Chapter 11

127 9 0
                                    


Chapter 11

*An evil daughter inlaw*

***

Da ke Huwaila ba ta san kan Asibitin ba da ƙyar su ka samu su ka yi gwajin bayan anyi ta mu su kwatance. Daɗin abin Likitan da yai gwajin yana jin Hausa ganin da Huwailan da Innayin duk sammakal ne shiyasa ya mu su bayani dalla-dalla yadda za su gane tareda cewa su dawo washegari su karɓi result ɗin su kaiwa Likitan da ya turo su. Innayi ta ma sa godiya.
Lokacin da za su fita ne Likitan ya ce "Mama ina yaranki  maza ne su ka barki kina yawo ke ɗaya?"

Innayi ta ce " 'ya ta ba ta ƙasar, tana karatu a Hawad"

"Hawad?" Likitan ya maimaita dan bai gane ba

"A ƙasar Amelika ta ke, makarantan koyon likitanci ne irin na ku" tana maganan ne cike da alfahari, idan akwai wanda ta ke alfahari da shi cikin 'ya'yanta to Raudha ne.

Likitan yai murmushi tareda addu'an Allah ya sa 'yarta ta gama karatu lafiya. Bayan fitan su da ɗan mintina yana duba computer kwatsam sai ƙwaƙwalwarsa ta ankaro ma sa ma'anar abinda Innayi ta faɗa wato Hawad, ashe Havard ta ke nufi, yai dariya yana ƙara maimaita sunan...

Bayan sun dawo gida Huwaila ta dafa mata spaghetti sannan ta tafi, kafin ta tafi ta ce " Inna sai dai fa ki ƙara haƙuri saboda gaskiya sha'anin Anty Fa'iza sai ahankali. Ba ta da daɗin sha'ani"

Innayi ta ce " ba komai, na gode Allah ya saka da alkhairi"

Da ƙarfe biyu da rabi Faiza ta dawo gida, ko ta kan Innayi ba ta yi ba. Innayin ne ma ta fito tana ma ta sannu da zuwa wanda ta amsa a fiska ɗaure.
'Yarta Mufeedah ta fara tambayar kowaye Innayi. Da ke rayuwar ƙarya su ka ɗauka wa kan su, da Hausa da Fulatanci duk babu wanda su ka koyawa Mufeedah, turanci su ke mata kuma dashi ta tashi ɗan gara Hausa wani abin ta na ɗan ji amma ba ta iya mayarwa.
Maimakon Faiza ta gaya ma ta ko wacece Innayi sai ta ce ma ta ta tambayi Daddyn ta idan ya dawo.

Yarinyar ta kalli Innayi ta ce "who are you?"
Innayi ta ma ta murmushi ta ce "Allah ya miki albarka"...

Da Huwaila ta shigo da yamma ta ma ta bayanin ta dafawa Innayi spaghetti da rana, Faiza ta haɗe rai ta ce kar ta ƙara yi mata girkin da ba ta sa ta ba.

"Anty Faiza na ga ba za ki dawo ba sai..."

"Huwaila ba na son shishshigi. Ki yi abinda na ce kawai"

Huwaila ta ja bakinta ta yi shiru...

Ƙarfe shida saura Idris ya shigo gidan amma bai leƙa Innayi ba sai da ya dawo daga sallar Isha.

Tambayarta yai ko ta je asibiti, ta gaya ma sa yadda su ka yi da Likita.  Ya ce Allah ya ƙara lafiya.

Yau dai tuwon Semovita da miyar kuɓewa Faiza ta yi, ta kawo wa Innayi abincin ba yabo ba fallasa.

Ko kafin su kwanta sai da ta yiwa Idris ƙorafi akan ita fa ya san yadda zai yi Innayi ta tafi ƙarshen sati dan ba za ta iya ɗawainiyar Uwar sa ba...

***

Washegari still Huwaila da Innayi ne su ka je su ka ƙarɓi result su ka kai wajen Likita, amma da ke ba su zo da wuri ba dole sai tafiya su ka yi akan washegari za su dawo.

A yammacin ranan ne kuwa Raudha ta kira Idris, da farko Ado ta kira shine ya sanar ma ta abinda ke faruwa, ta ji zafin rashin gaya ma ta da ba su yi ba tun farko, shine ta kira Idris ɗin.
Sun jima suna tattaunawa kafin daga baya ta ce idan ya koma gida ya haɗata da Innayi...

Daren ranan bakin Innayi har kunne saboda farin ciki. Sosai su ka yi taɗi da Innayi, har ta ke sanar da ita aikin da ta ke yi a free time ɗin ta. Innayi ta rinƙa saka ma ta albarka. Bayan sun gama wayan ne Idris ya tambayeta yadda su ka yi a Asibiti ta sanar da shi ya ce gobe zai haɗa ta da wani saboda ya ji bayanin da Likita zai yi. Innayi ta gyaɗa kai kawai...

RIBAR UWA (Hausa novel)Where stories live. Discover now