*NYAKU*
_(K'udan Zuma)_*Na*
_Sadeeey ce, Yar Gatan Royal Star_
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_*Alk'alaminmu 'yancinmu*
......𝕄𝕦𝕟𝕪𝕒𝕟 𝕜𝕠 𝕨𝕒𝕣𝕒𝕟𝕚, 𝕞𝕦𝕟𝕪𝕒𝕟 𝕜𝕠 𝕨𝕒𝕣𝕒𝕪𝕚, 𝕨𝕒𝕝𝕒 𝕜𝕠 𝕨𝕒𝕣𝕒𝕟𝕚 𝕛𝕠𝕟𝕕𝕖, 𝕥𝕠 𝕒 𝕗𝕒𝕞𝕚𝕕𝕚 𝕜𝕒𝕝𝕞𝕒𝕛𝕚 𝕒 𝕗𝕒𝕞𝕚 𝕕𝕦𝕟𝕪𝕒......
*ℙ. 9
................Duk da kasan cewarsa namiji, haka kuma ba mai kana nan shekaru ba, sai dai jinsa a jikin mahaifiyarsa yasa yaji duk jarumta da taurin zuciyar da yake dashi ya ji sun kau, take rauni ya maye gurbin, wani irin damuwa da kunci yake jin zuciyarsa a ciki daya haddasa canjawar bugun da zuciyarsa keyi ji, shi ba mai saurin kuka bane saboda taurin rai da zuciyar da Allah ya masa, amma sa boda jinsa a jikin mafi soyuwar halitta, yasa yaji hawaye na tsatstsafowa daga cikin kwanyar kansa, sannu a hankali yaji zuciyarsa na sanyi, kaso arba'in na damuwar sa ya gushe, take ya fara sauke ajiyar zuci tamkar wanda yayi tsere, hakan yasa ya maida idanun sa ya lumshe, yana mai tunanin abubuwa da yawa {𝑼𝒘𝒂 𝒌𝒆𝒏𝒂𝒏, 𝒖𝒘𝒂 𝒂𝒃𝒂𝒓 𝒌𝒂𝒖𝒏𝒂𝒓 𝒚𝒂𝒚𝒂𝒏𝒕𝒂, 𝒖𝒘𝒂 𝒂𝒃𝒂𝒓 𝒔𝒐𝒏 𝒚𝒂𝒚𝒂𝒏𝒕𝒂, 𝒖𝒘𝒂 𝒌𝒆𝒏𝒂𝒏 𝒇𝒊𝒕𝒊𝒍𝒂, 𝒂𝒃𝒂𝒓 𝒕𝒊𝒏𝒌𝒂𝒉𝒐 𝒅𝒂 𝒕𝒖𝒕𝒊𝒚𝒂, 𝒇𝒂𝒓𝒊𝒏 