page 10

308 8 3
                                    

*KOWA YA IYA ALLONSA*....

   *Na SadNaf*

        Page 10

4WEEKS REVERSE PCOS SYMPTOMS PROMO CHALLENGE wanda za’a fara on 1st January 2024.
Program ne da mukema mata masu CUTAN PCOS. Muna taimaka musu wurin magance wannan CUTAN ta hanyar
1. Basu magungunan cutan
2. PCOS CYSTERHOOD discussion group
3.PCOS and Hormonal imbalance reversal da
4.Fertility Treatment
CUTAN PCOS yanada alamomi kaman:
-Yin kiba ba bisa dalili ba
-Yawan Kasala
-Rashin Bacci
-Gashi a gemu,saman ciki,da saje.
-Kuraje a fuska, baya da kirji
-Rikicewar jinin al’ada:Daina zuwa,ko zuwa sau biyu a wata.
-Zubewan gashi
-Yawan kwadayi
-Yawan Kamuwa da infection akai akai
-Daukewar sha’awa
-Rashin sha’awa
-Motsi a ciki
Dama dai sauran alamonin shi.
Zaki iya tuntuban mu ta WhatsApp a wannan number 08109388227 domin yin register,Ko kuma a shafukan mu na yanan gizo a TIKTOK,YOUTUBE da INSTAGRAM me suna “LafiyarMataTv”

*Page 10*


Ahmed tijjani matashi ne dan gayu Mai ji da Kansa,kyaun da Allah ya mi shi yasa Yan mata rububin shi,iyayensa ba masu rufin asiri bane ba duk karatun da Yayi na Gwamnati yayi kyaun da yake dashi da karya yasa shi muamalla da yaran masu kudi har Kuma ya saje dasu.

A irin yaudarar Yan Matan da yake yaran masu kudi ya fada hannun Hindu da ta zame masa cingum,a lokacin iyayen ta na da rufin asiri.

Sosai take masa hidima,kama daga kyautar riga su turare,sai lafiyayyen abinci da take yawan masa idan yaje wajenta zance.

Ya so ace yaci banza ya ware kamar yadda ya Saba yiwa Yan mata dan shi kam bai ga kalar macen da yake so ba har a lokacin.

Dan shi Yar gidan masu hannu da shuni yake San aura wacce babanta zai bashi jari Mai kauri a bashi gida da mota.

Sai dai burinsa bai Kai ga cika ba bai Kai ga haduwa da irin wacce yake so din ba.

Hindu ta makale ta nace masa ba wani aiki ne dashi ba amma Hindu tace taji ta gani a karshe tabiyo ta wajen Mahaifiyar sa.

Da itama take mata hidima ta karfin tuwo ba wani kaunar Hindu yake ba, mahaifiyarsa ta tilasta masa aurenta.

A buga bugar da yake ma a lokacin ba wani taka kara Yayi ya karya ba

Ya auri Hindun da bai mata lefe ba tace ta yafe matar kaddara yake Kiran Hindu Dan itace take San shi.

Shi dai Yana zaune da ita ne kawai a Babu yadda zai yi.

Koda suka yi Auren Hindu ke fama da dawainiyar gidan

Shi kam wani shago gare shi na siyar da kanana waya hade da Yan manya sai cajojin waya rigar waya da sauran su.

Shi ma duk kudin ta wajen Hindu ya same su dan ba laifi dangin Hindun suna da rufin asiri da Kuma hadin kai.

Idan Yana neman abu Koda Hindu bata dashi sai ta Nemo masa a wajen danginta.

Ba yadda bai yi dan ya koyawa kansa kaunarta ba amma ya kasa Santa

Haka suke zaune yana cin kudinta tare da sakar mata hidimar gidan nasa tunda tace taji ta gani.

Tsalle tsallensa kawai yake wajen kula Yan mata.

Dan Yan matansa sun fi goma har lokacin bai cire rai da haduwa da irin wacce yake so ba Yar manyan mutane.

Duk da Hindu ba wai mumuna bace ba ya kasa Jin Santa a zuciyarsa ban da kyautata masa da take da ba abinda zai ce Yana so bata masa ba ya kasa Santa.

Yakan yi mata rashin mutunci dan yaga ko zata zuciya su rabu duk arzikin yaran dake tsakaninsu guda biyu.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 26, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

KOWA YA IYA ALLONSA Where stories live. Discover now