*KOWA YA IYA ALLONSA*....
*Na SadNaf*
Page 5
4WEEKS REVERSE PCOS SYMPTOMS PROMO CHALLENGE wanda za’a fara on 1st January 2024.
Program ne da mukema mata masu CUTAN PCOS. Muna taimaka musu wurin magance wannan CUTAN ta hanyar
1. Basu magungunan cutan
2. PCOS CYSTERHOOD discussion group
3.PCOS and Hormonal imbalance reversal da
4.Fertility Treatment
CUTAN PCOS yanada alamomi kaman:
-Yin kiba ba bisa dalili ba
-Yawan Kasala
-Rashin Bacci
-Gashi a gemu,saman ciki,da saje.
-Kuraje a fuska, baya da kirji
-Rikicewar jinin al’ada:Daina zuwa,ko zuwa sau biyu a wata.
-Zubewan gashi
-Yawan kwadayi
-Yawan Kamuwa da infection akai akai
-Daukewar sha’awa
-Rashin sha’awa
-Motsi a ciki
Dama dai sauran alamonin shi.
Zaki iya tuntuban mu ta WhatsApp a wannan number 08109388227 domin yin register,Ko kuma a shafukan mu na yanan gizo a TIKTOK,YOUTUBE da INSTAGRAM me suna “LafiyarMataTv”*Page 5*
Nana firdausi
Hawaye kawai take zubar wa tunda ta isa gida dan da dukan alamu Hajiyar da take yiwa aiki ta koreta daga aikin.
Dan bayan ta hau Napep din haka ta cigaba da kiranta a waya taki d'auka.
Bata damu ma da raunin da taji ba da zata iya zuwa taga shaidar ciwon da taji amma ta gargade ta akan kar ta sake ta taka kafarta tazo gidanta idan ba haka ba zata sa a saki Karnukan da take balain tsoro.
Yau ban da halin matsi da suke ciki bata Jin zata ma iya jure irin cin Kashi da wulakanci da Hajiyar da take wa aiki take mata ban da yaranta da suka Mai da ita baiwa.
A baya kafin ta gama secondary Mahaifiyarta ke aikatau dan asirin su ya rufu dan mahaifin su ya dade da rabuwa da mahaifiyar su tun ma tana primary.
Su hudu ne Kuma itace babba
Ta taso da tausayin Inna da taci sunanta dan sunan ta aka sa mata shi yasa aka b'oye sunanta ake kiranta da Nana.
Mahaifinsu kuwa watsar da su yayi bai ma san ya suke rayuwa ba.
Dan talauci yasa ya gudu ya bar su bayan ya rubutawa inna saki uku.
Daga baya suke Jin labarin garin da ya gudu yaje anan ya sake Aure ya tattara rayuwar su ya watsar.
Daga lokacin inna ta hau fadi tashi dan ta kula dasu.
Itace cinsu shansu har zuwa suturar su.
Inna ta Sha matukar wahala sosai a kansu.
Da haka yasa take burin girma ta taimaka mata
Inna sai da ta hade gidaje uku da take wa aiki a haka ta samu ta gama primary har zuwa secondary din.
Inna saboda su tak'i Aure dan duk Wanda yazo aurenta zai ce ba zai iya rike mata Yara ba
Ta Maida yaran gidan dangin babansu.
Amma haka inna tak'i auren duk dan ta kula dasu.
Koda ta gama secondary school din sai take ganin lokaci yayi da inna zata huta itama da wanan aikatau din da take.
Dak'yar inna ta barta ta nemi gidan da zaa ringa biyanta da tsoka idan ta fita tun bakwai bata komawa gida sai karfe takwas na dare a gidan wata Hajiya Hauwa ta samu aikin.
Al bashin na da dan yawa sai dai wahalar da take Sha wajen aikin.
Duk da wahalar da take Sha bata tab'a yarda inna ta sani dan tasan halinta zata iya hana ta.
Kaninta Mubarak shi ma haka yake fita buga bugan Allah cikin ikonsa kuwa asirinsu ke rufe dan da irin aikin da inna ta dade tana yi suka mallaki wani madaidaicn gida mai dakuna uku duk da dakunan basu fiye girma ba.