𝒄𝒊𝒌𝒊 𝒅𝒂 𝒋𝒊𝒏𝒅𝒂𝒅𝒊, 𝒎𝒂𝒉𝒂𝒊𝒇𝒊𝒚𝒂 𝒉𝒂𝒔𝒌𝒆𝒏 𝒄𝒊𝒌𝒊𝒏 𝒓𝒂𝒚𝒖𝒘𝒂𝒓 𝒚𝒂𝒚𝒂𝒏 𝒕𝒂, 𝒎𝒂𝒉𝒂𝒊𝒇𝒊𝒚𝒂 𝒉𝒂𝒍𝒊𝒕𝒕𝒂𝒓 𝒅𝒂𝒕𝒂 𝒔𝒉𝒂 𝒎𝒂𝒌𝒂 𝒘𝒂𝒉𝒂𝒍𝒂 𝒇𝒊𝒚𝒆 𝒅𝒂 𝒌𝒐 𝒘𝒂𝒄𝒄𝒆 𝒉𝒂𝒍𝒊𝒕𝒕𝒂 𝒂 𝒅𝒖𝒏𝒊𝒚𝒂, 𝒉𝒂𝒍𝒊𝒕𝒕𝒂𝒏 𝒅𝒂 𝒃𝒂𝒚𝒂𝒏 𝒂𝒍𝒍𝒂𝒉 𝒅𝒂 𝒎𝒂𝒏𝒛𝒐𝒏𝒔𝒂 𝒃𝒂𝒃𝒖 𝒌𝒂𝒎𝒂𝒏 𝒕𝒂, 𝒔𝒉𝒊𝒏 𝒘𝒂𝒚𝒆 𝒌𝒂𝒎𝒂𝒕𝒂 𝒌𝒂𝒔𝒐 𝒌𝒖𝒎𝒂 𝒌𝒂 𝒏𝒖𝒏𝒂𝒘𝒂 𝒌𝒂𝒖𝒏𝒂 𝒊𝒅𝒂𝒏 𝒎𝒂𝒉𝒂𝒊𝒇𝒊𝒚𝒂 𝒃𝒂???? 𝒀𝒂 𝒂𝒍𝒍𝒂𝒉 𝒌𝒂 𝒂𝒛𝒖𝒓𝒕𝒂 𝒊𝒚𝒂𝒚𝒆𝒏 𝒎𝒖 𝒅𝒂 𝒎𝒂𝒇𝒊 𝒂𝒍𝒌𝒉𝒂𝒊𝒓𝒊𝒏 𝒔𝒂𝒌𝒂𝒎𝒂𝒌𝒐 𝒘𝒂𝒕𝒐 𝒈𝒊𝒅𝒂𝒏 𝒂𝒍𝒋𝒂𝒏𝒏𝒂𝒕𝒖𝒍 𝒇𝒊𝒓𝒅𝒂𝒖𝒔, 𝒚𝒂 𝒂𝒍𝒍𝒂𝒉 𝒃𝒂 𝒅𝒐𝒏 𝒊𝒔𝒂𝒏𝒂 𝒃𝒂, 𝒚𝒂 𝒂𝒍𝒍𝒂𝒉 𝒌𝒂𝒊𝒏𝒆 𝒂𝒍𝒍𝒂𝒉, 𝒂𝒍𝒍𝒂𝒉 𝒏𝒂𝒔𝒂𝒏 𝒊𝒅𝒂𝒏 𝒌𝒂 𝒃𝒂𝒏𝒊 𝒃𝒂𝒃𝒖 𝒎𝒂𝒊 𝒉𝒂𝒏𝒂𝒘𝒂, 𝒉𝒂𝒌𝒂 𝒌𝒖𝒎𝒂 𝒊𝒅𝒂𝒏 𝒌𝒂 𝒉𝒂𝒏𝒂 𝒃𝒂𝒃𝒖 𝒎𝒂𝒊 𝒃𝒂𝒚𝒂𝒓𝒘𝒂, 𝒖𝒃𝒂𝒏𝒈𝒊𝒋𝒊 𝒌𝒂 𝒋𝒊𝒌𝒂𝒏 𝒎𝒂𝒉𝒂𝒊𝒇𝒊𝒚𝒂𝒕𝒂, 𝒂𝒍𝒍𝒂𝒉 𝒌𝒂 𝒈𝒂𝒇𝒂𝒓𝒕𝒂 𝒎𝒂𝒕𝒂, 𝒌𝒂𝒔𝒂 𝒓𝒂𝒉𝒂𝒎𝒂, 𝒉𝒂𝒔𝒌𝒆, 𝒏𝒊'𝒊𝒎𝒂 𝒂 𝒄𝒊𝒌𝒊𝒏 𝒌𝒂𝒃𝒂𝒓𝒊𝒏𝒕𝒂 𝒅𝒂 𝒅𝒖𝒌𝒌𝒂𝒏 𝒎𝒖𝒔𝒖𝒍𝒎𝒂𝒊 𝒃𝒂𝒌𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 } ......
Sun dauki lokaci mai tsayi a haka ba tare ko wanne yayi magana ba, sai numfashin da yake saukewa a kai a kai, ruwan dake gefenta ta mika masa ba tare da tayi magana ba, hannu ya saka ya amsa ba tare da musu ba, ya saka kofin tambulan din a bakin sa ya fara zugan ruwan sanyin dake ciki.
bayan komai ya lafa ne, ta kalleshi kana cikin sanyin murya da kuma nutsuwa irin na iyayen dake son magana da yaran su ta ce......
