*NYAKU*
_(K'udan Zuma)_*Na*
_Sadeeey ce, Yar Gatan Royal Star_
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_*Alk'alaminmu 'yancinmu*
*ℙ26__29*
______Istihara neman za6in Allah, haka kuma tayi kaman yadda mahaifinta ya buk'ata...
Taji kuma wanda hankalinta yafi karkata gareshi, amma inaa, wani abu ne yazo ya danne mata kirji, haka kuma akwai abunda take ji akan Saleem mai girman gaske, wanda ita kanta tana ji yayi mata k'arfi, sai dai bata da wani wayo ko dabara, domin kuwa k'addara ta riga fata.....
Shirye-shirye take na zuwan Saleem gidan, wanda tasha masa magiya kaman ba gobe, daga k'arshe dai ta samu ya ce zaizo, ta gayawa Ammy cewa Saleem na zuwa, Ammy dai bata nuna mata komai, duk da tasan waye ne Saleem d'in....
Abun da Muraydah bata sani ba shi ne Abie da Ammy sun gama yenke hukunci akan auren Muraydah, Ammy ta nusar da Abie tare nuna masa illar aurar da Muraydah ga yaro irin Saleem, gama ahalin baki daya, domin kuwa bashi da abunda mutum zai Iya daukan dansa ya bashi, sannan ita haka kawai taji Saleem din mata ba, saboda nacin da Muraydah ta nuna a kansa yayi yawa, infact ita ta fara tsoron abun, domin ita zata Iya cewa bata taba ganin so irinsa ba, son ma maso wani, don ita kanta tasan Saleem bai damu da Muraydah kaman yadda ita ta damu dashi ba, tun a matakin farko wato kiran waya, duk wanda ya zauna da Muraydah na wuni daya, zai san ita ke neman Saleem bashi yake neman ta ba...
Haka kuma daga k'arshe ya yarda, kuma ya yenke hukuncin kiran Muraydah ya nuna mata matsayinsa, tare da gaya mata hukuncin daya yenke akanta, duk da tana da hakki a kansa, amma dole ne ya kareta daga fad'awa abun da zai cutar da ita, koma kai tsaye ya ce daga halaka, don Allah kadai yasan abunda zata tarar a can, don masu Iya magana suka ce wai daga ganin kura ansan zaici Akuya...
*** ***
***Saleem ya zo kaman yadda yayi alk'awari, (sai dai abunda bata sani ba, zuwan ma ba rad'in kansa bane, su Bilal ne suka saka shi zuwa, bayan sun gama hure masa kunne tare da d'orasa akan wassu abubuwan da ba dai-dai bane, don daga farko ya ce bazai je ba, amma sai su bilal suka lo6a shi, akan cewa kar yak'i zuwa, daga k'arshe har suka ce masa kawai yaje ya gama da komai a yau, kar ya bar gidan har sai komai ya kanka ma, ya doru akan abunda suka gaya masa ya zauna akai daram, har wani munafukin murmushi fuskarsa ke fitarwa....
***
Muray & Saleem
"D'agowa yayi daga danna wayan da yake ya sauk'e idanunsa akan kekkyawar farar fuskarta, ta asalin fulani da babu algus a ciki, murmushi yayi dashi kadai yasan ma'anarsa...
Kana cikin wani irin boyayyen yanayi ya ce
"Beb, kin sani ina sonki, tunda ni na fara miki, nazo wannan zuwan ne muyi magana ta fahimtar juna, ina son na tura gidan ku maganan auren mu shin kin amince???
Cikin wani irin yanayi da Allah kadai yasanta a ciki ta ce" Haba Hubby yanzu idan zaka turan ne sai kayi min magana? Bayan kasan abunda nake jira daga gareka kenan?
Murmushi Saleem yayi da shi kadai yasan ma'anarsa, kana ya ce "dole na gaya miki ai, shin kina so na? Kin amince na zama miji a gareki? Kin amince zaki zama matar Saleem mallakinsa? Mai iko dake da komai naki??
Cikin wani irin mashahurin dadi ta ce "Ehh"
Murmushi yayi daga farko, daga haka ya canja fuskar zuwa ta tausayi, idanun sa ya kankance kana ya ce "matsalar d'aya ce Beb, sai naga kaman gidanku ba za'a barmu muyi aure ba, kaman basa so na, anya zasu barmu muyi aure...
Cikin wani irin yanayi da take ji tun zuwan Saleem data kalli kwayar idonsa, ta ce,
Ai Wallahi duk duniyar nan, banga mai rabani da kai ba, ko da kuwa waye ne ba'ayi ruwan tsiransa ba, banga mahaluk'in daya isa ya rabani da kai ba, ko da kuwa Abie ne da kansa!
Abie dake tsaye bakin kofar falon, domin Ammy ta gaya masa cewa Saleem yazo, da nufinsa zaizo ya ce masa yayi hakuri, ya zaba wa Muraydah miji....
Sai dai jin abunda suke tattaunawa yasa ya tsaya, cikin fushi, da fusata ya ce.....
07041353907
YOU ARE READING
Kudan Zuma
RandomWannan littafi labarin wata yarinya ne akan wata yarinya mai suna Muraydah, wacce ta bijirewa umarnin iyayen ta akan auren saurayin da iyayen basu da tarbiyarsa ba, ita kuma ta nace har takai baban ta ya cire yayi furucin cire hannu a kanta, Wanda d...