*NYAKU*
_(K'udan Zuma)_*Na*
_Sadeeey ce, Yar Gatan Royal Star_
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
P. 5
*"Majjere ndun nyimre nyimbbi nyimbbini bawo mun, humtata humtinta sonahumare, Majjere defata defnata nyamnata sakko harna majjere halkere nwembere, ndoggu mdoggina bandun yaha yahina bandum..... "*
P. 5
................ Shi Aboki tamkar tauraro haka yake hasakawa acikin rayuwar ka, haka kuma tamkar Tambari ne shi, mutane ne basu gane illar abokin banza ba.
Da kasan rawan da aboki yake takawa a rayuwarka da ka nutsu ka san abokin daya kamata ka za6a.
Shi Aboki na gari tamkar mai saida turare haka yake, kayi kokarin za6awa kanka aboki na gari domin abokin 6arawo, masu Iya magana suka ce 6arawo ne.
*MURAYDAH*
shigowar Ammy kenan dakin Muraydah ta sameta kwance kaman kullum tana Sana'a ta danna danna waya, domin Muraydah na cikin yan matan da sukayi amanna da social media dama wayan kanta....
Bata da aikin daya wuce danna waya, irin wannan illar Ammy ta guje mata tayi kokarin hana Abhie saya mata, amma inaa yaki.
Gashi nan aikin karankanta na kokari gagaranta, tana nan kwance kaman kashin maciji ba taki ba magani....
Cikin jin haushi ammy ta make kafarta kana ta ce "Wallahi you will never change Muraydah, nayi Iya kokari na ganin kin canja but I can't, kin dauki rayuwa da zafi but zaki sha wahala, mutum kaman Ruwa baki da aiki sai kwanciya da danna waya, dama. Don irin ku nasara ya kirkiri waya, Don Wallahi kuna tare da aiki ja...... Zumbura baki Muraydah tayi tun lokacin da ammy ta bugi kafarta, sake yamutsa fuskarta Muraydah tayi jin Ammy taci gaba da fadin,
"Kekam na rasa wace irin Mace za'a tayar, bazan miki baki ba, amma ina fatan ki zuwa gidan da zaki gyaru (kashhh sai dai abunda ya dami uwa a cikin rai akan Yayan ta tamkar ciwo ne, domin kuwa Ammy bata San hakan zai iya faruwa acikin rayuwar Muraydah ba? Wannan babban kuskure ne da iyaye musaman mata ke aikata wa na fadan magana ba tare da tunanin bakin uwa yafi kafin takwabi, Wanda nan da nan yake Iya samun da especially Mahaifiya. )
*Note*_Ke uwa ce dole ne kisan irin kalmomin da zasu na fito wa daga bakin ki, domin kuwa kuskuren furuci kadan zakiyi kiga ya kama yaro. A matsayin ki na uwa Mahaifiya ki sakawa bakin ki linzami, domin kuwa gaskiya ne da aka ce every mother is a woman, but not every woman is a mother, ki zama uwa ta gari wacce a koda yaushe Yayan ki zasu yi alfahari dake, kasancewarki uwa haka kuma makaranta, kar mummunan magana tana fito wa daga bakin ki, kada ma ki vari bakin ki ya saba da hakan, a ko da yaushe Addu'a da fatan Shiriya ya dinga fitowa daga bakin ki ke uwa akan Yayan ki da Allah ya baki amana, UBANGIJI yasa mu dace........_
"Chaiiiii ammy kekam kullum sai kiyi ya fada, to yanzu kuma me kike so?
Muraydah ta fada a yanayi na shagwaba...."Uhmmm shi kenan ai kije Abhie na ki ranki ta fada tana juyawa, fuskarta na nuna damuwa a game da hali na Muraydah din.....
Mai makon ta tashi daga wannan lokacin, Amma ina ni banga ta tashi ba sai ma wayanta data ci gaba da dannawa, Wanda ya kara dulmuyar da ita cikin mantuwa, daya kai har ammy ta sake dawowa dakin, don sake Kiran ta a karo na biyu...
Wannan karon cikin bacin rai ta sa hannu ta kwace wayan tana mai buge hannun ta, data kawo ciki hanzari ganin an wafce wayan. Shagwabae fuska tayi ganin ammy ce.
Cikin hanzari da zallan 6acin rai ta ta tare ta, tare da fara fadin fadi........
Manage please....
YOU ARE READING
Kudan Zuma
RandomWannan littafi labarin wata yarinya ne akan wata yarinya mai suna Muraydah, wacce ta bijirewa umarnin iyayen ta akan auren saurayin da iyayen basu da tarbiyarsa ba, ita kuma ta nace har takai baban ta ya cire yayi furucin cire hannu a kanta, Wanda d...