Chapter 13
*condolence*
***
Dogon suma Raudha ta yi dan duk taimakon gaggawa da ya bata dan ta farfaɗo ba ta farfaɗo ba hakan yasa ya ɗauketa ya wuce da ita wajen motar sa yayinda Emilia ta bi bayan sa saboda itama ta biyo bayan Raudha ne dan ta bata jakarta da kuma wayarta da ta baro shine ta ga abinda ya faru.
Bayan ya shimfiɗa Raudha a kujerar baya yai wa Emilia nuni da ta shigo gaba, ba ta ɓata lokaci ba ta shiga ciki da sauri...A asibitin ma sai da ta kai kusan awa uku kafin ta farfaɗo, bayan wasu daƙiƙai da farfaɗowan ta ta kama kuka. Kukan ne ya ja hankalin Emilia da ke zaune gefenta tana latsa waya. Ta yi ta yi ta sanar da ita abinda ya faru amma ba ta gaya ma ta ba illa cewa da ta ke yi "i want to go home"
Emilia ta ɗau wayarta ta kira wanda su ka zo tare. Sallah ya fita yi amma da tare su ke zaune da shi a ɗakin. Bayan ya sanar da ita yana hanya ne ya sa ta kashe wayar ta cigaba da kallon Raudha da ke kuka, ba ƙaramin tausayi ta ba ta ba domin ta san duk abunda zai sa Raudha kuka haka to ba ƙaramin abu ba ne.
Ba wai sun shaƙu da Raudha ba ne sosai amma watan da ya wuce da ƙanwar Emilia ta mutu ta je ta ma ta ta'aziyya har gida ita da Azhar hakan ya sa ta ke ƙara ganin Raudhan da daraja, wannan ya sa su ka fara ƙawance.Kafin Prof Bamalli ya iso Raudha ta cire ruwan da aka ɗaura mata wanda saura kaɗan ya ƙare. Ƙoƙarin tashi ta ke yi Emilia ta tareta.
"Emilia please let me go" ta faɗa da dasasshshiyar muryaEmilia ta girgiza kai. Raudha ta fara ƙoƙarin tureta amma ina Emilia ta fi ƙarfinta. "Rodha calm down, professor Bamly is coming"
Ta girgiza kai tana cigaba da tureta, da ƙyar Emilia ta samu Raudha ta nitsu ta zauna a bakin gado ta cigaba da kuka.
Turo ƙofar da aka yi ya sa Raudha ta ɗaga idonta ta kalli wajen ƙofar. Professor Bamalli ne ya shigo tareda sallama, ba ta iya amasawa ba sai ma kawai ta sunkuyar da kanta.
Emilia ta kissing goshin Raudha ta ce "take care dear, i'll call you later"
Bayan Emilia ta fita ne Prof Bamalli ya jawo kujera ya zauna yana fuskantar Raudha.
"Raudha" ya kira sunan ta a hankali. Ta ɗago ta kalleshi na ɗan daƙiƙu kafin ta sunkuyar da kai ta cigaba da sheshsheƙar kuka.
"Na san ke musulmace Raudha, kuma kin sani yarda da ƙaddara yana ɗaya daga cikin cika-ciken musulunci. Saƙon mutuwa akwai ciwo, musamman idan wanda ya rasu makusancin ka ne. Sai dai Allah da ya haliccemu shi ya tsara wa kowa adadin lokacin da zai yi a doron ƙasa, hakan ya sa idan lokaci yai ko second ɗaya ba za ka ƙara ba"
Raudha ta ɗan sassauta kukan na ta tana sauraron sa. Prof Bamalli ya cigaba.
"Innayi mahaifiyar ki ce ko?"
Maimakon ta bashi amsa sai ta kifa kan ta a gwiwowinta tana ƙara sautin kukan ta wanda ke ratsa zuciyar mai sauraro.
"A maimakon kuka Raudha addu'ar ki ta ke buƙata yanzu, ki daure ki yi ma ta addu'a"
Ta ɗago ido da sauri ta ce "Sir ba ka san Innayi ba ne, ba ka san irin wahalhalun da ta sha a kan mu ba. Bai kamata ta mutu ba, bai kamata ta tafi ba tareda na cika alƙawurran da na ma ta ba. Bai kamata ta tafi ba tareda..."
"Manzon Allah da ya fi kowa daraja ya bar duniya Raudha. Babu wani da zai rayu ba tareda ya ɗanɗani zafin mutuwa ba, kisa a ranki mutuwa ita ce hutu gareta. Iya lokacin da aka ɗibar ma ta kenan a duniya. Raudha a duk inda mahaifiyar ki ta ke Insha Allah tana cikin farin ciki" maganar sa ya katseta.
Hawaye kawai ta ke yi tana yi tana goge majina da bayan hannun ta. Hakan ya sa Prof Bamalli ya ciro handkerchief ya miƙa ma ta.
Nasiha ya cigaba da yi ma ta bayan ya lura ta ɗan nitsu. Ya ƙare da ba ta labarin na sa mahaifiyar.