*KOWA YA IYA ALLONSA*....
*Na SadNaf*
Page 7
4WEEKS REVERSE PCOS SYMPTOMS PROMO CHALLENGE wanda za’a fara on 1st January 2024.
Program ne da mukema mata masu CUTAN PCOS. Muna taimaka musu wurin magance wannan CUTAN ta hanyar
1. Basu magungunan cutan
2. PCOS CYSTERHOOD discussion group
3.PCOS and Hormonal imbalance reversal da
4.Fertility Treatment
CUTAN PCOS yanada alamomi kaman:
-Yin kiba ba bisa dalili ba
-Yawan Kasala
-Rashin Bacci
-Gashi a gemu,saman ciki,da saje.
-Kuraje a fuska, baya da kirji
-Rikicewar jinin al’ada:Daina zuwa,ko zuwa sau biyu a wata.
-Zubewan gashi
-Yawan kwadayi
-Yawan Kamuwa da infection akai akai
-Daukewar sha’awa
-Rashin sha’awa
-Motsi a ciki
Dama dai sauran alamonin shi.
Zaki iya tuntuban mu ta WhatsApp a wannan number 08109388227 domin yin register,Ko kuma a shafukan mu na yanan gizo a TIKTOK,YOUTUBE da INSTAGRAM me suna “LafiyarMataTv”*Page 7*
Nimrah
Cikin farin ciki ta isa Asibtin ta wuce office dinsu Kai tsaye.
Itace a morning duty da wata mmn ihsan Hindu Kuma tana off amma tace zata shigo ta tayata,dan haka suke yi,duk da ita tafi taya Hindu yin aikin,duk ranar aikin ta wani zubin Hindun bata fiye zuwa ba.
Basu fiye shiri da Mmn ihsan din ba dan sam tasu bata zo daya ba sosai,suna dan hirar su zata fara nuna musu abinda suke yi bai dace ba saboda shigowar da suke Asibtin Koda ba ranar aikin su ba dan kawai su ga juna suyi hirar duniya da akan irin hirar sun Sha fada da mmn ihsan din kaca kaca,kauyancin ma mmn ihsan din suke gani, Hindu kuwa ta tsaneta ma,ba wani harkar juna ma suke shiga ba,duk ranar da Nimrah ta ga Hindun bata zo ba shine take dan Hira da mmn ihsan din a rashin zuwan Hindun.
Jakarta ta ajiye ta fita bayan sun gaisa da maman ihsan dake ta cike ciken wani files dake jibge a gabanta
Nimrah tana aikin duba patient tana zuba tsaki dan sam bata ji dadin zuwan da Hindu ba tayi ba.
Da ace itaca a off ko night da ta matsa mata akan tazo ta tayata bata san mai yasa take mata haka ba
Tasan dai mijinta ba zai tab'a hana ta zuwa aiki ba dan yadda Hindun ke bata labari mijinta na balain shakkarta bata bashi fuskar da zai Wani rainata
A fadar ta ma ko tambayar shi bata yi idan zata fita unguwa Kuma bai Isa Mata magana ba,sosai take sha'awar irin yadda Hindu ke abinda ranta ke so dan sai take ganin Jameel takura ta yake yi,ita Hindu nada freedom.
Wajen goma ta koma office ta zauna.
Duk rashin ganin Hindu ya sa zuciyarta kunci
Wayarta ta Kara jawowa ta kira lambar Hindun dan tana ta Kiran wayarta bata d'auka
Tsaki kawai take jerawa mmn ihsan kuwa shayinta kawai take Sha tana satar kallon Nimrah da ke rike da waya tana jera tsaki
Alkawari tayi wa kanta akan daina shiga harkar Hindu da Nimrah.
Dan taga alamar sunyi nisa ba Jin kira suke ba,duk wani abu da suke duk bai dace ba,takan yi mamakin wane irin miji Nimrah ke Aure da ya kasa ma bincike ya gano yanayin aikin nasu.
Tasan Hindu cutar da Nimrah take yi amma Nimrah ta kasa ganewa
Maganar Nimrah ya katse mata tunanin da take.
"Mmn ihsan kinga Ina ta Kiran Hindu bata d'auka Anya lafiya kuwa"?
"Tom Yau off take ai akan me zata daga wayarki tana tare da mijinta"
Murmurshi Nimrah tayi tana "Ai ko off muke kinsan sai munzo dan ba zai yu mu zauna gadin gida ba Sanin da nayi wa Hindu kam akan mijinta ba zata ki zuwa aiki ba"
