Chapter 06

130 7 0
                                    


Chapter 06

*A Mother alone*

Al'ada da ake yi da jimawa wanda ya fi ƙauri tsakanin Hausawa da Fulani inda za ka ga idan mace na jinya za ta koma gidan su har sai ta warke, Al'ada ce da kwata-kwata bai kama hankali ba. Idan ina da lafiya mu na tare amma idan jinya mai tsanani ya kamani to sai dai na koma gida wannan kwata-kwata bai dace ba. Amma Alhamdulillah tunda yanzu neman ilimi da ake ya sa an samu massive chanji sosai.

Duk jinyar Innayi da ta yi a asibiti 'yan uwanta ne su ka biya kuɗi su ka kuma yi ma ta hidima. Buba kam dama fama ya ke da kan sa balle ma ace zai iya taɓuka wani abu.
Daga wajen Alhaji Nuhu mijin Halimah ake tunanin samun kuɗi sai dai ko gaisuwa bai zo ya yi ba balle ya kawo wani abu.
Haka Innayi ta yi kwana ashirin da bakwai a asibiti kafin aka sallameta. Zuwa lokacin ta warke sosai kuma ta yi kyan gani, 'yar ta Raudha ma na nan cikin ƙoshin lafiya madaran da ta ke sha sosai ya karɓeta...

Bayan Innayi ta dawo aka shiga wani sabon rayuwa. Sosai aka ja ma ta kunne a asibiti akan ta rage ayyukan da ta ke yi idan har ta na son ta samu lafiya. Hakan ya sa ta ajiye sana'ar ƙosai da daddawa a lokacin, sai dai fa abubuwa ba su zo ma ta da sauƙi ba. Domin sai da ta ƙwammaci gara ta koma sana'ar ta saboda asirinta ya rufu da babu da ta ke fama da shi.
Mijinta Buba kam tun da ya ji ya fara samun sauƙi ya watsar da maganar komawa asibiti. Dama kuma rashin lafiyar Innayi ya ɗauke hankalin iyalin sa daga batun ciwon idon sa.

Raudha Auta, Raudha 'yar gata, Raudha Alkhairi, Raudha haske, kaɗan daga kirarin da Innayi ke wa 'yar tata kenan. Duk da kuwa a zahiri Raudha ba cikin gata ta taso ba, asalima duk cikin yaran Innayi ita kaɗai ce ba a yanka ma ta ragon suna ba balle har ayi wani hidiman suna. Hatta kayan sawa duk kunce ake sa ma ta sai da ta kwana biyu a duniya kafin aka samu kaɗan daga cikin ma su zuwa gaishe da Innayi su ka zo da kyautan kaya wa jinjira.

Wata uku da haihuwar Raudha Buba ya makance. Ya fara da ganin biji-biji ne, bayan kwana uku idon ya dena gani gaba ɗaya. Tashin hankali ya shiga wannan gida domin Buba tamkar mahaukaci haka ya dawo lokacin da idon sa ya makance, faɗa ya ke da kowa tareda baiwa iyalensa laifi bisa makantar sa. Anyi ƙoƙari an tara kuɗi an maida shi Kano amma abin duk maganar kuɗi ne, sannan bayan kuɗi an nuna mu su ko da anyi ma sa aikin ba su da cikakken yaƙinin idon sa zai koma gani kamar da.

Kuɗi su ka yi wahalar haɗuwa har ta kai 'ya'yan sa su ka yi shawaran sai da ɗaya ɓangaren gidan sa wanda bai ƙarisa ba. Buba yai fir akan shi ba za a saida ma sa gida ba.  Daga ƙarshe aka nemo bashi da ƙyar akan za a koma da shi a ma sa aiki. Buba ya ce ya fasa, wai an ma sa kwatancen mai magani a ƙauyen Takadunga chan zai je. Akayi-Akayi da shi ya ƙi zuwa asibiti dan haka aka barshi.
Daga ƙauyen Takadunga sai da ya ziyarci ƙauyuka biyar amma still ba maganar sauƙi. Kuɗin da aka ci bashi dan a ma sa aiki a asibiti kaf ya kashe su wajen ma su maganin gargajiya. But still ba abinda ya chanja Buba ya zama makaho.
Da ya ga ba shi da sisi sai ya haƙura ya koma zaman gida. Saboda zuwa aiki ba zai yiwu ba ya sa ya yi voluntary retirement ya cigaba da jiran kuɗin pension.

A wannan lokaci ne Buba da ya ke ji da ƙarfi da kuma kyau da  kwarjinin Fulani ya koma abun tausayi. A lokacin ne ya san cewa gani rahama ne na Ubangiji. Gashi dama lokacin da yana da ido bai jawo kowa ajikin sa ba hakan ya sa yanzu da ya rasa ido ya koma bashida kowa, bashida aboki da zai kira na shi sannan bashi da ikon gane fari ko baƙi.

Indo ce ta fara sarewa da shi. Ganin ga Makanta da baƙin hali ya sa ta ce ba za ta iya zaman ba ta nemi ya sawwaƙa ma ta. Sai da aka kai ruwa rana kafin ya amince ya sawwaƙa ma ta. Da za ta tafi ta ɗau yaranta biyu ta yi gaba da su. Ta sani ko ta barsu ma wahala za su sha, Harga Allah ta san Innayi za ta iya riƙe amanar su amma kuma itama fama ta ke da na ta 'ya'yan kuma ba wani samu ta ke ba shiyasa ta zaɓi tafiya da yaran.

RIBAR UWA (Hausa novel)Where stories live. Discover now