafi ta inda bai zata ba, haka kuma bai tsamman ta,
Shi din ba mutum bane mai yawan magana ko mita akan wassu abubuwan da suka shafi rayuwar sa ko na mutane, hakan yasa baya magana ko da Ammy akan abunda yake damunsa,
Yana rayuwarsa ne dai dai da yadda ubangijinsa ya tsara masa ita, yana da uwa a raye amma bazai Iya gaya mata abubuwan dake damunsa ba, don gani yake tamkar ya hada Allah da wani ne, hakan yasa yayi shuru, sai dai sannu a hankali damuwar tayi ta cinsa ba tare da ya farga ba,
Ammy kanta kallonsa kawai takeyi, amma ba karamin damun ta yayi ba, har fada wa tayi ita ma, (uwa kenan) amma ganin bai gaya mata bane yasa ta zuba masa idanu, don tasan a irin tarbiyar da tayi wa ALIYU da sauran yaran ta, duk abunda yake damunsa indai zata Iya sani to ita ce Mace ta farko da yake gaya wa, wannan tarbiyar da tayiwa yaran ta kenan
_(a matsayin ki na uwa kiyi amfani da damar ki na tun tasowar yaranki ki tarbiyar da su, Kada ki nunawa yaranki tsanani, domin manzon Allah SAW yace *Yassiru wala tu assiru, wato ku saukaka Kada ku tsanan ta* ki zamowa yayanki aminiya, sannan ki koya musu yadda zasu na fada miki damuwar su, ki nuna musu lokacin sakin fuska daban lokacin kamun fuska daban, ba wai ki daure gammm ba, domin komai ma rayuwa Ana so idan aka ciza sai a hura..... Allah yasa mu dace.... )*****
"acikin wadanda suke zuwa wajenki ki duba wanda ya kwanta miki, kuma kika yaba da hankalinsa, karki bari rudin zamaani ya rudeki, karki bi so, ki yi nazari kiyi tunani domin Allah SWT ya ce
وعسى أن تكرهوا شيأ وهوخيرلكم, وعسى أن تحبوا شيأ وهو شرلكم والله يعلم وأنتم لاتعلمون....
_"Perhaps you hate a thing and it's good for you..._
_And you love a thing, and it's bad for you" _
_Ma'ana sau tari kana kin abu alhali alkhairi yake a gareka, sannan sautari kana son wani abu alhali ba alkhairi yake a gareka ba_
Don haka ki duba abunda ya dace, duk da nasan babu abunda zai canja kaddara face addu'a, kiyi tunani kiyi nazari, sannan ki nemi zabin Allah.....
Nan da kwana biyu zakiji daga mahaifiyarki, ki gaya mata wanda kika zaba kika ga ya dace da irin mijin da kike so wa kanki, Mijin da ba zakiyi dana sanin zabansa ba, mijin da zaki bugi kirji a ko ina ki fadi waye shi, Mijin da ba zakiji nauyi, da kunya fadan waye shi ko kuma halayensa ba, sannan Wanda kika ga ya dace daya zama uba ga yaranki, suruki kuma D'a ga iyayen ki, nagartacce, mai Ilimi, Wanda ya fiki hankali, nutsuwa da hangen nesa,
Abhie ya karasa maganar cikin wani irin yanayi da shi kadai yasan sa."toh in sha Allah Abhie zanyi hakan , ta karasa maganar kanta a kasa, daga haka ya sallameta ta mike ta nufi dakin ta....
Tabbas idan da tayi tunani a maganganun Abien na tsakiya dana karshe duk jurwaye yayi mata mai kama da wanka, Wanda a shekarunta ya kamata ta gane, amma inaa masu Iya magana sunce Wanda yayi nisa baya jin kira, wuya ce kadai zata sa shi yaji ba shiri ....
Daga isar ta daki waya ta dauka taci gaba da live din da take a manhajar tiktok don dama pause ta saka ta amsa kiran abie, Wanda shi ya kara shagaltar da ita, daga yin abubuwan da Abie yace tayi.
Sai ranan da ya diba mata ya cika ta tuna, da ta dami kanta Nan kuma wata zuciyar ta raya mata cewa "wani zabi zaki nema, ai tunda Allah ya hadaku ya gama tabbatar da alkhairi acikin tarayyar ku, don haka ba wani istihara da zakiyi, Saleem ne alkhairin ki Muraydah, nan kuwa ta hau kai ta zauna,"
******
Ido ta tsura masa, ganin tunda suka gaisa tsawon wassu dakiku ya sadda kansa kasa bai dago ba,
"Baba na lafiya kuwa?
"Lafiya klau Mamy,
To meke damunka naga kayi shuru?
Ba kwana - kwana ya zayyane mata komai, daga farkon haduwar su har zuwa inda yaji su Saleem na maganganun, kana ya rufe da fadin cewa "Mamy hankali na ya tashi dana ji manufar Saleem akan Muraydah, Mamy na rasa yaya zanyi, bayan ke ban ta6a jin son wata halitta kaman Muraydah ba, ita ma bansan ina son ta ba sai dana ga zan rasata, Mamy kiyi min addu'a kar wannan kaddara tafi karfina, ni d'in mai rauni ne akan wannan siyayyar, na rasa yaya zanyi, ya karasa maganar cikin kuna da zafin da yake ji a cikin zuciyarsa, idanun sa sun kad'a sunyi ja, a yayin da jijiyoyin idonsa suka mike suka fito rad'a-rad'a.....
Ita kanta Mamy ba k'aramin tashi hankalin ta yayi ba, da jin manufar Saleem akan Muraydah, kana cikin danne nata tashin hankali ta ce "lallai soyayyar ta rikita maza, dubi yadda ta mayar min uba, ta fada cikin barkwanci tana mai fad'ad'a fuskarta da murmushi tamkar babu abunda yake damun ta.
Murmushi shima ALIYU yayi kana ya sunkuyar da kansa k'asa,
Numfasawa tayi kana tace.......
YOU ARE READING
Kudan Zuma
RandomWannan littafi labarin wata yarinya ne akan wata yarinya mai suna Muraydah, wacce ta bijirewa umarnin iyayen ta akan auren saurayin da iyayen basu da tarbiyarsa ba, ita kuma ta nace har takai baban ta ya cire yayi furucin cire hannu a kanta, Wanda d...