*NYAKU*
_(K'udan Zuma)_*Na*
_Sadeeey ce, Yar Gatan Royal Star_
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_*Alk'alaminmu 'yancinmu*
......𝕄𝕦𝕟𝕪𝕒𝕟 𝕜𝕠 𝕨𝕒𝕣𝕒𝕟𝕚, 𝕞𝕦𝕟𝕪𝕒𝕟 𝕜𝕠 𝕨𝕒𝕣𝕒𝕪𝕚, 𝕨𝕒𝕝𝕒 𝕜𝕠 𝕨𝕒𝕣𝕒𝕟𝕚 𝕛𝕠𝕟𝕕𝕖, 𝕥𝕠 𝕒 𝕗𝕒𝕞𝕚𝕕𝕚 𝕜𝕒𝕝𝕞𝕒𝕛𝕚 𝕒 𝕗𝕒𝕞𝕚 𝕕𝕦𝕟𝕪𝕒......
*ℙ. 9
................Nasaara bazai taba daina k'era waya ba, kaman yadda waya bazata daina dulmiya rayuwar mutane cikin shagala ba.
Ba abunda ke cikin waya sai shagala da lokaci ba, waya tana taka muhimmiyar rawa, wajen shagaltar da bawa daga amfani da lokaci, ganewa kawai kowa ya kasayi, duba da irin mummunar sabon dake shiga tsakanin waya da mai ita, kina daga ciki Muraydah, Allah ya shiryi masu halin ki.
Gata nan, na dawo miki da ita, sai ki warke daga zazzabin dake damun ki Wanda ya kamaki sanadiyyar karbe wayanki da nayi, Wallahi Allah kina da aiki babba....
Wannan waya kikayi wasa zata zame miki jarrabawa, muddin ko baki canja ba to bana ce komai ba, amma akwai matsala.
Ammy ta kare maganar tana dungurar mata da wayan a kanta, kana ta bar dakin cikin jin zafin yadda yarta ke neman maida waya rayuwar ta......
Ba tare data damu da fushin Ammyn ba ta dauki wayan ta cikin jin dadi, don take ta nemi zazzabin ta rasa, (dama ai zazzabin na wayar ne)
******
Tafiya yake sannu a hankali, tafiyar dake motsa dukkan gabban jikin sa, taku yake tamkar baya son taka kasar, tafiya yake cikin rashin kuzari, sai dai rashin saurin tuni ya haifar wa tafiyar da wani irin salo wajen mai kallon sa.
Sallama dauke a akan labbansa ya shiga cikin palon Mahaifiyarsa, inda ya same ta zaune kaman yadda ya tsammanta......
Ido ta kura masa, tun sanda ya shigo tamkar mai son karantar wani Abu.
Farar mace ce, wacce a kalla zata kai kamanin shekaru hamsin da biyar da haihuwa, fara ce tas wacce hutu da yanayin kyawun jikin ta ya 6oye hakan, tana zaune a yayin da take kallon Tashar Sunna TV, yatsun hannun ta da suka sha jan lalle ta mika alamun ya zo.
Cikin kara saurin ya kara so inda take,
A kasan kafafun ta ya zauna, kana ya Dora kansa akan kafunsa, daga haka ya maida idanun sa ya lumshe, yana mai sauke ajiyar zuciya.....
Shi kadai yasan abunda yake ji, sai kuma ubangiji daya halicceshi.......
Numfashin Mamy ta sauƙe, don ba tun yau ba, take hango damuwa ƙarara akan fuskarsa ba, ganin bai gaya mata bane, yasa ita ma bata nuna masa ba, amma kuma ganin abun yaƙi ci, yaƙi cinyewa ne ya dameta, amma dai koma me ne zata taya shi da addu'a, ba abinda zatayi masa daya wuce ta a matsayinta na uwa, kuma mahaifiya.......
******
Zuwa lokacin da aka saka musu tuni sun taru a dakinbautan nasun kaman yadda suka sani, ko nace suka saba.
Palour ne mai matuƙar girman gaske, Wanda yasha kayan alfarma na more rayuwa, an masa kwalliya da ja da baki, musamman ma carpet din dake malale a ƙasan palourn.
Sai da Duk kyau da haduwan cikin palon kujeru guda uku ne ƙadai a ciki, wato na manyan, a yayinda da na tsakiyan yafi ko wanne kyau, don shi asalin kujera ce, ta sarakuna, wacce akayi ta da danyen zinare, a yayinda sauran biyun kuma akayi su da zallan ƙarfe mai kalan zinare, kana aka kawata jikinsu, sukayi kyau na ban mamaki da al'ajabi......
********
Mace ce wacce daga gani ta dan manyan ta, don zata Iya kai shekaru 56 da haihuwa ko ma fi da hakan, tabbas don tsufa kam ta tsufa, domin ba wani kyan jiki gare ta ba, Wanda zai gasa boye tsufan natan.
Zaune take kan wannan babban kujera, kanta sanye yake cikin kambu mai kyau Wanda akayi shi shima da danyen zinare, Wanda ya kasance na girma, haka kuma ya sauko ta gaba har kan hancinta, haka ma hannun ta rike yake da sanda, dogo kalan kambun dake bisa, kanta.
Na gefen daman ta wani mutum ne, Wanda zai Iya kaiwa 44 zuwa da 46 da haihuwa, don babban mutum ne, sai kuma na gefen hagun ta daya kasan ce, Saleem.
Sai mutanen dake ƙasa su, wanda ke gurfane tamkar masu ne neman yafiya (wa iyazubillah) dukkan su babu mai kaya a jikin sa, sai wassu kyallaye, da suka daura a k'ugunsu, kana da kuma tsakiyar kansu,
A yayinda ita kuma, ta zama ba kaya a jikin ta, sul kenan, tsirara, sai wannan kambun dake kanta (aikin ɓurut kenan)....
Gabansu kaɗan kafin a isa gaban Uwar tasun wato tsakiya kenan, abu ne tamkar ƙwarya, ko nace kasko, dake cike da jan jini, kana bakin kaskon an ɗaura masa shima jan ƙyallen wanda ya zagaye kaskon dashi.....
Dukkansu sunyi shuru, kana sun sunkuyar da kayukansu a kasa,
Sandan hannun ta, ta dan buga, Wanda yasa naga Kaseem ya Mike, cikin tafiyan hankali tamkar mai neman izinin carpet din da yake takawa a kai, still kuma kansa na ƙasa,
Gaban kaskon yaje ya tsaya, wassu maganganu yayi, kama ya saka hannu ya daga kaskon daga kan abun zaman da aka mishi, domin ajiye shi.
Duk girman kaskon nan, haka ya kimkimeshi, yana ci gaba da tafiya sannu a hankali, a yayin da su kuma suke raka shi da wassu maganganu, da ba'a gane ko menene suke faɗa ba.
Har gaban ta yaje ya dire haskon nan,
Hannu ta saka ta karbi kaskon, kana ta k.........
07041353907
YOU ARE READING
Kudan Zuma
RandomWannan littafi labarin wata yarinya ne akan wata yarinya mai suna Muraydah, wacce ta bijirewa umarnin iyayen ta akan auren saurayin da iyayen basu da tarbiyarsa ba, ita kuma ta nace har takai baban ta ya cire yayi furucin cire hannu a kanta, Wanda d...