Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KjdJvmEU9y22BLwHpmN0KA
'''Ko juti fuu wodi kerol, wala ko warani njode, ko taga fuu reai, to a wadi munyal a yottoto kerol majun……'''
P. 4
................ Hakan yasa cikin iyayen Alhaji Abubakar Mukaddas Alkali shi kadai ya rage, domin su dai Yayansu ne suka ja musu. Dan kuka kenan Mai jawa uwarsa jifa.
Bayan bayar da jinin mahaifansu sai kudi suka fara shigowa musu ta ko wani bangare saboda jini Mafi daraja da suka bayar.
Sai suka dago gidan Abba (Alhaji Abubakar Mukaddas Alkali) da zama, takunkumun da ya daura musu ne yasa ba shiri zaman ya ta6ar, domin ba lallai su juri wannan takuruwar ba, beside suna kallo Suma sun tsaya da kafafun su a yanxu, sun Kai matakin mallakar gidaje moto ci nasu na kansu.
A zaman da sukayi a gidan shi ne ya fahimshi halaye mugaye a game dasu, sai da yayi kuka ya Kuma tausayawa abokan nashi da yanzu basa Raye sai dai matsalar itace basu bar Yaya na gari ga alummar annabi ba, don zai iya cewa annoba suka mutu suka bari.
Zuwa wannan lokacin Haydar Yana final Year a jamia, ana ganawa Kuma ya fitar dashi wajen saboda fahimta da yayi tamkar Yana son bin ayarin su, domin dai sarki yawa yafi sarkin karfi, don a wannan lokacin Haidar ya dan fara biye musu wajen neman mata, saboda kwadai ta masa hakan da suke a kullum, kafin ya dawo Abba ya Gina masa asibiti nashi na kanshi, nan ya saka masa ma'aikata masu kula da asibitin, shi Kuwa bai dawo ba sai daya Kai matakin PhD duk akan bangaren mata, daga nan ya tattaro ya dawo kasar sa ta haihuwa, yaji bakin cikin ganin su Saleem Basu canja ba sai ma gaba da abubuwan su sukayi, domin shi dai barin da yayi cikin su na lokaci ya taka muhimmiyar rawa wajen gyara shi da Kuma ganar dashi.
Sai ya dawo kyamatar Zina, a Egypt yayi karatu dake kasar akwai musulunci da kansa yaje kotun musulunci ya amsa bulalin da aka tanadar wa mazinaci Amma Wanda baiyi aure ba, ko Abba bai sani yayi jinyarsa shi kadai ba tare da sanin wani na gida ba, Yana warkewa kuwa yayi Shirin gidan, don dama ya gama karatu yayiwa Abba karya me akan zai jira wata takarda.
Ba takardan da zai Jira kawai Yana so ya koma gida fresh ne da sabon rayuwa.
Domin tunda ya zauna a kasar yake tunanin wannan rayuwar daya biyewa su Saleem sukayi, tunda ya zo kasar bacci Mai Dadi ma gagaransa yake. Amma a ranar da aka masa bulalin bacci yayin mai nauyi Mai dadi baccin daya jima baiyi irin sa ba, duk da ciwon dake jikin sa. Daga nan Yaci gaba da tuba da alkaqawarin bazai koma ga zunubin ba.
Domin Kuwa dama _Anniyatu Alla ya udu ila zambihi (Kuma yayi niyya bazai koma ga zunubin ba_
*Ya Kuma Yi alkawarin barin Zina kaman yadda ya bar cikin mahaifiyarsa bai koma ba, kaman yadda ya bar nonon mahaifiyarsa bai Kara sha ba*
Yana dawowa bada jimawa ba ya soma aiki a asibitinsa, a gefe guda Kuma Yana hadawa da kasuwan ci, da hannun jarin da ya zuzzuba a kamfanoni da dama.
Kafin kace kwabo ya tsaya da kafafun sa ba tare da sanin kowa ba, domin dai Mai nema Yana tare da samu, domin Allah ya ce tashi in taimakeka.
Haydar cikekken saurayi ne mai kekkyawar fuska da kererren kira na jiki saboda motsa jikin da yakeyi akai a kai Kuma ba dare ba Rana.
Dogo ne shi fari kakkarfa mai matsakaicin jiki, haka Kuma mutum mai zuciya da rashin yawan magana.
Mutum Wanda abun hanun mutum bai dameshi, mutumin da bai damu da shiga damuwar wani ba kaman yadda baison a shiga nasa Domin shi haka Allah yayi shi baya son shiga abunda bai dameshi ba, baya kula abun da bai kula kaman yadda baya hankali akan abunda ba na shi ba. Wannan shi ne *Dr. ALIYU ABUBAKAR MUKADDAS ALKALI*
Wanda mutane ke masa kallon da ba halinsa ba. Saboda mutane da yake zama dasu, domin bature ya ce Show me your friend and I will tell you who you are, a yayinda bahaushe yace Abokin 6arawo 6arawo ne.....
YOU ARE READING
Kudan Zuma
RandomWannan littafi labarin wata yarinya ne akan wata yarinya mai suna Muraydah, wacce ta bijirewa umarnin iyayen ta akan auren saurayin da iyayen basu da tarbiyarsa ba, ita kuma ta nace har takai baban ta ya cire yayi furucin cire hannu a kanta, Wanda d...