*KOWA YA IYA ALLONSA*.....
*Na SadNaf*
Bismillah Rahmanir Rahim
Page 1
Karamar Wayar vivon hannunta ta kurawa ido tana ta kyalkyala dariya ko kifta idonta bata yi.
Cikin bandakin dakin da take kuwa Jaseem ne dan kimanin shekara hudu da hawaye da muryarsa ta dashe saboda kukan Kiran sunan Aunty Basira da yake tayi majinar dake ta zubo masa ta dame da kukan da yayi fuskarsa duk ta bushe yafi awa daya akan toilet Yana ya gama amma Basira tana can tana Kallo ba kuma jinsa ne ba tayi ba,tana Jinsa sarai,tashi ne ba zata yi ba sai ta gama kallon da take ban da duka da rankwashin da Jaseem ke Sha a hannunta da tsinuwa dan gani take wahalar da ita kawai yake saboda tana aiki a gidansu.
A hankali yayi parking a farfajiyar gidansa dake d'auke da shukokin fulawa da fitilu da suka kawata madaidaicn gidansa da bai fiye girma ba,amma yadda aka fitar da ginin gidan yasa gidan balain haduwa kamar irin gidajen turai.
A hankali ya kashe motarsa Ya jawo brief case din dake gefensa ya fito daga motar Yana yamutsa fuskarsa saboda gajiyar da ya kwaso.
Koda ya doshi cikin gidan ji yake Ina ma Yana shiga ya Samu Nimrah da ba Wanda zai Kai shi Jin dadi,dan bayan ta masa tausa sai ya sauke sha'awar da yake fama dashi da a yanzu ya fara sa shi ciwon Mara.
Tunanin da zai sameta yasa yaji ya harba din dan a balain bukace yake dauriya kawai yake kwana uku ma kenan bai Saka ta a idonta ba Yana fita take dawowa kafin ya dawo ta fice.
Koda ya shiga palon ba kowa sai kamshi turaren wuta dake tashi a palon da dan sanyin Ac da yake a kunne.
Akan kujera ya jefar da brief case dinsa dan yasan Nimrah ma bata nan ya d'auka yau zata dan Jira shi tunda kwana ukun basu hadu ba.
Lumshe idonsa yayi Yana tunanin irin rayuwar da yake da Nimra da a yanzu ya fara gajiya.
"Uwarka zanci idan ka Kara Kiran suna na shege Mai kwala kwalan ido sai na gama Kallona zan zo na wanke ma dan iska"
Maganar daya daki kunnensa kenan daya sa shi Bud'e idonsa a hankali ya mik'e tsaye batare da ya shiryawa haka ba.
Cikin dan mamaki ya doshi dakin Basiran dake can lungun da kitchen yake har lokacin Yana iya jiyo ashar din da take yi.
Jaseem daya fado masa da muryar Jaseem da ya Jiyo yasa yaji gabansa ya fadi.
"Aunty Basira na gama dan Allah ki wanke min"
Ya ji muryar Jaseem na fitowa daga dakin.
Jikinsa rawa ya d'auka ya mik'a hannunsa ya tura k'ofar dakin da aka dan rufo.
A kwance ya hango Basirar tayi rub da ciki da wayarta da ta saka a jikin pillow tana ta kallonta tana dan wasa da kafafunta biyu da ta dage sama.
Tunda ta fara aiki a gidan wanan shine karo na farko da ya zo bakin k'ofar dakin Basirar da bata fi shekara goma sha takwas ba.
Bai manta irin rikicin da yayi da Nimrah akan d'auko Yar aikin da zata na kula da jaseem da ya gaji da d'auko shi daga gidansu ba.
Kansa wani irin Sara masa yayi da yaji Jaseem da yake Jin duk duniya babu tamkar sa duniyar sa na magiya cikin kuka Yana "Aunty Basira zan Sha ruwa dan Allah ki wanke min"
"Wallahi idan nazo bandakin nan ko sai na ci uwarka kaji tsinanan yaro zai dameni,uwarka ta tafi karuwanci da sunan aiki take zuwa ko kwana ba tayi a gida,
Ubanka nan da baya dariya shi ma sai yaga dama yake dawowa gidan,gani sun ajiye mai gadi ta kular musu da gida,tunda ni ba mutum bace ba.
Na gama uban aikin nan nazo zan huta saboda mugunta sai Ina cikin hutawa kake tsirar Kashi wallahi Ina ga dama akan masan nan zaka kwana dan iska kawai Kara Kiran sunana ka gani"