page 2

191 13 3
                                    

*KOWA YA IYA ALLONSA*....

   *Na SadNaf*

        Page 2

4WEEKS REVERSE PCOS SYMPTOMS PROMO CHALLENGE wanda za’a fara on 1st January 2024.
Program ne da mukema mata masu CUTAN PCOS. Muna taimaka musu wurin magance wannan CUTAN ta hanyar
1. Basu magungunan cutan
2. PCOS CYSTERHOOD discussion group
3.PCOS and Hormonal imbalance reversal da
4.Fertility Treatment
CUTAN PCOS yanada alamomi kaman:
-Yin kiba ba bisa dalili ba
-Yawan Kasala
-Rashin Bacci
-Gashi a gemu,saman ciki,da saje.
-Kuraje a fuska, baya da kirji
-Rikicewar jinin al’ada:Daina zuwa,ko zuwa sau biyu a wata.
-Zubewan gashi
-Yawan kwadayi
-Yawan Kamuwa da infection akai akai
-Daukewar sha’awa
-Rashin sha’awa
-Motsi a ciki
Dama dai sauran alamonin shi.
Zaki iya tuntuban mu ta WhatsApp a wannan number 08109388227 domin yin register,Ko kuma a shafukan mu na yanan gizo a TIKTOK,YOUTUBE da INSTAGRAM me suna “LafiyarMataTv”

*Page 2*

      Nimrah

5hrs ago

A zaune take a palo tana latsa wayar hannunta sai murmushi take ta zubawa dan hira take da Hindu da kusan itace aminiyarta yanzu bata da sama da ita,a asibiti daya suke aiki kusan halinsu yazo daya da komai shi yasa suke ji da juna.

Tab'a ta da Jaseem yayi da ya fito daga dakinta da Basira tana d'auko shi daga makaranta ta masa wanka ya Sha tea bacci ya d'auke shi.

"Mummy ruwa zan Sha"

Jaseem yace a karo na uku yana Kara tab'a ta har lokacin idonta na kan wayarta ta kasa dagowa ta Kalli Jaseem dan labari hindu ke bata na yadda suka kwashe da mijinta Daren jiya.

Ta matsu shidda tayi ta fice daga gidan yadda zasu hadu su Sha labari.

"Kai Jaseem yanzu dan zaka Sha ruwa ba zaka je ka fadawa Basira ba sai kazo ka dameni"

Tace tare da Jan dogon tsaki ta hau kwallawa Basira da Jaseem ya fara zuwa dakinta ta zuba masa rankwashi aka tayi kasa da murya tana "Dan uwarka ka baro karuwar uwarka a Palo kazo ka dameni akan zaka Sha ruwa sai na cire ma idon nan naka shege"

Ta Kai hannu kamar zata tab'a masa idon

Jaseem kuwa yayi baya da sauri tare da barin dakin basirar da yake balain tsoro kamar mutuwarsa.

Har Dan cikowa idonsa yayi da kwalla amma Nimrah duk bata lura ba saboda chatting din da ya d'auke mata hankali

Basira da sauri ta fito daga dakinta tazo ta zub'e agaban Nimrah da take Jin dama tana da halin shaketa.

Dan tana Kona mata rai yadda take bautar da ita a gidan.

Shi yasa idan ta gama bata wahala kafin ta fita,tana fita  take sauke haushinta akan Jaseem.

Duk da ta girmeta amma a ido tafita jiki,dan idan kaga Nimrah tunani za kayi bata fi shekara Sha takwas din ba dan Karamin jikine da ita sosai irin na Fulani nan gata da kyau kamar wata budurwa.

"Wai uban me kike a ciki Jaseem ke neman ruwan Sha"?

"Bandakin da kika ce na wanke nake wankewa Aunty"

"Toh ruwa zai sha ki bashi ruwa ya Sha kizo ki kunna masa cartoon yayi Kallo.

Idan Kin gama wanke bandakin Kuma ki canza zanin gadon dakin Abu Jaseem kafin ya dawo ya min masifa"

"Toh Aunty"

Basira tace da sauri ta sungumi Jaseem dan a gaban idon Nimrah sosai take tattala Jaseem duk da wani zubin Jaseem na dari dari da nuna Jin tsoronta.

KOWA YA IYA ALLONSA Where stories live. Discover now