*The bride*Muhammadu Jo'o shi ne ɗa na huɗu a gidan su ya na da yayye mata uku da ƙanne maza uku da autar su Faɗimatu. Da ke auren wuri ake yiwa yara mata a ƙauyen na su shiyasa bai wani shaƙu da su ba, lokacin da ya taso an aurar da 'yar farin su Maimunatu mai bi mata ma ba a jima ba aka aurar da ita. A taƙaice dai ya taso da tsananin son 'yar ƙaramar ƙanwar na su Faɗimatu wanda kuwa duk gidan sun fi kama da juna. Sai dai shekarar Faɗimatu shida a duniya ta rasu sakamakon zazzaɓin cizon sauro.
Muhammadu kowa ya shaideshi wajen kyawawan halayen sa da jajircewan sa wajen harkan noma. Yayinda tsaransa ke kora shanu su na tafiya da su Kudu, ma su Noma kuma na saida gonakin su suna shiga birni , shi ya jajirce ne wajen noma sosai yana ƙoƙarin inganta rayuwar sa da ta ƙannen sa. Domin a shekarunsa shashida Allah yai wa mahaifin su rasuwa da ake kira da Baffa Jo'o. Daga wajen mahaifiyar sa ya samu umurni a kan yai aure saboda ya zama yana da iyalin sa, dan ya fi jin daɗin kula da ƙannen sa sosai.
***
Aminatu 'ya ce ga Malam Isiyaku Chadi. Malam Isiyaku da iyalen sa su ka zo ƙauyen Tunfure kusan shekaru ashirin da su ka wuce. Ilimin addini da Malam Isiyakun ke da shi ya sa ya samu gindin zama a ƙauyen Tunfure ba tareda mutanen ƙauyen sun damu da rashin sanin asalin sa ba. Malam Isiyaku ya kan ce daga chan gabashin Chadi ya shigo Nigeria inda yai ta yawuce-yawuce kafin har Allah ya sa ya samu gindin zama a Tunfure.Kafin Aminatu, Malam Isiyaku sai da ya busine 'ya'ya takwas sannan Allah ya sa Aminatu ta tsaya, kuma har ya rasu ita kaɗaice 'yar sa...
Muhammadu ya yi karatun Allo a gaban Malam Isiyaku ne, inda tun Aminatu na ƙarama ta ke burgeshi.
Yana saurayi ɗan shekara shatakwas Aminatu na shaɗaya aka yi auren su bayan an sha fama kafin Goggo Talatu mahaifiyar sa ta amince, dan a da ta nuna ra'ayin ya auri 'yar ƙanwar ta amma ya ƙi saboda soyayyar Aminatu da ya rufe ma sa ido. Shigowar Aminatu gidan kyawawan halayenta da sanyinta ya sa Goggo ta sake jiki da ita har ta fara son ta. Duk da ƙarancin shekarunta tana bin Goggo sau da ƙafa tamkar Goggo ce ta haifeta.
Shiru-shiru shekara ɗaya ta shuɗe ba maganar haihuwa ta biyu ma ta shige shiru, hankalin Goggo ya tashi ta fara ƙorafi saboda shekaru biyu ba wasa ba ne a wajenta. Ƙwatsam sai ga ciki ya ɓullo, murna a wajen Muhammadu ba a magana, Goggo ma ta yi farin ciki tunda ya tabbata ɗanta na da lafiya. Tun cikin na ɗan ƙarami ya ke ba wa Aminatu wahala har ta kai da cikin yai nisa. Muhammadu ya nemi a kai Aminatu Asibiti a dubata amma Goggo ta ƙi ta ce lalaci da ragonta ke sa Aminatu wannan tsirfe-tsirfen ciwon, a cewarta komai zai wuce idan cikin ya girma. Cikin na girma Aminatu na ƙara bushewa, ta yi wani fayau da ita kamar ba ta da jini. Ana haka aka wayi gari da rasuwan Malam Isiyaku wanda ya kwana lafiya amma ya mutu cikin baccin sa. Aminatu ta yi baƙin ciki da wannan rashin yayinda ta ke kuma fama da nata ciwon.
Sosai Muhammadu ya ke ƙoƙarin kula da ita daidai gwargwado kuma ya damu da rashin lafiyarta. Wani lokacin idan ya shiga garin Misau ya kan siyo wa Aminatu tsire ko balangu ya kawo ma ta a ɓoye ta ci, dan ya kan ji ana cewa idan mace na da ciki ana so ta riƙa cin abu mai daɗi. Har buredi ya ke siyo ma ta idan ya shiga cikin garin na Misau.
Ƙarancin shekaru, rashin jini da cutar malaria da typoid da su ka haɗu su ka yiwa Aminatu katutu a jiki ya sa wata rana da safe Aminatu na daka ta faɗi ta suma. Bayan ta farfaɗo naƙuda ta fara gadan-gadan da cikin ta da ke wata takwas. Muhammadu ya tafi ya nemo Amalenke da za a kai Aminatu asibiti dan hankalinsa ya tashi da halin da Aminatun ta shiga. Lokacin da ya shigo gidan ya samu Goggo na rusa kuka yayinda Delu ungozoma ta ke riƙe da jaririyar da Aminatu ta haifa. Bai bi ta kan jaririyar ba ya shiga ɗaki ya tarar da gawar Aminatu kwance cikin jini ya buɗe zanin da Delu ta rufe ma ta yana ganin yadda matar sa kuma masoyiyarsa ke kwance kamar mai bacci amma kuma ba rai. Ya shiga kiran sunan ta da ƙarfi yana faɗin ta tashi ta ma sa magana. Da ƙyar ƙanin sa Habu da abokin sa Iro su ka zo su ka janyeshi a wajen gawar...
![](https://img.wattpad.com/cover/356680236-288-k563877.jpg)