*****
Wayar a kunne ne, don har wannan lokacin Ammy bata kashe ba.
Ta dauka zata kalli miss calls din Saleem saboda kwana kin data dauka bata ki rasa ba, sai dai taga wayam, sai ma missed call din Numbern dake kiran ta kullum Wanda ta sakawa suna a ranta anace, don shi kam yafi kwaya 40,
Tabbas taji wani iri a ranta, hakan kuma ya sosa mata rai ba kadan ba, amma saboda karfin da giyar soyayya tayi mata a zuciya yasa bai wani yi tasiri ba, bata ganin laifin sa ko kadan, har yau bata ji wani Abu daya rage mata soyayyarsa ba a cikin zuciyar ta sai na karuwa da yakeyi, duk da ba zuwa ya keyi a kai gidan ba, don baya zuwa yanzu kwata kwata, a daa ne yy yayin zuwa gidan kusan sati sau biyu.
Bata bi ta kan wannan no din ba, sai kawai ta buge da kiran number din Saleem Wanda aka masa saving da *H. Y. T* kira na FARKO har ya yenke ba'a dauka ba, sai Ana biyu ne ya dauka murya kasa kasa don lokacin yana tare da Bilal suna masha'arsu....
A yayinda da su kaseem ke kan sofa don ba kunya juna suke ba.
Bilal ya matsar daga jikin sa kana ya dauka wayan, cikin magana kasa kasa yake amsa mata komai, cikin maganan ne take ce masa ai Ammy ce ta karbi wayan ta shiyasa yajita shuru kwana biyu , ba tare da wata damuwa ba, yace mata "OK,"
A hakan dai suka gama wayan yana bata amsa a takaice kaman wani miskili, don kwata kwata Saleem na miskili bane, kawai wa ita yake yiwa,
Kaseem ne ha kalleshi bayan gama wayar tasan kana ya ce "Dude bata wannan hanyar zaka bi da yarinyar nan ba, ai kamata yayi, ka nuna mata so idan an shiga daga ciki ta ga zahiri, amma ai hakan zaka fita mata a rai....
Kallonsa Saleem yayi na wassu dakiku, kana ya murmusa, sannan ya ce" kai ma kanka kasan Inada yarda da kaina, ka kuma San bana wasa da kuduri na, ni nasan irin son dana cusa mata, haka kuma da taimakon Uwar Zaure, wanda hakan yasa zata Iya bijirema kowa ciki har da wadanda suka kawo ta duniya."
" Amma dai ba za'a ki bin taka ba, gwara naci gaba da mata shigo-shigo ba zurfi, kafin ta shiga ramin ta gane tamkar ramin karya, don kuwa kurerre ne, bashi da zurfi,
Duk kansu shewa suka buga a dakin tamkar wassu yara.....
Ba karamin tashin hankali Dr. A.A ya shiga ba, da jin maganganun su Saleem, har wani jiri yake gani, jin wai ya hadata da Uwar tsafinsu, hakan na nufin juya mata kai sukayi kenan, "innanillahi wa inna ilaihirraji'un, wannan su ne kalmomin dake fita a bakin sa, dakin da bai shiga ba kenan, don dama ya zo wajensu ne saboda wai ko idan ya zauna cikin childhood friends dinsa, don yasan zai dan kara sakewa, amma sai ma wani abu daban daya kara dauka ma kansa, direct gida kawai ya koma, da isarsa ya nufi side dinsa, ba tare daya shiga 6angaren Mamy ba, da shigarsa bai zarce ko ina ba, sai garden din dake bayan side dinsa ya nemi daya daga cikin kujeru dake cikin garden din ya zauna...........
07041353907
YOU ARE READING
Kudan Zuma
RandomWannan littafi labarin wata yarinya ne akan wata yarinya mai suna Muraydah, wacce ta bijirewa umarnin iyayen ta akan auren saurayin da iyayen basu da tarbiyarsa ba, ita kuma ta nace har takai baban ta ya cire yayi furucin cire hannu a kanta, Wanda d...