12

1 0 0
                                    

*NYAKU*
_(K'udan Zuma)_

*Na*

_Sadeeey ce, Yar Gatan Royal Star_

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*


*ℙ. 12

______ "Rayuwa cike take da k'alubale, jarrabawa, da kuma wahala, dole ne ka wahala a rayuwa musamman a lokacin kuruciyarka, idan kuma kak'i shan wannan wahalar tamkar ka ajiye ta ne wa tsufanka, rayuwa kaman wuk'a haka take takan iya zama alkhairi ko sharri, kayi kokarin lullube sharrin da alkhairin.......

Kayi hakuri da kaddarorin rayuwa hakuri shi ne kadai
bangon da zaka dafa, kayi hakuri a halin damuwa bakin ciki ko farin ciki, kayi hakuri a duk yadda rayuwa tazo maka, wannan shi ne halin mumini, Allah SWT yace

وَاَطِيۡعُوا اللّٰهَ وَرَسُوۡلَهٗ وَلَا تَنَازَعُوۡا فَتَفۡشَلُوۡا وَتَذۡهَبَ رِيۡحُكُمۡ‌ وَاصۡبِرُوۡا‌ ؕ اِنَّ اللّٰهَ مَعَ الصّٰبِرِيۡنَ‌ۚ...

Don haka kayi hkr da yadda kaddara tazo maka kaci gaba da addu'a, sannan ka sani life without problems, is like school without classes you will never learn anything ka kwana da sanin wannan....

Tashi kaje, addu'a ta na nan gareka har zuwa randa kasa zata rufe min ido, bazan daina maka addu'a ba, In sha Allah.

Daga nan ya mike ya tafi yana mai jin zuciyarsa na dan rage zafi.....

Dama wa'adin da Abie ya diba wa Muraydah already ya cika, kuma har Ammy ta tambaye,

Muraydah batayi k'asa a gwuiwa ba, wajen gayawa Ammy Wanda take so, wato Sameer, ba tare da tayi istiharan da Abie yace tayi.....


Hakan yasa ya aiki Ammy wajen kira masa ita Muraydah, duk da yaji abunda tace, amma yana son ya jinkirta ko wani alkhairin zai biyo baya, baya son ayi gaggawa akan lamarin, duk da dai Ammy bata kai ga gaya masa akan w wanda ita Muraydah ta zaba a matsayin miji....


*** *** ***

Muraydah ce gurfane a gaban Abie kasa a sunkuye, tayi tsumu-tsumu kaman mara gaskiya...

"Kaman dai yadda na sani kin fadawa mahaifiyarki Wanda kika zaba, duk da bata kai gaya min ba...

Sai kuma yau wassu mutane, bazan ce wassu ba, don shima uba yake a gareki tunda abikina ne tun a makaranta, muka samu aiki tare, daga karshe Allah ya raba ta hanyar transfer, yanzu kuma ya sake hadawa...."

Fattt, fatttt haka kirjin ta yake bugawa tunda taji Abie ya fara magana, maganan Abie ne ya katse mata tunanin ta takeyi...

"Alhaji Abubakar Mukaddas, bata san dalili ba, haka kawai taji gabanta ya fadi a ambaton sunan da Abie yayi...

"yazo akan akwai yaron sa daya ganki yana so, shi ne suka zo tambaya, bazan yenke hukunci ba tunda bansan me kika cewa mahaifiyarki ba, hakan yasa nace zanyi shawara....

Na kara miki lokaci, kije ki sake nazari da tunani akan mutum biyu, kiyi istihara akan su kiji akan waye hankalin ki yafi karkata....

Kar kibi son zuciya, zai kaiki ya baroki, karki manta maganganun dana fada miki a baya...

Kiyi tunani, kiyi nazari kiyi addu'a, Allah ya zaba miki mafi alkhairi tashi ki tafi......

Mukewa tayi ta tafi, banda mita babu abunda takeyi, tsinuwa kuwa ta yi wa Wanda aka zo ta dalilinsa yafi cikin roka, don cewa tayi shi ya ja mata, yana neman rabata da masoyin ta Sai dai wane ne yayi gigin rabata da abun kaunar ta Wallahi zai gommace kida da karatu, don jikinsa zai gaya masa sai ta masa *GASHIN K'ANK'ARA* (My next novel 💃💃💃) kai zata na iya kashe shi ba abunda ya mata zafi a yadda take jin son Saleem Wallahi bata ga wani mahalukin daya isa ya rabata dashi ba, Wallahi ko kaddara ce da zata ganta sai sunyi kanta waye, don ko gidansu ta shirya bari muddin aka ce za'a rabata da Saleem.

Kwafa tayi tuna wai Abie yace tayi istihara a fili ta furta "Abie kullum sai kace istihara istihara, nikam ba wani istiharan da zanyi gaskiya....

Wata zuciyar ce ta ce mata" to ke ki gwada istiharan mana kiga me zai faru," kaman bazata yarda ba, sai kuma ta gyada kai.....

Kudan ZumaWhere stories live. Discover now