page 3

193 15 0
                                    

*KOWA YA IYA ALLONSA*....

   *Na SadNaf*

        Page 3

4WEEKS REVERSE PCOS SYMPTOMS PROMO CHALLENGE wanda za’a fara on 1st January 2024.
Program ne da mukema mata masu CUTAN PCOS. Muna taimaka musu wurin magance wannan CUTAN ta hanyar
1. Basu magungunan cutan
2. PCOS CYSTERHOOD discussion group
3.PCOS and Hormonal imbalance reversal da
4.Fertility Treatment
CUTAN PCOS yanada alamomi kaman:
-Yin kiba ba bisa dalili ba
-Yawan Kasala
-Rashin Bacci
-Gashi a gemu,saman ciki,da saje.
-Kuraje a fuska, baya da kirji
-Rikicewar jinin al’ada:Daina zuwa,ko zuwa sau biyu a wata.
-Zubewan gashi
-Yawan kwadayi
-Yawan Kamuwa da infection akai akai
-Daukewar sha’awa
-Rashin sha’awa
-Motsi a ciki
Dama dai sauran alamonin shi.
Zaki iya tuntuban mu ta WhatsApp a wannan number 08109388227 domin yin register,Ko kuma a shafukan mu na yanan gizo a TIKTOK,YOUTUBE da INSTAGRAM me suna “LafiyarMataTv”

*Page 3*

    Jameel

Da b'acin rai ya kwana dan ko baccin ma bai wani yi ba saboda tsananin b'acin rai.

Jaseem ya kurawa ido cikin tsananin tausayi da tunani tsawon lokacin da Basira ta d'auka tana gana Masa azaba batare da Sanin shi ba,dan Nimrah kam zai iya cewa haifar Jaseem kawai tayi bata san zafinsa ba.

Shekara biyar kenan da Aurensu.

Sai da suka kwashe shekara uku suna soyayya kafin suyi auren.

A lokacin ta gama secondary  school.

Tana shirye shiryen fara zuwa school of nursing.

zai iya cewa yayi Yan mata daban daban amma da yazo kan Nimrah yasan ya hadu da irin macen da yake so.

Dan Nimrah irin Matan da yake so ne.

Sai aka dace itama tana san shi a wanan lokacin.

Sai dai ko da ya fito mata da maganar Aure.

Sai ta nuna masa mahaifinta ba zai yarda ya aurar da ita  ba a yanzu sai idan ta gama makaranta har Kuma ta fara aiki.

Tana cikin karatun suna soyayya sai  yaji idan bai mallaketa ba ba zai tab'a samun nutsuwa da kwanciyar hankali ba ya je ya samu mahaifin ta da taki bashi dama ya same shi.

Gidansu Nimrah wayayyu ne Yan boko ya Kuma lura Yan gidansu Nimrah suna daraja karatu sosai.

Kamar yadda Nimrah kuwa ta fada masa da ya samu mahaifin ta ce  masa yayi Aure ba yanzu ba sai Nimrah ta gama karatu ta fara aiki,ba gatan da zai yiwa Nimrah sama da ya tsaya mata ta samu ilimi da abin dogaro da kai kafin ya aurar da ita.

Ko yayarta sai da ta fara aiki tayi Aure,Allah bai mai arzikin haihuwar Yaya Maza ba,mata kawai yake dasu dan haka su zai dage wajen inganta rayuwar su.

Da naci da komai da alkawarin ba zai tab'a hana ta karatu da aiki ba ya shawo kan mahaifinta Mallam Umar.

Mallam Umar mahaifin Nimrah na da rufin asiri daidai  nashi ba dai za'a saka shi a sahun masu kudi ba.

Amma a tsaye yake akan iyalinsa yana kuma iya biya musu bukatarsu.

A haka ya Auri Nimrah da yaga kamar mahaifin ta bai so ba,ya so sai da ta gama makaranta ta fara aiki ya aurar da ita.

Mahaifiyar ta kuwa sai ya karanci bata wani kaunarsa dan ko gaisheta yaje yi bata fiye bashi fuska ba,kamar yadda mahaifin Nimrah ke bashi fuskar.

Dan dak'yar take amsa gaisuwar sa idan ya shiga dan ya gaishe su.

A binciken da yayi ma kafin manya su shiga maganar yake Jin labarin Mahaifiyar su Nimrah masu kudi take so taga yaranta na aura saboda gidansu Nimrah ba laifi kyawawane kwarai.

KOWA YA IYA ALLONSA Where stories live. Discover now