Chapter 15

339 23 4
                                    


Chapter 15

Epilogue

Rasuwan Innayi ya zo da sauyi da dama, da masu daɗi da marasa daɗi. Kuma dukkan 'ya'yanta babu wanda bai ga darasin rayuwa ba.

Raudha tun tana irga watanni da aure har ta fara irga shekaru. Kaman Innayi itama bata samu haihuwa da wuri ba. Bata sa damuwa a ranta ba dan addu'ar ta shine Allah ya bata 'ya'ya masu albarka, 'yan'yan da za su jiƙanta, su ji tausayinta, 'ya'yan da za su zamowa musulunci abun alfahari.
A ƙarshen shekararsu ta uku da aure ne ita da Prof suka tafi aikin Hajji. Aikin Hajjin da sai wanda Allah ya kira yake zuwa. Duk yadda ita da Baffah suka ci burin kai mahaifiyarsu Hajji, Allah bai ƙaddara hakan ba.

Bayan dawowarsu ne suka shirya zuwa Nigeria sai dai laulayin ciki da ya sata a gaba yasa suka janye tafiyar zuwa wani lokaci.
Tun daga laulayi Raudha ta fara jin tsoron haihuwa, take kuma jinjinawa Innayi da ma duk wata UWA. Ashe ciki da haihuwa babu sauƙi, a hakan ka gama haifan yaro ko yarinya su zo su muzguna maka ko kuma su ɗaukeka ba a bakin komai ba.

Laulayi tun watan farko har sai da ta shiga wata na biyar kafin ta fara jinta garau. Tana samun kulawa sosai a wajen Mijinta da Umma. Duk wani aure ana samun saɓani itama natan akwai, sai dai soyayya, haƙuri da addu'a su suka zaunar dasu lafiya ta inda ba a taɓa jin kansu ba. A yayi yawa shine ka ga anyi fushin kwana biyu amma yawanci a yini ake faɗa a kuma shirya.

Musabbabin son zuwanta Nigeria ma saboda Idrissa ne. Har ga Allah bata masa fatan da zai samu iftila'in da ya faɗa ma sa ba sai dai dama hakan yana daga cikin ƙaddararsa. Prof ya riga ya ɗage tafiyar sai bayan ta haihu amma ta so ta je Nigeria ta ga yadda rayuwa ta juya da ɗanuwan nata...

Tun bayan auren Raudha Idris bai sake zuwa Misau ba. Kunyar 'yanuwansa ya ke ji, yana kuma ƙoƙarin haɗa kuɗin da ya ci. Ita kam Faiza ko ajikinta dan nunawa ta yi ba ta damu ba gida ne dai za su tare tunda an gama. Ba yadda ya iya haka suka koma gidan watanni goma shaɗaya da rasuwan Innayi kenan.
Komawarsu ba da jimawaba aka yiwa Idris transfer zuwa Maiduguri, haka ya tafi ya bar Faiza a Bauchi duk ƙarshen wata yana zuwa hutu.

A wani hari da 'yan Boko Haram suka kai wa bankin da Idris yake aiki ne iftila'i ta faɗawa Idris. Bomb aka jefa musu, lokacin da bomb ɗin ta tashi, ta yi awun gaba da rayukan wasu yayinda wasu kuma suka rasa wani sassa na jikinsu ciki har da Idris wanda ya rasa hannunsa na hagu.

Da farko ma da aka ji labarin an ɗauka ya rasu sai daga baya aka gane da ransa. Daga Maiduguri aka fara jinyarsa kafin su Ado suka dawo da shi Bauchi ƙarshe dai Ado da Iro ne su ka sai da gidansa aka yi duk wani hidimar asibiti da shi. Sai gashi Idris ɗan gaye ya koma mai hannu ɗaya, ɗaya hannun dumgulmi ne kawai a wajen kafaɗarsa. Tashin hankali Idris ya shiga ba kaɗan ba, ta ina zai fara rayuwa a haka.

Bayan an sallameshi Misau aka wuce da shi, ɗakin zaure aka bashi dan ɗakunan ciki an gyara an sa haya a ciki.  Tun yana asibiti ya fara ganin izina domin matarsa Faiza 'yar ƙwalisa da ya ke ji da ita kamar zinare ko diamond ita ne dai ta fara nuna masa ƙyama saboda yanzu ya koma mai hannu ɗaya. Ya kirata ta zo Misau amma ta ce ba za ta iya zama a Misau ba ga kuma aikinta. Tunda ya bar Bauchi watanni huɗu da yai a Misau ko mai kamar Faiza bai gani ba. A wata na biyar ne sai ga ɗan saƙo wani ƙaninta wai ya zo karɓan takardar sakin Faiza. Ya ɗau waya ya kira Faizan dan ya ji dalilin wannan saƙo.

"Kai ma Idris tun daga asibiti ya kamata ka sani aurenmu ya ƙare, kai ne dai ba ka sa shi ya zama offficial ba. Na ɗauka rashin zuwana Misau zai sa ka gane amma ka ƙi, yanzu kam haƙurina ya ƙare ka turo min takardata"

Tsabar takaici kasa magana yai sai hawaye.
Ina I love you? I'll never leave you, I promised to be with you till the end of my life ɗin su ka shiga?.

Dama soyayyar gaskiya ce ke tsayawa through trying times, through thick and thin. Kwata-kwata ba su gina soyayyarsu tsakani da Allah ba.
Ita Faiza ta ga ɗan farin bafulatani zubin larabawa shi kuma Idris ya ga wayayyiyar mace 'yar masu kuɗi.

RIBAR UWA (Hausa novel)Where stories live. Discover now