Chapter 14
*A bride*
***
Jirgin su ya sauka a Abuja wajajen sallar maghrib, a tunanin Raudha a wannan lokacin za su nemi motan Bauchi ko ma na Jos su ka samu su tafi sai ta ga sun nufi cikin gari.
"Hotel a cikin gari akwai tsada" ta faɗa a hankali.
Maimakon Prof ya ba ta amsa sai kawai yai murmushi.
Maimakon Hotel wani Babban gida su ka nufa a Wuse II."Gidan abokina ne, tare mu ka yi karatu" ya faɗa dan ya cire ma ta damuwa.
Matar Dr Ahmad ta tarɓeta da kyau. Umaimah da Dr Ahmad auren haɗin gida aka mu su kuma dukkan su 'yan boko ne, dan Umaimah chartered accountant ce, mahaifin Dr Ahmad tsohon Minister ne wanda ya rasu shekaru kusan biyar da su ka wuce.
Bayan ta ci abinci ta yi sallah su ka ɗan taɓa hira da Umaimah kafin ta kwanta, kusan ƙarfe goma ta gota bacci mai daɗi ya tafi da ita.
Washe gari Dr Ahmad ya ba su Driver wanda zai kai su har Misau. Ƙarfe tara na safe su ka kama hanya, sai a lokacin kuma Raudha ta shiga fargaba, bugun zuciyar ta ya ƙaru. Ina ma za ta iya maida hannun agogo baya, ina ma ko da sau ɗaya ne za ta sake ganin Innayi, tana cikin wannan tunani sai hawaye.
"Ya Allah! Kin manta alƙawarin da ki ka min kenan?" Prof ya faɗa da sigar lallashi
Ta girgiza kai tana ƙoƙarin goge hawaye, tanayi wa su na zubowa.
Nasiha prof ya fara ma ta wanda ya sa dole ta haƙura da kukan. Daga baya ma ta sa earpiece a kunne ta kunna ƙur'ani tana sauraro.
Tun da su ka iso Jos ta fara bacci ba ta farka ba sai da su ka wuce Bauchi har sun kusa isowa Darazo.
"Abban Yusrah ashe na jima ina bacci kaman na ga mun wuce Bauchi ko?"
"Da ba ki tashi ba idan mu ka iso goya ki zanyi na shiga da ke ciki. Ta yi saurin rufe fiskarta da gyalenta tana murmushi
"Ko na gwada ne idan mun je?"
"Kayya ni kam" ta dunƙunƙune gefe tana cigaba da rufe fiskarta...
***
Tunda su ka shiga garin na Misau jikinta yai weak, ba ta yi kuka ba amma sai sauke ajiyar zuciya ta ke a kai-akai. Shekara biyu da sati biyar rabonta garin. Akwai 'yan chanje-chanje da ta spotting tun a hanya. Ta dinga yiwa Driver kwatance har su ka iso anguwar su. A dai-dai bakin layin su motar ta tsaya, da ke yamma ne kwalbatin da ke wajen matasa sun kafa majalisa ana ta gulma, ganin dalleliyar motar da ta tsaya gefen su ya sa gaba ɗaya su ka zurawa motar idanu, suna tunanin wa ke da irin motar a garin.
"Ni da Malam Isa za mu samu masallaci mu yi sallah, idan na dawo zan kira ki sai ki yiwa Yayan na ki magana mu ƙariso"
Ta gyaɗa ma sa kai tana ƙunshe kukan ta.
"Please ban da kuka" nan ma gyaɗa ma sa kai ta yi.
Da Bismillah ta buɗe ƙofa ta fito tana ƙoƙarin gyara gyalenta tareda maimaita Hasbunallahu wa ni'imal wakil a zuciyarta.
"Ehohoho! Wallahi Anty Raudha ce" wani matashi cikin samarin ya faɗa yana tahowa da gudu. Idon matasan chui a kan ƙofar motar lokacin da su ka ga alamun ana buɗewa. Jin Salihu ya ambaci Raudha ya sa su ma su ka sa ihu wasu su ka bi bayan sa.
Salihu kaman wani ƙaramin yaro haka ya rungumi Raudha yana murna. Salihu ɗan Yayan ta Ado ne kuma zai kai irin 14-15yrs haka."Antyn mu sannu da zuwa, sannu mutan America" haka su ke ta faɗa, su ka tisa ta a gaba kamar za su ɗauketa sama, haka su ka rakota har ƙofar gidan na su. Da da ne sashen su za ta fara shiga ta ga Innayinta sai dai yanzu ko ta shiga ba ta san mi za ta tarar ba, ƙila gidan ma ya gama nurƙushewa.
Ta daure ta bi Salihu su ka shiga ƙofar Yaya Ado.