*KOWA YA IYA ALLONSA*....
*Na SadNaf*
Page 6
4WEEKS REVERSE PCOS SYMPTOMS PROMO CHALLENGE wanda za’a fara on 1st January 2024.
Program ne da mukema mata masu CUTAN PCOS. Muna taimaka musu wurin magance wannan CUTAN ta hanyar
1. Basu magungunan cutan
2. PCOS CYSTERHOOD discussion group
3.PCOS and Hormonal imbalance reversal da
4.Fertility Treatment
CUTAN PCOS yanada alamomi kaman:
-Yin kiba ba bisa dalili ba
-Yawan Kasala
-Rashin Bacci
-Gashi a gemu,saman ciki,da saje.
-Kuraje a fuska, baya da kirji
-Rikicewar jinin al’ada:Daina zuwa,ko zuwa sau biyu a wata.
-Zubewan gashi
-Yawan kwadayi
-Yawan Kamuwa da infection akai akai
-Daukewar sha’awa
-Rashin sha’awa
-Motsi a ciki
Dama dai sauran alamonin shi.
Zaki iya tuntuban mu ta WhatsApp a wannan number 08109388227 domin yin register,Ko kuma a shafukan mu na yanan gizo a TIKTOK,YOUTUBE da INSTAGRAM me suna “LafiyarMataTv”*Page 6*
Jameel
" Hajiya kiyi hakuri ba biyayya ne ba zan iya Miki ba a gaskiya idan har Nimrah tana so ta cigaba da zama dani sai ta hakura da aikin nan nata dan har ga Allah na gaji ba zan iya cigaba da zama da ita Muna tafiya a haka ba.
Allah ya rufa min asirin da zan iya d'auke mata duk nauyinta da ya rataya a wuyana,tunda har Allah ya hore min duk abinda take so zan iya yi mata shi.
Idan har zaman hakane bata so zan Bude mata pharmacy ta ringa zama tana samun kudaden da take so da ko tana dashi ba wani abu da zai taso a gidana ta iya min.
Gata nan ki tambayeta shekara biyar data d'auka tana Aikin nan ba dare ba rana,shekara biyar da ta d'auka tana bautar aikinta ba tare da ita ta sauke nauyin aurenta dake kanta ba ta tab'a siyan k'oda kwayar maggi a gidana idan Babu? Hajiya wane namiji ne zai iya d'aukar abinda ni nake d'auka a zamanin nan?da sunan Ina da Aure Hajiya matata bata san tamin girki kafin ta fita ba,Yar aiki zata bawa tamin,da sunan Ina da Aure Hajiya Nimrah bata San tsafatace gidana balle ta kula da Danmu daya tilo,bansan dadin aure ba tunda ta fara aikin nan,Jaseem bai san dadin uwa ba ta sakarwa Yar aiki ragamar komai.
Waya san tsawon lokacin da Basira ta d'auka tana cutar damu Hajiya?
Kinsan Koda Nimrah bata fita aiki ba ba abinda take iya yi a gidanan sai dai ta saka Yar aiki.
Akan me ni kuwa zan cigaba da zama a haka sau nawa sai dai nazo gidanan naci abinci Hajiya.
Idan ta tafi aikinta wani zubin ba'a nan nake kwana ba da Jaseem kafin ta d'auko Basirar.
Nimrah ta kaini bango nikam na gaji.
Nimrah Sam bata San darajar Aure ba,ba kuma ta Jin magana
Idan zata tafi aiki haka zata ci kwalliya ta bulbula turare ta sa wani Karamin hijabi da sunan tana da Aure wa take so ta burge a wajen aikin?
Idan har kika ga Nimrah na rawar jiki toh zata je aikine
Ba abinda ya shafeta da Jaseem ko ni,akan me kuwa zan cigaba da barinta tana zuwa aiki
A gaskiya Hajiya Ina cutuwa a zamantakewar mu idan har Nimrah ba zata hakura da aikin ba gwara kawai an sauwake mata nasan bani da Mata dan dama kamar bani da matar,ba da ga kanta aka fara aiki ba
Abokaina da yawa matan su na aiki nakan dan bugi cikinsu naji ko irin zaman da nake da Nimrah suke yi Suma da matan su amma ban taba Jin Wanda yake fuskantar iirn matsalar da nake fuskatnta a wajen Nimrah ba.
Kiyi hakuri baki tab'a sawa nayi abu banyi ba amma wanan kam ba zan iya ba Nimrah dole ta zabi daya aurenta ko aikinta"
Jameel yace Yana sauke numfashi fuskarsa a balain hade dan tunda yaga Kiran Hajiya a wayarsa yasan karshenta dama Nimrah sai dai ta Kai kararsa wajen Hajiya
